Kalaman soyayya 2023
Kalaman Soyayya 2023
Babu mamaki yanda idanuwanki ke satar zuciya haka murmushinki yake kara saurin bugawar zuciyata.kamar yanda kinka san cewa amo na sautinki yana tasiri ko a kunnuwan yan uwanki haka nake jin canzawar yanayina duk lokacinda nake jin muryarki.ki kara godiyar Allah akan tarin baiwa da ya baki.
Farkon rayuwarda nayo a baya dariya nake ga wadanda suke soyayya har nake ganin cewa shirme sukayi saboda ban yarda da siddabarun da ke acikinta ba.amma yau na samu damar gaya miki cewa kin canza kowane motsi na rayuwata.har nake jin kamar zan iya daukar nauyin kowane mai yin soyayya ya samu cikar dukan muradin shi.yanzu na yarda indai har akwai soyayya aduniya to sanadinki ne
Kece gaskiyar rayuwa,kece asalin burin da nake fata,kece gaskiyar mafarkinda nake kowane dare,kece farko da karshen kowane tunani da nakeyi idan nayi zaune shiru ni kadai. Idan kin yarda kece kinka bayyanarda asalin ni wanene awannan duniyar..kiyi yanda kike so kowa ya amince numfashi da nake domin ki ne.kece kadai mafarkinda ke yawan zama gaskiya arayuwata.
Watakila bazan samu damar sanar dake a kullum ba amma ki sani kalmomin da ke a baki ba zasu iya gabatarda shaukin da nake ji ba duk lokacinda nake sauraren dariyarki.hakika dariyarki magani ne na kowace irin cuta dake addabar zuciya.
Kowa ya kasa yarda dani cewa ban ta6a ganin halitta mai kyau da kwarjininki ba,idanuwanki bansan dame zan misalta haskensu ba,kyawo kike ko ba kwalliya,kowa cewa yake aljana nake gani nace kece mutune biyu kacal suke yarda da zance na.mama da baba nima kaina na fara amincewa ke aljanarda ke hana idanuwana runtsawace idan dare yayi.ki daina zuwa a mafarkina indai ke ba aljanar bace da gaske
Me yasa nake girmama sunanki? Me yasa zuciya da idanuwa suke yawan yaba kyawonki? Me yasa rai da jiki suke jin kamar babu wata aduniya da ta kaiki? Me yasa nake yawan tuna sunanki? Me yasa nake da tsananin buri da bege akan soyayyark? Wadannan sune tambayoyi da kullum suke dakatar dukan motsina.
DAKE NAKE
Dukkanin abinda zakiji daga gareni babu Karya ko niyyar yaudara a cikinsu yanxu ko kuma a chan gaba,Gundarin abinda maganata zuwa gareki zata kunsa KALMAR SO che,amma fa idan zaayi mata gunduwa gunduwa bani tsammanin zan iya warware maki zare da abawa,RANKI YA DADE kamar da wasa kyakykyawar tarbiyyarki ta saKa min SONKI a cikin zuciyata a cikin Kankanin lokachi,idan da zan samu yanda nake so DAKE NAKE fatan shiga babban dandalin masoya na wannan duniyar da kuma wanda ke a Kiyama,koda ban samu yanda nake so ba ina fata zaki rubuta sunana a madaukakiyar fadar zuciyarki a matsayin masoyi mai daraja koda bata farko Dukkanin abinda zakiji daga gareni babu Karya ko niyyar yaudara a yanxu ko kuma a chan gaba,Gundarin abinda magana zuwa gareki zata kunsa KALMAR SO che,amma fa idan zaayi mata gunduwa gunduwa bani tsammanin zan iya warware maki zare da abawa,RANKI YA DADE kamar da wasa kyakykyawar tarbiyyarki ta saKa min SONKI a cikin zuciyata a cikin Kankanin lokachi,idan da zan samu yanda nake so DAKE NAKE fatan shiga babban dandalin masoya na wannan duniyar da kuma wanda ke a Kiyama,koda ban samu yanda nake so ba ina fata zaki rubuta sunana a madaukakiyar fadar zuciyarki a matsayin masoyi mai daraja koda bata farko bace.
Sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma'abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga jikina. kada ki bar ni shawagi tamkar tsuntsu a sararin SAMANIYA. KALAMAN SACE ZUCIYA sukuma wadannan wasu dadadan kalamaine da akefurta su ga abar qauna a mabanbanta lokaci ko yananyi. Dandanon su yafi zuma dadi balle sukari ,sukan sanyaya zuciya ,sukan raunana zuciya ,sukan qarfafa zuciya ,sukan sa a sallamar da zuciya duka ,saboda shauqin su da saka masoyiya cikin
Inama ace za'a maimaita shekarun da suka wuce baya domin na samu damar bayyana kalmar soyayyarda nake miki domin kuwa karni yaya kadan na iya bayyana miki matsayinki arayuwata.
slm allah ka karemin mijina ^ allah kataimaki mijina ^ allah yafewa mijina ^ allah kaga tausan mijina ^ allah kadaukaki mijina ^ allah kabarni nida mijina amin.
Hubby nah inasonkah sosai allah dai yabarmin kai har abdah kaxama nawah nikadai my inah kaunarkah matukah karekeni amanah mijinah bye
tattausan kalami zazzakar murya hadadden murmushi kayataccen kallo kyau natsuwa kunya hakuri kamala tausayi aminci allah yakara tabbata gareka malami kamili salihi hafizi haziki sarki sarkin kyawawa gami da yardah da aminci su kara kasancewa ga amintacciyar zuciya wadda so da kaunar tah suka mamaye rayuwatah hakika kai nawane domin kai kadai ne nake burin kasancewa tare dakai abin alfaharina I LOVE YOU with all my heart bye.
slm mijinah barkah da safe rabin rainah allah y karah mah tsawon kwanah mijinah sobodah inkasance tare dakai cikin farinciki my inama tukar kaunar kah mijinah
allah sarki mijina rabin rainah farincikinah hasken idanuwanah inasonka mijina banidah kamarka arainah ina matukar jidah kai xuciyah allah yamallakah mini kai nikadai badah kowa bah da nayi farinciki marar misaltuwa mijinah plx don allah karikemin amanah har abada karka barni my ina matukar kanarka sosai a cikin raina
matata Kin wadata zuciyata da farin ciki kin haskaka rayuwata da haskenki kulawarki a gare ni ta musamman ce hakan ya sa nake jin kaina tamkar sarkin wata masarauta mafi girma da karfin iko. Ina Son Ki. nakira baki dauka ba hope dai lapia
A hankali a hankali ina ta ba ki filayen zuciyata ina so in rasa kaina a garin yin hakan ta yadda ba zan taba samuwa ba da sannu sannu dai ina ta mika rayuwata izuwa gareki ya masoyiyata kinzama abar kaunata wannan duk saboda karamcin kine a gare ni a yayin da nake kara kusantuwa dake duk tunane tunane na suka fara bayyana ya masoyiyata kin zama abar kaunata kamar giza-gizai haka kika zamo inuwa a gare ni kamar ruwan sama haka kika jike ni da farin ciki kamar iska haka kika tafi da tunani na kin sabunta kaddarata ta hanyar samar da sabuwar safiya a rayuwata Dake kawai nake son kare rayuwata
Masoyiyata Allah ya halicci zuciya be domin soyayyah zan kasance Mae yiwa soyayyarki bauta tamkar bawa agareta, ina mai matukar godiya ga Allah da hotemin ke amatsayin masoyiya.
