Zaman Aure ga Budurwa
Zaman Aure ga Budurwa
Da farko shidai ibada aurece kuma sunnah ce ta Annabi Muhammad (SAW).
Aduk Inda akace mutum ibada zaiyi sai ya jajirce yasa tsoron Allah duk abinda zai aikata.
Allah(SwA) yasanya rayuwa tsakanin jinsi biyu wato namiji da mace Shi zama na aure inaka daurashi fatan zama Nahar abada akemai duk da hauwa nacewa zo muzauna zo musaba:ma'ana ana iya Samuwar da zatakai GA anyi saki shiyasa ake yawan fada ma duk wani Wanda zaiyi aure dama wadanda ke ciki cewa auree Dan hakuri ne shiyasa hakuri Yana da a bugun aure.domin Indai babu hakurin nan bugun zatayi wahala.
Da farko dai Zan Fara da bangaran Maza tunda ance arrijalu kauwwamuna alanisa'i.abisa. Ka'idar musulunci Indai namiji ya Auri mace ya dauki nauyin ciyar da ita da kuma tufatar da ita,dadakuma sauran bukatu na tau da kullum dabasufi karfinsa ba gwargwadon abinda yake samu a yau da kullum wajibine ya amince da wadannan abubuwa Kafin abashi aure.kekuma mace zakiji iyayenki na cewa Shifa aure Dan hakuri ne kibi mijinki sauda Kafa inyace kiyi kiyi inyace bari Bari saboda aljannar ki na tafin kafarsa dole sai kin jajirce domin neman aljannarki a gobe kiyama..
Babban Abu na farko da rayuwar take bukata shine fahimtar juna idan ana samun fahimtar juna tsakanin ma'aurata to babu shakka shakka zatayi dadi so communication is very very very very very important tsakanin ma'aurata Wanda hanyar kawai zaku zauna kuji matsalolin juna har Ku samu mafita
Sannan salon na da dadi in ana Kara nunawa juna so da kauna ana fadawa juna kalamaimasu dadi da sanyaya zukata
A Zama na aurene kuma Allah zai azurtaku dasamun karuwa wato zai Baku haihuwa Wanda kune zaku tarbiyartar dashi kubashi sutura Ku kula da bayyananshi kukula da mu'amallarshi da mutane da dai sauransu.
Kowa na taka rawar rawa Kan tarbiyar yaranshi Amman ta uwa tafi girma saboda ita ke zaune dasu a gida ita tasan shige da fitansu ita tasan komai nasu sabanin mahaifi da sai ya dawo yake nashi kokarin.
Shi zaman aure Yana bukatar kyautatawa domin Jin dadi da Samun lafiya Mai dorewa.
Zaman aure zamane na gaskiya da rikon Amana dakuma da kuma rike sirrin rayuwar tsakanin Ku anaso ma'aurata su kasace masu rufawa junan su asiri .
ABUBUWA BIYAR DA masu son rai:
1:Rashin kunbiya kunbiya:duk Halin da kake ciki Karka Bari matarka taji labari wani waje ko aure zaka Kara yakamata tafarajinshi daga. Bakinka ba'a bakin wasuba.
Kema mace duk Halin da kike ciki ki tabbatar kin fadawa mijinki in fita zakiyi kifadamasa duk inda zakije kifadamasa Kar a gano Azo a fada masa a samu matsala.
2:GASKIYA DA RIKON AMANA:Kurike amanar junan Ku.gaskiya itace wani Babban makami dake aure .yarda da junan ku shine zai zama ginshikin zaman Ku tare Indai babu yarda to ko auren ya daure zai zama Mai yawan tawa.
3:GIRMAMA JUNA DA MUTUNTAWA:
Yazama wajibi ki GIRMAMA mijinki da muradunshi Indai har Bai kaucewa hanya ba shima yazama wajibi ya girmama naki muradun.
Kar ma'aurata su zamo masu cin damar junansu da wulakanci wannan dabi'un suna warware aure dole sai mun kula sosai da irin lafazin da zamu dinga fadawa junan mu.
Yakamata ma'aurata sugane cewa Dan Adam na buƙatu da mutuntawa.
4:SAUKE HAKKOKIN JUNA: yazama wajibi GA ma'aurata su buqatar junan su HAKKOKIN da suka rataya akansu.
Dole ne Miji ya sauke hakkinshi na ciyar dake da tufatar da. Ke da duk wani Abu dayake hakkin SA dole ya sauke Shi.
Haka kema mace dole ki kula da duk mijinki da kula da jinshi ganinshi da abunda bashikenan ba kiyaye sirrin mijinki,kyautatawa miji,da dai sauransu.
5:KAUNA DA YABAWA:
Indai har zaman aure ne ya hadaku to dole a dinga nunawa juna kauna da wadannan suna Kara sa zaman aure yayi karko
A sami masu yawan tausayawa juna Dan tausayi nakara dankon soyayya
Idan matarka NADA ciki nunamata Kafi kowa tausaya Mata Ka kula da ita sosai zataji dadi.
Haka kema kizama Mai yawan tausayawa mijinki musamman in yana Cikin yanayin Rashin Jin dadi.
Akwai da yakamata ma'aurata su kiyaye:
1:mutunta iyaye da dangin juna
2:almubazzaranci
3':a guji wulakanci
4:a guji raina juna
5:A guji manta alkairi
6:yiwa juna uzuri
7:iya magana
8:yawaita godiya.
0 Response to "Zaman Aure ga Budurwa"
Post a Comment