Aikin Enumerator a Kungiyar Street Child ga Masu Kwalin Sakandare, NCE, Diploma da Degree
Aikin Enumerator a Kungiyar Street Child ga Masu Kwalin Sakandare, NCE, Diploma da Degree
Street Child kungiyar agaji ce ta Burtaniya, wacce aka kafa a shekarar 2008, wacce ke da nufin samar da damar ilimi ga yara masu rauni a duniya, Street Child ta fara aiki a Saliyo shekarar 2008 kungiyar na aiki tare da karamin adadin yara masu yawo kan titi don canza rayuwar yara fiye da 50,000 a Saliyo, Laberiya da Nepal. A shekarar 2017 kungiyar ta kaddamar da aikinta na farko a Najeriya domin taimakawa yaran da rikici ya shafa a Arewa maso Gabas su samu ilimi.
A yau ne kungiyar ta fitarda da sanarwar daukar aikin Enumerator inda ta bayyana cewa Enumerator zai himmatu ne wajan karbar bayanai amintattu wato qualitative/quantitative field data and data entry using mobile platforms (e. g koboCollect or SurveyMonkey).
Abubuwanda Ake Bukata
- Mai cikewa dole ne ya kasance yanada Takardar Sakandare, OND/HND/Bachelor’s degree
- Ya kasance yanada gogewa acikin aikin Enumerator
- Ya kasance uanada saukin fahimta da iya zamantakewa
Yadda Zaku Cike
Idan kunada ra'ayin yin aikin Enumerator a kungiyar Street Child kubi wannan shafin domin cikewa https://forms.gle/Q5xXk3k3fPNaTU4E9 yakin ku aika C.V naku a wannan adireshin email dake a kasa hr.nigeria@street-child.org
ALLAH Yasa Mu Dace Baki Daya
0 Response to "Aikin Enumerator a Kungiyar Street Child ga Masu Kwalin Sakandare, NCE, Diploma da Degree"
Post a Comment