A duniya duk Wanda yasameki a matsayin masoyiya wallahi yagama yin babbar nasara a rayuwa, domin kin kasance mace wadda ta mallaki duk abunda wata mace takeda shi, samunki ba karamar nasara bace.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d'auke da 'korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d'auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
Matata Uwar 'ya'yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d'aya, ina cike da zumud'in son dawowa domin cin girkin ki mai dad'l. ki kula min da kan ki, sal na dawo. Ina son ki matata.
Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za'a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.
so wani abu ne mai kyawu, kuma wani yanayi ne da mutum zai so ya damke. 'So. shi ne yanayin da kan sa ka ji ka a raye. Ina_fatan kin fahimci cewa zan so ki har karshe, saboda ba kin kasance budurwata kadai ba, ke ce Aminiyata.
So dayawa wasu masu yiwa soyayya mummunar fahimta sukance mace batada tabbas akasin basu samu wadanda ke kaunarsu da gaskiyaba, nikuma inada ke kuma nagamayin babbar sa'a a rayuwata, ke macece wadda babu irinta a rayuwa.
Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba.
Matata Uwar 'ya'yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d'aya, ina cike da zumud'in son dawowa domin cin girkin ki mai dad'l. ki kula min da kan ki, sal na dawo. Ina son ki matata.
Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.
Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba. Murmushinki Yayi, dariyarki Ba'a magana, Kin iya tafiya, Komai naki mai kyau ne, ina fatan mu Kasance tare. Naso ace inada wani qarfi domin tabbatar miki yadda kike ta Musamman a zuciyata, ke wata kalma ce wacce ke zane a xuciyata.
Samuwar ki a cikin rayuwata ya samar da gagarumin canji ga ‘karuwar farin-ciki na ta hanyar sauraren muryarki da kuma kasantuwata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsari. Ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, kina d’aya daga cikin mutanen da ba zan taba mantawa da su ba har abada a cikin rayuwata. ki huta lafiya
Agaskiya ina matuqar sonki saudat wlh sosai sosai fiye da yadda kife ke son ruwa hmm to dan yi murmushi mana (ana furtawa masoyiya irin kalamannan cikin murmushi me dauke da kallon qauna,mace tana iya hadawa da hawayen qauna dan raunata zuciyar masoyinta da qara so da qauna)
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya
Haskenki tamkar hasken farin watane mai haskaka sararin samaniya Wanda take dauke wani sanyi mai ratsa jini da jijiya, haskenki tamkar hasken zinariya Wanda yake sheqi da walwalin haske marasa misaltuwa.
yaune nake so na baiyyana miki irin son danake miki ,kisani shamsiyya wlh bani da wasu kalmomi ko ma auni dazasu iya bayyana son danake miki ,nidai ina sonki ,ina qaunarki ,kece burin zuciyata ,farin cikin raina cikar mafarkina wlh sham siyya matuqar ba zaki'iya qairga ruwan tekuba to bazaki iya qididdi ge son da nake miki ba
Cutar sonki batada magani agurin likita saidai ke,cancantarki ce tasa hakan zurfa'a ina me tabbatar miki bazan taba jabaya a soyayyarkiba kece farincikin raina burun zuciyata zurfa'ah tawa wai dan Allah zurfa'ah wanna irin so nake miki haka? Pls fadamin dan Allah, Uziri zakiyimin masoyiyata nakan rasa kwanturol dazarar naji dadadan kalamanki masu dake da wani sauti me ratsa zuciyata ,kai lallai nayarda so Aljannar duniya ni gatawa na samu hmm Allah yabani ke hafsat.
Kasance mai faranta zuciyar wanda yake kokarin faranta taka zuciyar koda kuwa kai zaka shiga cikin damuwa ne, Kasance mai kare mutuncin masoyin ka a lokacin da kuke tare ko bakwa tare da shi, Tirsasawa zuciyar ka son wanda ya nuna yana son ka a zahiri babbane ko yaro, talakane ko mai kudi, mace ko namiji, kyakkyawa ko akasin haka.
Gajeriyar saƙon soyayya na iya yin silar kara shauƙi a zuƙatan masoya, Gajerun kalaman soyayya Sukan bayyana tare da zayyana abunda zuciya take ƙunshe dashi zuwa ga masoyi ko masoyiya. Don haka idan kuna son nuna soyayyar ku ga masoyan ku, Yana da kyau kuna aika musu da wasu gajerun saƙonni na soyayya masu ban mamaki kuma na musamman!
Shin masoyina izuwa yanzu ko ka fara jin gajiya a jikinka kuwa? Saboda ka kasance kana motsi a cikin zuciyata a tsawon dare ka kuma kasance mai zagaya dukkan jikina ta kafar da jinin jikina ne kawai yake gudana a cikin kowace safiya da yini. Ina son ka. Wajen zubin kwalliya Ke gwana ce, kin cinye gasar kyau da zuciyata ta saka, Ina Mata suke, suzo su kalli sarauniya ta!
sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina. Kin saye zuciyata ƴar amana, duk sirrika na kin lamishe su, baki rage min komai ba sai zuciyar, dan Allah karki nisa dani!
Muryarki tamkar sarewa ce wadda idan ana busata tamkar anayinta ne a cikin karkashin zuciyar mai sauraro, ina matukar alfahari da ke a rayuwa. Ina son na kasance a gefen ki kullum, domin na rinƙa sauraron sautin muryar ki mai kama da na kanari , na ringa kallon murmushin ki kamar farin madara!
Kin dauke makullin shiga zuciyata, dan haka babu wata mace da zata samu damar shiga kece Sarauniyar Zuciyata Kamar yadda ake gane farin fulawa acikin jajayen furenni, haka Soyayyar ki take bata boyuwa a zuciyata, Ina son abubuwa uku agareki, idanun da basa kuka, bakin da baya karya, Soyayyar da bata mutuwa.
Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni! Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan taba mantawa dake ba masoyiyata, bana fatan ranar da zaki kasance cikin koda kuwa wani ne zai batamiki rai barantama nida kai na.
Ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciyata. Fatana a kullum ki gamsu da cewa, Ina Son Ki.SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d'aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.
So gamon jinine, hakika sonki ya zamo jinin jikina na godewa Allah Subhanahu Wata’alah da yayi sanadiyar haduwa ta dake kuma hat na iya kasance mai kaunar ki a wannan duniyar ta mu ta Masoya, Ina Son Ki!..
kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma'abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min. Bani da kamar ki a rayuwata, karki gujemin, ki kasance dani, zan zama garkuwa agareki
Yanayin zafi kan sa mutum yayi gumi amma duk yadda yanayin zafi yayi tsanani da zarar na tina ki Masoyayi ta sai naji wani sanyi a jikina har cikin birnin Zuciya ta, ta yadda zanta dacewa ana cikin yanayin zafi ne ma duk kuma a sanadiyar Soyayyar ki.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki. Aminan juna nake so mu kasance, ba abokai ba, domi mu kasance da Soyayya ta har abada. Wasu lokutan idanuna suna min gizo da hoton ki, amma nasan zazzafar qaunar da nake miki ne, saboda kece a zuciyata!
