Yadda Ake Zama Da Miji Ma'aikacin Gwamnati
Yadda Ake Zama Da Miji Ma'aikacin Gwamnati
Shidai Zama kowane iri ne sai mutum yayi hakuri duk abunda kike ki ko kike gani ana miki na ba daidai b a koda yaushe nakance kisa Allah a ranki sannnan ki tuna dacewa shifa aure ibada ne so duk abunda kikeji da kin tuna wannan Zaki samu sauki acikin zuciyar ki .
Da farko dai shi Zama da Miji Ma'aikacin Gwamnati ba shida wata illa saidai watarana in one way or the other zaka bukaci mutum a kusa dakai bayanan Yana wurin aiki kuma idan kinsa tunani kinyi la'akari zakiga cewa aikinan fa Yana yinshi ne domin ke da 'yayan ki kuma idan baa fita a nemo ai watarana zaa wayi gari ba ko abin Karin kumallo a gidan
Don haka idan kin kasance kina daya daga cikin matan da mazajensu ke aikin Gwamnati b wai damuwa dakiyi b aa kiyi farinciki kuma ki kire Mijinki hannu biyu ki bashi Kulawa ta musamman ai abu ne wanda ma zakiyi farin ciki dashi domin mutum dubu suna neman aikin Basu samu ba
Idan kinsan Mijinki Yana fita tunda safe balle akasari aikin Gwamnati ma ai tun safe ake fita a shiga office ki tashi tunda wuri ki gyara gidanki kiyi abin buda baki ki gyara yaranki idan suna zuwa makaranta ki shirya su yazamana dai koda maigida zai fita kin gyara komai kin hada komai idan da abinci yake zuwa office koda zai tashi kin kammala komai yazama ready shima zai ji Dadi a ransa ki je ki gyara shi ki zaba masa kayan da zai saka ki bashi breakfast yaci yanaci kina masa kalamai masu sanyaya zuciya idan ya kare zai fita ki rakashi har bakin gate kimashi addua ki watsa masa kisses a fuska da bakinshi kice Allah ya tsare miki shi yadawo dashi gida lafiya cikin aminci .
Uwargida ina mai tabbata miki idan har kina masa haka a koda yaushe zai kasance cikin tinaninki har sai ya dawo gida Yana office Amma hankalinsa Yana gida saboda kin bashi duk abunda yake bukata zakiga ma watarana lokacin tashi daga aikin baiyi ba Amma zaice shi gida yakeso ya tafi saboda kin Riga kin sace masa zuciya baya ganin kowa idan ba ke b kuma still idan ya fita office Zama bai same ki b idan kin kwatanta ya danyi Kamar 2 hours haka a office sai ki dauki wayanki ki dinga aika masa da sakonin soyayya da kuma dan picture haka hakan zaisa yaji Dadi kuma yaji b wanda yakeson gani idan ba ke b koda kuwa gaya wata a can wurin aikin bazai damu b saboda Yana samun Kulawa ta musamman a gidansa.
Idan Mijinki Yana kai dare a wurin aiki kiyi hakuri ba komai bane kin Riga kinsan lokacin dawowarsa saiki hada masa abincin sa kafin ya dawo ki gyara yaranki kiyi wanka kiyi ado Yanda da ya shigo a gida yaji baya bukatar komai idan bake b shi kuma a lokacin ya dawo yaci abinci ta huta yara sunyi bacci sai ku zauna ku samu time yabaki time dinki ku tattauna sannan a biyawa juna hakki na zamantakewar aure idan har kina samun wannan a wurin Mijinki ma'ana idan yadawo daga aiki zai baki time dinki kiyi fira ayi dariya tor Banga abun damuwa b anan dama mafi yawan abunda kesa mata basa son miji Ma'aikacin Gwamnati shine wasu mazan da zarar sun dawo gun aiki zakiji sunce sun gaji of course akwai gajiya Amma iyalinka sunada hakki a kanka wanda yazama wajibi ka sauke shikenan ita macc ba tada time a wurinka wanda hskan bai dace b
In conclusion wadannan hanyoyin da shawara dana lissafa a sama sune mafi inganci da Mace zatabi ta zauna lafiya da Miji Ma'aikacin Gwamnati.
Allah yasa mudace yakuma bamu ikon aikatawa.
0 Response to "Yadda Ake Zama Da Miji Ma'aikacin Gwamnati"
Post a Comment