Zafafan Kalaman Soyayya 2023
Zafafan Kalaman Soyayya 2023
Masoyiyatah Ina gudun Fushinki fiye da gudinda nake ma Tsoran kamuwa da Talauci Kaunarki tabi jikina Ina sonki fiye da yadda nake son Kudi.
Kai Alherine Kuma Ni'ima acikin Rayuwata Kai watane da haskensa ya haskakka zuciyata inajin dadi idan na kalleka doran kasa nacike da Cirrai Sararin Samani nacike da taurari Duniya nacike da Halittu Nikuma Zuciyatah nacike da Tsantsar so da kaunarka.
so wani abu ne mai kyawu, kuma wani yanayi ne da mutum zai so ya damke. 'So. shi ne yanayin da kan sa ka ji ka a raye.
Ina _fatan kin fahimci cewa zan so ki har karshe, saboda ba kin kasance budurwata kadai ba, ke ce Aminiyata.
KIN ZARCE SAURAN MATA
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SINADARIN RAYUWA TA.
SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
ZAN SO KI JI.
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
KE CE MURMUSHI NA.
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da
na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!
HMM!! KI YARDA DA NI.
A dukkan lokacin da dare ya yi, ki d’aga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki, karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm! Ki Huta Lafiya.
INA SON KASAN
CEWA A TARE DA KE HAR ABADA.
A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya. A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare. Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji. Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan ta6a canjawa a kan hakan ba.
Na Mata:
INA SONKA MASOYI NA!
Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!
MU KASANCE A TARE.
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!
INA FATAN MAFARKI NA YA ZAMA GASKIYA.
A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka. Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!
MASOYI NA.
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.
KA ZAMA RUHI NA.
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne ka
sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina
kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma'abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min
kiyi min agaji, ki tausaya min, ki tallafe ni, ki amince dani a cikin zuciyarki, sonki ya gama shiga jikina.
kada ki bar ni shawagi tamkar tsuntsu a sararin SAMANIYA.
♥♥FARILLAN SOYAYYA♥♥
1 Tsoron Allah.♥
2 Hakuri.♥
3 Rikon Amana.♥
4 Kulawa.♥
5 Rikon Alkawari.♥
6 Fadar Gaskiya.♥
7 Tsafta.♥
8 Kwalliya.♥
9 Kalaman Soyayya.♥
10 Kunya.♥
11 Kishi.♥
12 Kulawa.♥
13 Iya magana.♥
T ♥♥SUNNONIN SOYAYYA♥♥
1 Zuwa zance.♥
2 Kyauta.♥
3 Tattali.♥
4 Yabawa.♥
5 Tarairaya.♥
6 Kawar da kai.♥
7 Mutunta juna.♥
♥♥MUSTAHABBAN SOYAYYA♥♥ 1 Shagwa6a.♥
2 Iya kallon SO.♥
3 Dawainiya.♥
4 Mutunta dangin juna.♥
5 Iya tura sako a waya.♥
6 Kiran juna a waya.♥
7 Yiwajuna Murmushin Soyayya.♥
♥♥ALAMOMIN SO♥♥
Akwai alamomin dake fitar da so, masu
tarin yawa suke bayyana soyayya ga kadan
daga ciki.
1. ♥KUNYA♥
da zarar soyayya ta fara shiga ko da ba a yi
furuci ba
sai kunya ta shiga tsakani, sai
aga masoyan a junansu suna jin kunyar juna.
2. ♥YAWAN KALLO♥
wannan alamace ta soyayya,misali ta hanyar
yawan satar kallo, idan masoyi yana kallon a
bin
son shi da ya waiga sun
hada ido xai kawar da kansa.
3. ♥FADUWAR GABA
♥
a lokacin da soyayya ta fara shiga xuciyatr
saurayi ko budurwa xa ka samu da zarar sun
hango juna kowa sai gabansa ya fadi
4. ♥YAWAN AMBATO♥
matukar soyayyar saurayi ta kafu a zutciyar
budurwa ko ta budurwa ta shiga ran saurayi
xaka samu yana yawan kawo labarin wanda
yake so din ako yaushe,
kuma duk inda ya ji an fara labarin wanda yake son xa
kaga ya nutsu yana sauraro.
5. ♥TAUSAYI♥
soyayya musamman ta gaskiya tana tare da
tausayi. Kuma sau tari zakaga masoyi ko
masoyiya suna matukar tausayi ga junansu
har hakan na haifar da damuwa ko saurin
kuka musamman mata. Assalamu Alaikum. Barka da hawa online!!!
Akwai dadin karantawa sosai.
0 Response to "Zafafan Kalaman Soyayya 2023"
Post a Comment