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan taɓa canjawa a kan hakan ba.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad'uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya. Dadi wuya ni dake babu batun fishi da juna, ko munyi ma mu zamu gyara kammu. Ina Sonki.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin d’aya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
Ke farar macece wadda ake yiwa alkunya da alkyabbar mata, gaki fara zuciyarki fara gaki da farar aniya, ina sonki kuma ina kaunarki kuma aurenki shine cikon muradin rayuwata. Na yi miki alkawari zan kasance dake har iya tsawon da nunfashi zai zauna a jikina. Bazan yada ke ba!
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar 'karshe, saboda kai ba saurayi ne ka. Hankali na zai kasance a kwance ne ranar dana ganki cikin daki rufe da mayafin amarci, na kiraki da amaryata.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi. Idan munyi Aure, bani da wata fargaba, domin naci zabe, mulki kawai zanyi domin saki farin ciki.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki. Na makance akanki, har nakai matsayin da bana gane kowa idan bake ba, Soyayyar ki ta wuce kima a zuciya ta! Alkawarin mu na nan, ni dake, babu rabuwa, babu yaudara, babu cin amana, kullum Farin ciki Habibina!
Yau zanyi shela, duniya ta sani cewa kin mallaka min Zuciyar ki, Kuma nafi kowa farin ciki da murna, nagode Aminiyata!, Sautin muryarki nake son nake ji a kullum domin yana sakani shauki, kuma yana sani qara sonki Matata!, Masoyiyata! Qaunata agareki Gaskiya ce, Kalaman dake fitowa a bakina Zahiri ne. Ki yarda dani!, Zan fafa ta da koma wanene indai akan ki ne, na bada rayuwa ta ta zamo fansa. Kece Duniyata!
da akwai wasu lokuta da nake zubr da hawaye saboda ke na san za ki ce saboda me Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin dana ji muryarki ko na tina da ke Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki maryam don Allah kitaimaka ki sabamin da naji muryanki Kafin na kwanta👏
Matata Ina sonki ina kaunarki ba zan daina sonki ba har sai lokacin dana rufe idona wanda ba zan kara bude su ba har abada ballantana nayi tozali da kyakkyawar surar jikinki da tattausan murmushinki wanda da mutum yana halitta da za’a iya cewa ke kika tsarawa kanki komai ba tare da tawaya ba. Hausawa sunce dan Adam tara yake bai cika goma ba, to ke a wurina kin kai 100% hakika yin maganarki da godiyarki a gareni yafi bani duk wani abu da yake cikin duniya. Nasan a cikin masu neman zuciyarki nine makaskanci a wurin rubutu sannan nakasasshe a wurin kalamai, hmm! Ina ma ana iya rubuto zuciya a turo da ita da ananne za ki iya tantance masoyi na gaskiya sauran duk gwadawa suke amma ni aikatawa nake
Yayin da kika iso bakin kofar zuciyata na sadaukar da rayuwata ga sunanki na koyi yadda zan rayu masoyiyata ada ban taba koyon yaya zan rayu ba ban taba koyon yadda zan rayu ba tare dake ba masoyiyata wadannan yabo ne na gaskiya nake miki da zuciyata yayin da na same ki sai duniyata ta kawatu matuka duniyata ta cika burinta duk kanmu ba a ciki muke ba yanzu ne da muka hadu muka zama daya. wlh matata inason Fiye da so idan da yanda zanyi da zandaukaka martabanki dasai nakira taron duniya nasanar da kowane namiji cewa nafi kowa dacen mata
Shi so wani linzami ne da ke jefa kansa a cikin zuciyar da ya ga dama domin sarrafata, wanda muddin ya sarkafe zuciyarka to hakika baka da wani yunkuri da za ka iya yi domin kubutar da kanaka face nemo wanda ka ke so din Ki sani cewa tuntuni wannan linzamin so da kaunar naki ya sagale zuciyata ta yadda bani da wani sauki da ya wuce na ga na mallakeki
Matata so tamkar rayuwane ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki a zukatan mu Rukayya duk sanda nace kituromn abbu, Rukayya ita Soyayya wata abace dake shiga cikin zuciya batara da kasaniba kuma itace jigon rayuwa Na tarasune waje daya
Na rasa me zance acikin wannan dare amma zan gaya miki abinda ya hana barci zuwa idanu na..ba komi bane illa tsananin kewanki.sai da safe
SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA. Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki! HMM!! KI YARDA DA NI. A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.
Labarin farin cikina yana farawa ne daga jin muryarki,asalin ma'anar soyayyata sunanki ne,.asalin kasancewata awanan duniyar sanadin ki ne..inason ne na bayyana ki da kalmomi amma zaki ce nayi son kai.kece asalin samun nutsuwa da kwanciyar hankalina
ZAN SO KI JI. Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki! KE CE MURMUSHI NA. Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
SLM yake tauraruwar mata kece dai kika ciritutar kyau abirni da kauye masoyiyata inhar nasa meki nayi babban rabo aduniya, Kaunarki tayi mini katutu tayadda bana numfashi har saida amincewar bugawar xunxurutun ruhin rayuwarki agareni
Na maza KIN ZARCE SAURAN MATA Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki. SINADARIN RAYUWA TA. SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
Kin zame min komi arayuwata.kece kaddarata kuma kece manufa ta..nagoda Allah kuma nagode fadi tashin da nayo baya har zuwa yau da na sameki.
