YADDA ZAKI HADA MAYONNAISE A GIDA
YADDA ZAKI HADA MAYONNAISE A GIDA
Assalamu Alaikum, a yau zan kawo maku wani
Abubuwan Bukata;
1. Kwai Biyu Manya
2. Lemon tsami ko ruwan Khal (vinegar) 2 teaspoon
3. Vegetable Oil ko Olive oil 1 Cup
4. Gishiri
5. Bowl
6. Whisker
Yadda zaki Had a;
Da farko dai zaki sam Bowl dinki mai Dan girma sai ki dauko kwayayenki guda biyu manya ki fasa su a cikin wani plate, sai ki raba kwaiduwar da farin. Bayan kin raba su sai ki saka kwaiduwarki a cikin bowl dinda kika tanada, ki dauko lemon tsaminki ko kuma ruwan khal (duk Wanda kika samu aciki zaki iya amfani dashi) sai ki debi teaspoon biyu ko kuma cikon spoon daya ki zuba acikin kwaiduwar ki. Idan kinyi wannan sai ki dauko whisker dinki ki fara buga hadinki. Bayan kin Dan bugashi ya cakudu sai ki dauko vegetable ko olive oil dinki Kofi daya sai ki dinga zubawa akai akai acikin hadinki kina kara bugawa. Idan kikayi haka zaki ga kina kara saka mai hadinki na kara yawa da kuma kauri
A gaskia munji dadi sosae amma baza'a iya hadawa da gwaiduwan kwai ba baki days
ReplyDeleteDaga Maman Hanan Tsanyawa