Alheri ga Ɗalibai da Suka Rubuta Jarabawar WAEC ta Afrika ta Yamma Daga 1999 Zuwa 2022 Hukumar WAEC ta Fitarda Shirin WAEC Digital Certificate
Alheri ga Ɗalibai da Suka Rubuta Jarabawar WAEC ta Afrika ta Yamma Daga 1999 Zuwa 2022 Hukumar WAEC ta Fitarda Shirin WAEC Digital Certificate
Hukumar shirya jarabawar WAEC ta Afrika ta Yamma ta kaddamar da wani dandali mai suna WAEC Digital Certificate wato dijital satifiket inda ɗalibai da suka zana jarabawar WAEC zasu iya samun original copy na satifiket din WAEC kai tsaye ta hanyar amfani da lambobi ko wayar hannu da na’urorinsu na yanar gizo.
Ranar 20 ga watan Oktoba 2022 aka kaddamar da dandali na WAEC na satifiket na dijital. Kimanin dalibai miliyan 2 ne ke yin jarrabawar kammala sakandare ta yammacin Afirka (WASSCE) a kowace shekara. Sabuwar takardar shaidar dijital tana samuwa ga waɗanda suka yi jarrabawar tun daga 1999.
Yadda WAEC Digital Certificate Platform Ke Aiki
Mataki na farko domin mallakar jarabawar WAEC digital shi ne ka zaiyarci shafin yanar gizo-gizon su dake kasa
https://portal.waec.org/account/register
Shigarda bayanai kamar su Candidate Number, yana da kyau mu sani cewa shidai wannan sabuwar fasaha da WAEC tafitar ba kyauta bane biya akeyi ta hanyar saka kuɗi a asusun wallet da suka tanada a shin nasu.
Fatan Nasara
0 Response to "Alheri ga Ɗalibai da Suka Rubuta Jarabawar WAEC ta Afrika ta Yamma Daga 1999 Zuwa 2022 Hukumar WAEC ta Fitarda Shirin WAEC Digital Certificate"
Post a Comment