Kyautar Kalaman So Daga Bakinda Baya Gajiya Da Ambaton Furucin Harafin Dake Fitar Da Sakon Gaisuwar Girma Agareki
Budemin Nashigo Kofar Zuciyarki Da Sannu Zan Zamo Dauwamammen Farin Cikin Da Zai Bunkasa Dukkan Wani Farin Cikin Rayuwarki
Assalamu Alaiki Yake Hakikar Halittar Da Bayananina Suke Nufi. Nazo Da Murna Zuwa Murmushi Da Farin Cikin Shaukin Samun Damar Ganin Kyawun Nasabarki
Kicemin Marhabun Yaka Taho Dan Gata Zuciyata Kazo Zan Baka Ruwan Hawayen Idanuwana Suna Kwaranyane Sanadin Nemanka
Annashuwa Da Shauki Ne Zasu Biyo Baya Farin Ciki Marar Misalin Adadi Shine Zai Rufe Dukkan Wasu Kofofin Damuwata
Zuciyata Tana Miki Sallama Ta Masoya Jinin Dake Kara Kuzari Ajikina Shima Yana Ladabin Gaisuwa Agareki
Yar Asalin Kyau Mai Dirar Hanci Siriri Matsakaici Kinada Kyawun Halitta Da Tsarin Iya Kwalliya Akan Burgewa
Sonki Ne Kadai Akan Tsarin Dukkan Tunanina Komai Nisan Dare Da Tsawon Wuni Iya Wuya Tunaninki Ne Akan Kwakwalwata
Kallon Tsakiyar Idanuwanki Suna Saukar Da Sabuwar Ni,ima Acikin Jikina Ta Hanyar Hakane Nake Kara Kaimi Wajen Ganin Nasamu Ganinki Akowace Rana
Dauki Ki Amsa Sunankine Nake Ambato Tsananin Sonkine Yake Tsuma Zuciyata Shiyasa Bana Gajiya Wajen Yaki Da Dukkan Wata Damuwarki
Alokacinda Hasken Wata Ya Keto Gabatowar Asbahi Wani Sauyin Yanayine Yake Sauka Mai Dadin Sanyi Dake Ratsa Fata
Gamsuwar Jiki Da Yanayin Annashuwar Ruhi Yana Haifar Da Tsantsar Kwanciyar Hankali Adaidai Lokacin Nutsuwa Tana Kara Samun Ma,abocin Kasantuwa Alokacin
Kwatankwacin Debewar Kewar Irin Wannan Lokacin Nakeji Ajikina Aduk Lokacinda Nakejin Sautin Muryarki Tana Ratsa Kunnuwana
Makurar Kalmomin Baki Sun Kure Wajen Kurewar Rerawa Dakuma Rubuta Sakonnin Dazasu Fahimtar Dake Irin Son Danake Miki Amma Har Yanzu Basu Ambaci Komaiba
Hasken Zuciyarki Yana Kan Idona Idan Nayi Bacci Sannan Nayi Mafarkinki Hakan Yana Wadatar Da Zuciyata Samun Walwala Iya Tsawon Lokaci Mai Nisa
Sallama Agareki Tareda Sako Na Musamman Wanda Yataso Daga Farkon Numfashin Zuciyar Dake Kiran Sunanki Akowane Bugun Numfashi
Kin Isa Ayi Miki Komai Shiyasa Na Mallaka Miki Abinda Yafi Komai Muhimmanci Acikin Jikina Wato Zuciyata
Na Gamsu Kuma Na Aminta Da Yawan Amanarki Shiyasa Na Damka Miki Amana Mafi Girma Acikin Rayuwata
Kici Gaba Da Bani Kulawa Nikuma Zan Cigaba Da Kyautata Miki Iya Tsawon Adadin Kwanakin Numfashin Raina
Kin Samu Kyakkyawan Matsuguni Acikin Raina Ina Alfahari Da Kasantuwata Acikin Rayuwarki Komai Wuya Zan Cigaba Da Kyautata Miki.
Rabbi Sarki Mahallicin Bayi Nake Roko Yasanya Kina Cikin Koshin Lafiya
tsamanin Sonkine Yake Dauke Da Al"audun Kafuwar Tarihin Rayuwar Kaunarki Wadda Ta Nashe Xuciyata Nakamu Da Tsananin Xillar Axabar Xumudin Sonki Wadda Hakan Ya Haifar Da Aukuwar Karuwar Begenki.
Y'a masoyiyata Hauwa Mai kyakykyawan suna.
Lallai Ba Shakka Sonki Xai Iya Xama Ajalina
Musamman Idan Xuciya Ta Rasaki Babu Makawa
Xan Bar Duniya Da Xanen Hotonki a Bangon
Xuciyata.
Ganin Kyakkyawar Fuskarki Kan Iya Samar Min Da
Warakar Damuwa Da Bakin Cikin Xuciya, Duk Da
Cewa Kyakkyawan Lafaxin Bakinki Shine Linxamin
Dake Janye Ra'ayina Wajen Sha'awar Xama Kusada
Ke.
Ki Yarda Da Cewa Inasonki Kuma Baxan Sauya
Ra'ayina Va Koda So Da Qauna Xasu Ratsa Jiki Da
Jijiyar Jini.Kece Daya Tilo.
Tarihi a Cikin Fadar Masoyan Asali.
My Inason ganin fuskar ki ta cika da farin Ciki, inason naga
annashuwa a tare dake, inason naga kina walwala na jin
daɗi, banason naga bacin rai naki, bana son kiyi kuka, kukan
ki tayar min da hankali yake, hawayen ki zazzabi suke
sakani, nakan dimauce idan bakya farin ciki. Burina ni dake
mu Kasance abokai na har abada, mu Kasance Aminai, mu
Kasance ma'aurata, ni dake mu Kasance hanta da jini. Mu
Kasance kamar ƙarfen jirgi dan ƙarfi, mu zamo kamar zinare
ko ina aka kalle mu an ga mata da miji cikin Soyayya. Mu
kasance masoyan juna na haƙiƙa.
MY Zanzo gareki domin warkar da raɗaɗi da xogin da zuciyata
keyi akan kaunarki, ciwon ƙaunarki ne abinda ke fisgar
xuciyata ta jefani cikin duniyar tunaninki, Shalele ƴar lele
sarakiya mamallakiyar xuciyana mai sarautar zuciyata sakon
ƙauna mai ɗauke da tambarin zuciyata zuwaga Queen ɗina kina Zuciyata.
Masoyiyata abar kaunata ki sani ina sonki ina kaunarki son da nake miki har ya kai ga…..ko da idanuwana a rife suke ke nake gani idan na bude su ke nake son gani. Ko da ba na tare da ke ina jin motsinki a cikin jikina Lokachin da nake tinaninki, kadaici shi ya fiye min komai dadi. Me ya sa kina rayuwa a cikin jikina ni ma ina rayuwa a cikin jikinki amma duk da haka nake jin tsakaninmu da nisa?
Sarauniyata taho gare ni ki kama hannuna ki furtamin kalmar kauna a cikin kunnuwana…na rayu saboda ke ki zo ki mutu a kai na…ki sani ni fa ko a lahira idan an tashe mu to ke nake so a matsayin matata….na samu biyayyarki me kuma ya rage zan roka a wajen ubangiji?
kawai numfashi nake so ga ubangiji don mu yi soyayya mai dorewa ni da ke….fatana Allah.ya tsawaita mana rayuwa ya ke abar kaunata…wacce nake ganin sunan ‘ya’yan da zan haifa a cikin idanuwanki….fakina da idanuwana ba za su iya fada miki ko kwatanta miki adadin son da nake miki ba don tuni na shide a cikin sonki, na zama ke. I Love You Mai Sona
Kece kadai acikin zuciyata,kece waddarashin ganinki kemai dani maraya.
Tunda idanuna suka kalli kyakkyawar fuskar ki,kunnuwana sukaji daddadan sautin muryar ki zuciyata ta fantsama cikin kogin kaunar ki ya sahibata abin alfaharina.
Idan ina tare da ke ko,online ko a Gidan ku ko a
Gari farin cikina bayamisaltuwa na kanjikamar kada na tafi gida domin
irin yadda nake son kasancewa tare da ke a kowanne lokaci ya mamaye dukkan wani burina. Hakika yawan sauraron muryar ki kadai ka
iyasawa naso abani daki na tare a gidan ku, bana tunanin matsalar komai in har
idanuwana nayin arba da kyakkyawar fuskar ki mai
cike da annuri da haske kamar wata dan daren 14,
ki kasance tauraruwa mai haskake gani na, nakan ji
dadin muryar ki a duk sanda kika furta man Kalmar so.
