Yadda Zaku Samu MTN data offer
Friday, September 2, 2022
Comment
Yadda Zaku Samu MTN data offer
Akwai wata MTN data offer, an jima ana amfani da ita amma naga kamar mutane da dama basu ankare da ita ba.
Idan wata buƙatar gaggawa ta amfani da data ta kamaka amma baka da ita, kuma baka son yin sub a lokacin ko kuma kana ganin zaka takura, in dai katin dake cikin layinka ya kai ₦50 ko sama kawai ka danna wannan USSD code ɗin *131*25# za su ciri ₦50 su baka 200MB (expiry date 2weeks).
200MB ai Zata iya isarka ɗan ƙaramin amfani na gaggawa, idan ma kana jin ba zata isheka ba sai ƙara kiran USSD code ɗin ka ƙara ta ₦50 har iya yadda zata isheka amfanin da kake son yi.
Amma kasancewar offer ce to inaga ba kowanne layi suke baiwa ba.
0 Response to "Yadda Zaku Samu MTN data offer"
Post a Comment