-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Zaman Aure

Yadda Ake Zaman Aure

Yadda Ake Zaman Aure

Da farko dai shi aure ibada ce kuma sunnah ce ta Annabi Muhammad (S.A.W).

A duk inda akace mutum ibada zaiyi kuwa sai ya jajirce  yyi dagaske kuma yasa tsoron Allah duk abinda zai aikata.

Allah (S.W.A) ya sanya zamantakewa ta aure a tsakanin jinsi biyu wato Namiji da Mace shi zama na aure idan aka hadashi zamane da ake fatar ya dore har abada  duk da hausawa kance zo mu zauna zo mu saba.. ma'ana shine watarana zaa samu sabani har ya kasance yakai ga Yanda baa so wato saki yashiga tsakani har yazamana Allah ya raba masoya shi yasa a kullum ake dada gayamana da cewa sai mutum yayi hakuri kuma hakuri nan dole ne domin idan babu shi zamantakewa zatayi wahala.

Zan fara daga kan maza a zamantakewa ta aure kafin bayani akan mata ta biyo baya  tun a bisa ka'idar shari'ar musulunci yasakance cewa idan Namiji ya aure mace ya dauki nauyin ciyar da ita shayar ta ita da kuma tufatar da ita da kuma sauran bukatu na rayuwa wadanda basufi karfin sa ba da kuma gwargwadon  abunda yake samu a yau da kullum wajibi ne ya amince da wadannan abubuwan kafin a bashi yarinya sai ya jajirce yaga cewa duk abubuwan dasuka wajaba akansa ya sauke na nauyin da ubangiji ya dora masa hakazalika akan mace zakiji iyayenki na gayamiki dacewa shifa aure hakuri akeyi ki zauna da Mijinki lafiya ki bishi sau da kafa idan yace kiyi kiyi idan yace ki bari ki bari domin ta karkashi kafafuwansa ne aljannar ki take don haka sai kin jajirce domin neman aljannar ki a gobe kiyama.

Babban abu na farko da kyakyawar zamantakewa ta aure take bukata shine fahimtar juna. Idan ana samun fahimta a tsakanin ma'aurata to ba shakka zamantakewa zatayi sauki kuma zatayi Dadi. Communication is very important a tsakanin ma'aurata wanda shi kadai ne hanyar da zaku zauna ku fahinci junanku domin idan abubuwa na faruwa kuma b communication na a zauna a warware matsala tor ana dada fadawa acikin matsala ne.

Aure akan ginashi akan zurfaffar soyayya anaso a koda yaushe wannan soyayyar ta dore sai anayi ana rika nunawa juna soyayya domin idan ba haka b soyayyar zata daina tasiri ana dan yi ana kalamai masu sanyaya zukata.

A Zama na aure ne Allah zai a zurta ma'aurata da samun karuwa ma'ana su samu haihuwa wanda a lokacin ne Allah ya baku wani kiwo dazaku matukar Kulawa dashi zai azurtaku da 'yaya dazaku Basu tarbiya mai kyau ku kula da cinsu da sururar su da shansu da abokan mu'amalarsu da duk wani sauran bangare na rayuwarsu.

Kowa yanada rawar da yake takawa a gurin tarbiyar yara. Tarbiyar uwa mace tafi tasiri a wurin 'yayanta domin itace ke zaune dasu a gida  a koda yaushe don haka itace zafi Kulawa da alamurran su da shige da ficen su domin kuwa shi Namiji yafi bayasanin abubuwan dake gudana a gida sai ya dawo.

Shi Zama a tsakanin ma'aurata Yana bukatar kyautatawa domin jin Dadi da samun kyakyawar zamantakewa

Zaman aure zamane na gskya da rikon amana da kuma rike sirrin zamantakewar ku..anaso ku kasance masu gaskiya a tsakanin ku da kuma rike amana da rufawa juna asiri.

0 Response to "Yadda Ake Zaman Aure"

Post a Comment