Lallai ni yau na zama bawan soyayya wanda nake ta fangima da fangan
fangan a cikin tafkin dausayin soyayyah wadda rasa ta zai iya tarwatsa dukkanin wani fatana da farin cikina.
A duk sanda na kwanta bacci zuciyata zata shiga shiryo mani irin daddadar soyayyar da ya wakana a tsakanin nida ke, sai kawai in ga ina wani irin murmushi jin dadi saboda dace da nayi dake a matsayin masoyiyata.
Amincin Allah ya tabbata ga amintacciya, Wacce zuciyata ta
aminta da amincinta, Wacce nakeyiwa SON da bana yiwa
kaina, wacce tazamto sarauniya me isashshen iko datake
tafiyar da mulkinta a yalwatacciyar fadar zuciyata, Ina
Tabbatar miki bawata bayanki, Ke kaɗai ce tawa.
Soyayya na iya chanja mutum, domin ita Soyayya ba'a ganin,
balle a koreta ko a hana ta shiga zuciya. Ba'a Cewa Soyayya
ga yadda ake so, sai-dai kayi yadda take so. Ba'a Shiri wa
Soyayya, ko babu shiri Idan taxo kamar mutuwa haka zata
shiga Zuciyar mutum. Duk wanda yayi so dan Allah to shine
keda riba, cikin Soyayyar ki babu sirki, na gani kuma na
gamsu kuma na Tabbatar da ke me ƙauna tace ta hakika, ki
sani, ni bazan taba son wata ƴa mace wacce bake ba, domin
zuciyata bazata taba jindadin zama da wata ƴa sama dake
ba, duk wani jin daɗin duniya bai damen ba indai babu ke.
Rayuwata Fansarki ce, Zuciyata Tini ta Rikirkice, Kunnuwana
Sun ƙi Karban zance, idanuwa na sun so su makance, duk
sanadin Soyayyar da kika amince mini, Mulkin zuciyar Shine
aiki na, samun farin cikin ki jindaɗi nane, Murmushinki
Annashuwa Ce ga zuciyata, Duk ranar da kikai fishi Dani
banida kwanciyar hankali, Ni Bawa ne ga Zuciyar ki.
Farkon Sallama Cikin Salamar Samun Sa,a Da Murnar Kasantuwa Cikin Dausayin Ni,imar Sanyin Murmushin Labban Bakinki
Idan Sautin Zancena Zaiyi Furucin Gaisuwa Agareki Yazama Dole Na Tunkari Gagarumin Murmushin Fuskarki Hakan Shine Zai Tabbatar Da Nutsuwa Acikin Ruhina
Zahirin Zallar So Shine Yake Addabar Ruhina Shiyasa Zuciyata Ta Kuduri Aniyar Taimakon Ruhina Wajen Isar Da Sakona Agareki
Rayuwata ta kasance rataye cikin tarkon soyayyarka, ka ɗana kuma ya kama ni. A dukkan lokacin da na kalli ƙwayar idanuwanka, na kan ji wani shauƙi mara misaltuwa. Ina Son Ka.
Ina cikin kewarka, ina cike da ɗaukin son ganin Ka, a cikin kowace rana son ka na lunkuwa a cikin zuciyata, fiye da yadda fatar bakina za ta iya furta hakan. Ka huta lafiya.
Abu mafi tsanani wajen sanya zuciya a damuwa shi ne, ka samu wanda kake so shi kuma a lokacin ya faɗa a son wata. Bana fatan hakan ya kasance a tsakanina da kai. Ina Son Ka! Ina Son Ka!! Ina Son Ka!!! Masoyina.
So abu ne mai wahalar da zuciya da kuma sanya ta nishadi. Zan so ka kasance cikin bani kulawa domin gujewa faɗawa wahalar ta so. Ba zan taɓa canja ra'ayina a kan ka ba har abada. Ina Son Ka.
Samuwarki a rayuwata ne ya koyar da ni har na san zahirin siffa ta SO. Sai bayan da muka yi aure na ƙara fahimtar soyayya ta gaskiya. Ina fatan mu kasance a tare da juna na tsawan rayuwa har zuwa gidan Aljanna. Ina matuƙar Son Ki matata. Amma a lokacin da na dawo gida za ki ƙara tabbatar da hakan. Hmm! Ina nan cike da zumuɗin son zuwa cin girkinki mai daɗi.
Kin Zarce Shiga Kinkai Bangon Kurewa Acikin Jerin Yan Matan Dake Takama Da Kyau Shiyasa Idona Baya Gajiya Da Kallonki Ayayinda Murmushina Yake Bayyanuwa Alokacinda Nake Kallonki
Halittarki Ta Tsaru Kin Kware Wajen Iya Furta Zancen Bakinki Yaya Rayuwa Zata Kasantu Idan Har Banyi Tozali Da Murmushin Fuskarki Ba
Bude Idanuwanki Kidubeni Tsananin Sonkine Ya Addabi Ruhina Dukkan Rayuwata Tatafi Akan Tsarin Daidaituwar Yawan Begenki
Karda ka so ɗaya, kuma karda ka so biyu, amma dai ka ci-gaba da son ɗaya wadda ta mace a kan son ka. Mijina kai ne abun alfaharina da kuma 'ya'yana. Ina Fatan Dawowarka Gida lafiya.
Kalmomi na kasancewa ma'abota sauƙi wajen furtawa a dukkan lokacin da SO ya kasance shi ne harshen furtawar. Zuciyata na yin haske a dukkan lokacin da muke tare, na kan shiga damuwa idan ka nesanta da ni. Duk da ka zamo mallakina amma zan so ka kasance mai kare min kanka daga harin da sauran mata zasu ke kawo maka a duk inda kake. A dawo lafiya.
Kana da damar tura wa abokiyar tsinkar furenka, amma ba a amince wani ya yi amfani da shi da niyyar yaudarar wata ruhi ba. Akwai mai ganin Ka/Ki a ko'ina wato Allah. A kiyaye haƙƙin mallaka, a guje wa satar fasaha.
Kizo Guna Muzauna Cikin Rayuwa Mafi Inganci Nidake Bazamu Rabeba Komai Wahalar Zaman Rayuwar Duniya Bazan Chanja Alakata Dakeba
Yanayin Rayuwar Duniya Cikin Hikimar Tafiya Da Al,amurran Yau Dakuma Gobe Kullum Ina Kara Tozali Da Sabon Sonki Wanda Yake Shiga Acikin Raina Adukkan Lokacinda Idona Yake Kallon Tafiyarki
Idan So Asaline Toh Ita Kauna Dolene Ta Zamto Tubali Na Musamman Idan Faruwar Hakan Tafaru Mezai Hanani Tunaninki?
Sonki Yakai So Har Yakai Bana Ganin Zuwan Mai Zuwa Alokacinda Muka Zauna Atare Domin Kallon Fuskarki Yana Dauke Dukkan Nutsuwa Dakuma Hankalina
Kalmomin da a kowane lokaci nake farin-cikin furta su gare ki su ne..... Kodan na san tini kin daɗe da sanin adadin yadda nake son Ki, nake kuma ƙaunar Ki sai dai kawai na ce bani da kamar KI. Burina a kullum bai wuce na ganin na mallake ki ba har abada.
Na kan ji wani abu a cikin zuciyata, ba komai bane face fitila wadda ke kunnuwa a dukkan lokacin da na sanya idanuwana a cikin naki. Ina son Ki fiye da yadda alamun hakan ke bayyana a saman fuskata. Ki huta lafiya.
Kina daga cikin mutanen da ba zan taɓa mantawa da su ba a rayuwata. Kin zamo cikin tinanina. Bana fatan zuwan wani abu da zai zamo silar rabuwarmu, ko da a ce mutuwa ce. Ina Son Ki.
Ki kasance mai ɗaga kanki Ki kalli sararin samaniya a cikin kowane dare, karda ki furgita a lokacin da kika hango wata mai tsananin haske, ni ma na yi hakan kuma na samu ganin wata tauraruwa mai haske idaniya da kore damuwar zuciya wato ke. Ina Son Ki.
A kullum na kan kwanta da tinaninki, na kuma farka a cikin mafarkina, na gan ki zaune kusa da ni, a cikin wani lambu ma'abocin tsintsaye da furanni. Tabbas a lokacin murmushinki ya fi komai jan hankalina, muryarki kuma ke samar da nutsuwata. Ki Huta Lafiya.
Duk inda ya tafi, ko me yake yi yana tinaninki. Ko bacci yake yi ko a farke yake, yana hasaso murmushinki. A dukkan lokacin da kika yi nesa da shi, wajen ganin fuskarki ba ya buƙatar hotonki. Karda ki yi tinanin wani ne na daban face ni. Ina Matuƙar son Ki kamar yadda kika daɗe da sanin hakan.
Da akwai wata ƙaya a cikin zuciyata, wadda ta kasance cikin sukana a dukkan lokacin da na tina tazarar da ke tsakaninmu. Da ma a ce zaki mayar da ni wani sashe na zuciyarki na tabbata da na samu sassauci. Abu mafi soyuwar furtawa a gare ni zuwa gare ki shi ne, Ina Son Ki.
Da akwai wata mace a cikin wannan duniya, wadda ta yi daban da sauran matan dake a gidajensu na aure. Ita ta kasance ta daban ce, halayanta kuma ababen so ne. Ba kowa bace face Ke, a saboda haka nake ƙara son Ki a kullum. Ki kula min da kan ki, har zuwa lokacin da zan dawo gida kulawarki ta dawo hannuna. Ina Son Ki Matata.
Masoyiyata, ina son na sanar da ke adadin yadda nake son Ki a cikin zuciyata, sai dai kuma, na rasa samun kalaman da zan yi amfani da su wajen bayyana hakan a gare Ki. Ina son ki. Ki kula min da kanki.
Da a ce a yau zan samu fukafukan tashi, na tashi izuwa sararin samaniya, na je na gano taurari, na sauko izuwa doron duniya, bana fatan Ki tsunduma cikin matsanancin mamaki a lokacin da na bayyana miki cewa kin yi kama da ɗayarsu wato Zara.
A dukkan lokacin da ka furta baka so na, babu inda ya fi dacewa da na ci gaba da rayuwa a cikinsa face kabari, domin kuwa na san daga ranar duniya za ta zamo wajen zubar hawayena. Ina Son Ka.
Zuciyata ta riga ta saba da kai, ta yadda nake iya jin tamkar na zamo cikin jakarka a dukkan lokacin da ka tashi fita. Da tinaninka nake wuni idan ka fita, sai kuma ka dawo nake samun sukunin yin murmushi. Ina Son Ka Mijina.
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba.
Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.
Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya d’ayace babu wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.
Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda Allah ya na so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka? Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE masoyiyata, ina son ki.
A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.
Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.
Salim ina son ka, me ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka? Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da SADAUKI.
Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!
A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina Son Ka!
A gaskiya sace zucciyar mace abu ne mai sauki ga wanda ya gane sannan kuma abu ne mai wuya ga wanda bai gane ba.
Tabbas idan dai har kana so ka yiwa mace satar zucciya dolene sai ka bi dokoki kamar haka:
1. Jan_Aji: ka sani fa mace bazata iya mallaka maka kanta hakannan kawai ba dolene sai ta ja maka aji dan ta gane halayenka da haƙurinka sannan kuma zata so ta gane ko da gaske ne kake sonta ko ba da gaske ba sabida mata sun tsani duk wani saurayin dake shirin yaudaransu, idan har kaga ka zowa mace kai tsaye ta amince dakai ba tareda jan class ba, to fa ka tsoraci lamarinta domin mace idan har cikakkiyar gogaggiyar mace ce to zata ja maka class sosai har sai ka kusan yin kuka tukunna.
2. Hakuri: Tabbas dolene sai ka zamo mai hakuri idan ba haka ba bazaka samu damar lashe jarabawar da mace zata yima ba sabida zakaga ababe da dama masu gasa zucciya, idan har baka zamo mai hakuri ba; to kai da yin soyayya da mace saidai a slow... 3. # Gaskiya: mace tafi son saurayin da ke gaya mata gaskiya kai tsaye, idan har kai makaryaci ne to ina mai tabbatarma da cewa idan har tazo ta gane sirrinka zaka sha kashi, dan haka ake kwatanta gaskiya daidai gwargwado.
4. Kulawa: dolene idan dai har kana son zamanka da mace ya ɗauki tsawon lokaci kuma yasa ta soka sosai fiye da kima to lallai kuwa dolene sai ka kula da ita tamkar yanda zaka kula da kanka a lokacin da kake cikin rashin lafiya. Kulawa yana ɗaya daga cikin siffofin abinda mata suke so.
5. Rarrashi_Tareda _Girmamawa Mace tafi so idan har ka sanyata yin fushi to ka rarrasheta tamkar yanda zaka rarrashi jaririya. Kuma mace zata ji daɗi sosai fiye da kima idan dai har kana girmamata, ta fannin yabon halayenta na kirki tareda nuna mata cewa babu wanda kafi so a duniya tamkar ita sabida tana da halin kirki.
Na gode da duk tasirinki a rayuwata. Kyawun fuskarki yana birge sassan zuciyata, yana rayuwa dani cikin wakafin soyayya. Na godewa Allah da yasa kikazo cetona a karshen numfashina domin ya rayar dani da sumbatar ikon ki. Komai nisan da ki kai, zaki kasance cikin zuciyata. Ba ko da inchi ɗaya ba za ki iya tserewa tunanina ba saboda ke tawa ce yanzu da har abada, ina ƙaunarki!
Igiyar da ta riƙe damu ba za a taɓa warwarewa ba, saboda tana nufin murayu tare har abada cikin hasken soyayya. Qaunar ki har zuwa ƙarshen zamani za ta kasance ta farko a kan gaba. Ina son ki bugun zuciya ta.
Kina nufin duniya gareni ni kuma ina rayuwa Zuciyarki cikin aminci. An canza rayuwata saboda kin shigo ciki. Na gode da duk kaunar da kike min. Zan dage da son ki har zuwa karshen zamani. Babyna zan so ki har abada. Zan nuna miki Soyayya ta a hanya mai ban mamaki kuma wannan zai bar zuciyar ki da farin ciki na har abada, farin ciki da tausayi Tare Da shauki
Ina Qaunarki kuma ina son komai game da ke. Ina jin dadin kokarinku a rayuwata. Akwai wannan turare naki na musamman wanda ke zuwa tare da wani Qamshi mai ƙarfi na fure, ki gaskata ni zan iya mutuwa akanki saboda ke koyaushe ki Rike ni sosai Shalelena.
Idan na tuna wani lokaci tare dake, Nayi murmushi ni kadai ina jin kamar ina kan dutse mafi tsayi. Ina fata zan iya raba zuciyata a gare ki don kiga irin farincikin da nake yi saboda kin kasance kusa da ni zaune cikin zuciyata. Shine mafi kyawun lokaci, kuma ƙaunatacce!
Na gode da kika kasance a duk lokacin da na fi bukatar ki. Ke irin wannan furen ce mai daraja mai cike da alheri kuma hakika na yarda da kyawawan halayenki Masoyiyata, kawai ina so in ce ina ƙaunarki sosai.
Ruhin jikina, Ina so kawai kice kina sona fiye da kowa. Kina sa na ji daɗi fiye da kowa. Saboda haka ina son ki fiye da miliyoyin mata. Inaso kiyi farin ciki.
Ina mamakin abin da zuciyata ta zama tun da na haɗu da ke. Nishaɗi dare da rana tunaninki koyaushe yana yawo a cikin ɗakunan zuciyata. Duk lokacin da nake bacci, nakan yi mafarkin ki duk da haka tunanina yana tunanin ki har sai na farka. Na nemi kadan na samu Qari, Na nemi karami an ba ni Babba, Na nemi dukiya guda daya amma an yi mani ruwan sama. Yanzu na jike a cikin ki Kin zama kamar lu'ulu'u kuma wannan yana tuna min cewa babu wani abu mai kyau da zai zo da sauƙi. Kina kama da jan yakutu, kuma wannan yana gaya mani yadda kika kasance na musamman. Kin zama kamar abun al'ajabi kuma wannan yana sanar dani yadda kikayi kyau. Ina son ki Abokiyar Rayuwata.
Kin sanya ni Shauki. Kaunarki a gareni yanzu itace taska ta musamman wacce ta cancanci kiyayewa fiye da komai. Duk lokacin da nake tare da ke, Zan iya sadaukar da komai domin kawai in kasance a gabanki domin hakan yana ƙara sanya ni nutsuwa. Ba za ki iya barina don wani ba sai dai cewa dole ne mu kasance tare har zuwa ƙarshen zamani.
An tsara ki koyaushe ki zauna a cikin zuciyata don haka ba zan rasa kiba a kowane lokaci. Don haka ki tsaya a cikin tunani na har zuwa karshen rayuwa. Ina son ki my gimbiya.
Ina son kina murmushi da fara'a. Ina sha'awar kyawawan shudayen idanunki saboda sun yi fice, Ina Qaunar salon rayuwarki. Ke babban tauraruwa ce wanda ba a saba da ita ba kuma saboda haka na sadaukar da zuciyata don ƙaunarki har abadan abadin.
Duk lokacin dana kwanta sai ina yawan ambaton tunanin ki, tinanin ki yakan mamaye hankalina ya bar min sarari don numfashi kuma ina son shi haka. Farin cikin da na samu na tuna ki a cikin zuciyata ya ishe ni iskar oksiji a gare ni in tsira. An halicce kine dan ni kadai. Allah ya zabe ki don kin dace da sararin samaniya na kauna a cikin zuciyata. Yanzu na cika Mutum mai iko domin ina da ke.
Babu wata shakka a cikin zuciyata cewa ina ƙaunarki ƙwarai da gaske. Ina fata zan iya gina maɓuɓɓugar da take zubar da ƙaunatacciyar ƙaunata domin ke don ki san irin ƙaunarki da kimarki agareni. Qaunar ki a cikin zuciyata tana ƙaruwa a cikin kowane second na rayuwata. fuskarki kyakkyawa ce wacce idan zan ambata, kuma halayenki masu kyau ne idan Za'a bada labari, soyayya ce take sa ni murmushi a duk lokacin da na gan ki. Ina son ki zuciyata.
Sonki baya gushewa, ya ba ni mamaki. Na kasance ina mamakin wace irin halitta ce ta musamman da Allah yayi, Hanyoyinki suna da Kawu cike da ban sha'awa, tausayi, Burgewa. Dole ne in zama mafi sa'ar da na same ki.
41. Ke tawa ce kuma babu abinda zai taba raba ki da ni. Kece farincikina, soyayyata da duk abinda yake sanyaya zuciyata. Ina son ku da dukkan zuciyata. A fuka-fukan kauna, ke tawa ce muna tashi tare kamar yadda tsuntsayen soyayya suke kaiwa zuwa matakin qarshe na Shauki inda muke morewa cikin soyayya da tausayi. Burina ya cika; kece farin cikin dana samu a rayuwata. Zo ki zauna da ni har zuwa karshen lokacin da Zanyi a Duniya.
Kullum ina son kasancewa tare da ke a kowane lokaci. Duk lokacin da nake tare da ke, nakan fi dariya. Don Allah koyaushe ki kasance tawa, har abada don haka zan iya ganinki har abada cikin soyayya. Ina Sonki da tausayinki.
Babu labarin soyayya da ya wanzu ba tare da zafin rai ya gauraye da farin ciki ba, muna iya yin rigima ko rashin fahimta da yawa amma hakan ba yana nufin ba za mu iya dawowa tare ba. Qauna ta gaskiya ba koyaushe take da laushi ba, amma duk da haka ba ta da tsauri. Baby, don Allah ki kasance tare da ni har abada. Ina son ki.
Ba zan iya tunanin yadda rayuwa za ta kasance ba tare da ke a rayuwata ba. Kin shigo rayuwata don tayar da ginshiƙan farin ciki a ciki. Tun lokacin da kika zama tawa, bani da wani dalili daya sa ni bakin ciki. Yanzu na fahimci irin sa'ar da zan samu wani abin almara mai kama da ke a rayuwata. Ina son ki babyna.
Babu wurin da zai rike sunanki har abada ba tare da an wanke shi ba. Na rubuta shi a yashi, an share shi, a kan dutsen har yanzu ban sake samu ba sai na fahimci cewa mafi kyawu kuma mafi aminci wurin rubutun sunanki shine zuciyata. Ina son ki Sarauniyar zuciyata!
Idan da ace ina son abu biyar, zan so kasancewa tare da ke har abada, ganin kina murmushi kowace rana, Ina fatan jin kasancewar ki a kowane minti na rayuwata. Ina so in taba ki in sumbace ki har abada kuma ina son in zama naki har zuwa ƙarshen zamani. Ina son ki.
Ranar farko da na hadu da ke na san dogon buri na ya zo ya wuce. Kece mai wa'azantar da zuciyata wanda nake jira tsawon wannan lokacin. Habibiyar zuciyata, kinsa naji na cika Burina, saboda kin damu sosai Dani, Yin tunani game da ke kamar abinci ne, ba tare dake ba, ba zan iya rayuwa tsawon lokaci.ba. Yanzu kece silar rayuwata domin yanzu na ganki a matsayin makamashin so na Qyasta wutar kauna a cikin zuciyata.
Kalaman Soyayya a Rubuce
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan,
lokaci na shud’ewa soyayyar ki na k’aruwa a cikin zuciyata, a lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta,
kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina k’aunar ki.
Matata Uwar ‘ya’yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d’aya, ina cike da zumud’in son dawowa domin cin girkin ki mai dad’i. ki kula min da kan ki, sai na dawo. Ina son ki matata.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haska idaniya, haka kuma kalaman ki tamkar siga suke ma`abocin zaki
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haska idaniya,
haka kuma kalaman ki tamkar siga suke ma`abocin zaki A yayinda naji muryarki nakan manta da duk wata hayaniyar da kunnuwa na suka saurara a tsawon yini guda,
Kalamanki sukan natsar da zuciyata inji tamkar bata taba shiga wata damuwa ba kece muradi na. Babu wani abinci da yake yi min dad’i a baki na matu’kar ba ke kika girka shi ba. Ina nan tafe izuwa gare ki da shirin zuwa cin abincinki mai dad’i.
Ki kula min da kanki. Burin kowane masoyi yasami abokiyar rayuwa tagari, a kullum ina yiwa Allah godiya da yabani nagartacciyar mace “irinki”
Ba zan iya musalta adadin yadda sonki yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana.
Ina son ki matata. A rayuwata na koyi yadda zanyi murmushi, yadda zanyi aiki tukuru, yadda zanyi soyayya, yadda zanyi kuka, amma ban koyi ta yadda zan jure rashinki
Nesantar ki babban aiki ne da yake jigata zuciyata, dama ace kin san halin matsi da takura da nake shiga da kuma shaukin son kasancewa a tare da ke da nake ji cikin zuciyata a dukkan lokacin da na nesanta da gida.
Trust is the greatest struggle for most lovers.
* Aminci shine mafi girman fafutuka ga mafi yawan masoya a rayuwar soyayya
* Trust is the root of love for a lover.
* Aminci jijiyane naso ga masoya
* If a lover loses trust in his ‘ partners, he will immediately shut down and withdraw.
* Idan masoyi ya rasa aminci a tare da abokin tarayyarsa, da‘ sauri zai gudu ya janye;
A. marriage is a collaboration of two hearts that join together to overcome the obstacles of life and create an atmosphare of sharedx pleasure and deeper love.
* Aure gamayya ce ta zukata biyu da kew' haduwa ' ga tunkarar kalubalen rayuwa gami da kirkirar yanayi na dadi da zurfaffan so.
Ba zan iya musalta adadin yadda sonki yake lunkuwa a zuciya ta ba a cikin kowace rana.
Ina son ki matata. A rayuwata na koyi yadda zanyi murmushi, yadda zanyi aiki tukuru, yadda zanyi soyayya, yadda zanyi kuka, amma ban koyi ta yadda zan jure rashinki
Nesantar ki babban aiki ne da yake jigata zuciyata, dama ace kin san halin matsi da takura da nake shiga da kuma shaukin son kasancewa a tare da ke da nake ji cikin zuciyata a dukkan lokacin da na nesanta da gida.
I cannot leave you down, because you are my life, our love like a biggest garden in the world. I love you.
* Ba zan taba barin ki ba, saboda ke ce -rayuwata. Soyayyarmu tamkar babban lambu‘ ne ma'fi girma a duniya.’ Ina sonki.
I cannot leave you down, because you are my life, our love like a biggest garden in the world. I love you.
* Ba zan taba barin ki ba, saboda ke ce rayuwata.
SoYayyarmu tamkar babban lambu ne mafi girma a duniya. Ina sonki.
* your partner must Satisfy ydur body mind and soul.
Abokin tarayyarka wajibi ya gamsar da gangar jiki, zuci da ruhin ka.
A man needs a good wife, whom he can trust with his heart.
Namiji na bukatar mace ta kwarai, wadda zai iya aminta da ita a zuciyarsa.
Love is something beautiful and a feeling that one will, like etay catch. Love, is the feeling that‘ makes you feel alive.
So wani abu ne mai dkyawu, kuma wani yanayi ne da mutum zai so ya damke. So shi ne yanay‘m d3. kan sa kajika Raye.
I hope you understand that I will love you untill the end, because you are not just my girl. But you ‘ are also my best friend.
Ina fatan kin fahimci cewa zanso ki har karshen rayuwa ta, saboda bazan kasance budurwata kadai ba, ke Aminiyata ce har abada.
Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!
Soyayya shine a duk lokacin da kalli cikin idunuwar wani kaga dukkan abin da ka bukata, kamar yadda na nagani a idanun ki.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya.
A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji.
Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya. Ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri,
ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciyata. Fatana a kullum ki gamsu da cewa, Ina Son Ki.
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare.
Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka! Duk mai shiga tsakani na da ke magulmacine da zana ganshi, sai na tsole idanunsa.
Nabaki surruka na, ki adana su, ko ki binne, ke kadaice a zuciya ta har abada bazan manta da keba. Na futo wajen aiki hakan na nufin mun yi nesa da juna.
Amma ina son, ki san da cewa, a duk inda nake, a duk inda na shiga, ba zan rabu da tinaninki a matsayinki na mata ta da nake matu’kar so da ‘kauna ba. Ina nan tafe a hanya zuwa gare ki. Ki kasance mai tina cewa, ba ni da kamar ki. Ina Son Ki.
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SINADARIN RAYUWA TA.
SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
ZAN SO KI JI.
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
KE CE MURMUSHI NA.
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da
na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!
HMM!! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.
INA SON KASAN
CEWA A TARE DA KE HAR ABADA.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba.
Na Mata:
INA SONKA MASOYI NA!
Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!
MU KASANCE A TARE.
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!
INA FATAN MAFARKI NA YA ZAMA GASKIYA.
A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!
MASOYI NA.
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.
KA ZAMA RUHI NA.
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne ka
sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina
kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma’abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min
kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga jikina.
Slm allah sarki babynah dafatan ruwa basu taremin kaiba akace bidar halak da wuya allah baka halalinka kuma ya azzirtaka da halar dinka brk da shan ruwa
Babbar yarinya kin sace Zuciya ta, tunaninki Dakuma Jin muryarki sune muradina dafatar zaki wayi gari lafiya Love U!
Sorry babynah kasan wllh inasonka banasone ka cutamin amma kayi hkr kaji my blood and heart
0 Response to "Kalaman soyayya 2023"
Post a Comment