YADDA AKE ZAMA DA MATA YAR KASUWA
YADDA AKE ZAMA DA MATA YAR KASUWA
Darko dai auren mata yar kasuwa yanda amfani ,kuma yana da rashin amfani, amfanita na farko idan mace tana kasuwanci idan miji bayada to zata taimaka ga lalurorin gida kafin Allah yabashi,to bazata tsaya da sai yakawo abida za a dafa ba,ko kuma irin biyan kudin marantar y'ay'an su idan ankayi rashin a bayada su matan sukan tamaka su biya ,ko kuma kamar lalurar kayan salla mace yarksuwa takan taimakama miji tayima yaran kayan salla ,mafiyawanci idan miji yayima yaro kala biyu to zakaga mace yarksuwa tayima yaron kala uku kaga biyar kenan sannan kuma duk wasu matsalolin da suka taso idan mijin bayanan zata iya walwale su kafin ya dawo gida kamar irin kudin makarantar yara da sauransu ,bayan haka kuma idan mace na kasuwanci koda wata matsala ta rashin lafiya ta kama wani daga cikin y'ay'an ya idan mijin baya gida to zata iya kula da yaran ba sai tajira mijin ba tace sai yadawo sannan zai kaisu acibiti ,To bayan haka kuma kwai rashin amfanin kasuwanci idan ba a bi abin yadda yakamata ba ,domin ko komi yana da tsari ba ason ayi abu kara zube , kowane abu yanada mahimmanci kuma yana rashin mahimmanci,1-dole ne mace da take kasuwanci ta kula da tarbiyar y'ay'an ta bawai idan tafita ba sai tagadamar dawowa ba sannan ta dawo ba ,basan abinda y'ay'an ta suke cikiba ko da ko tabar wadanda suke kula dasu ,itama ya kamata tarinka yi tana dawowa tana kula cinsu da shansu da kuma tarbiyar su,kada tabarsu suna ta abinda sunkaga dama kuma tarinka dawowa kowane lokaci taga damar dawowa kada tasa takamammen lokacin ta nadawowa gida don ta gane abinda ke gudana agidan donko da yaranda ke gidan da matar da take kulawa dasu kowa zai iya abinda yaga damar yi domin ko akwai wadasu halaye mafiyawancin yara wadanda idan mahaifiyarsu batanan zasu iya yinsu ,idan kuma tananan baza suyi suba,to don haka duk wadda a yarkasuwa dole ne ta kula .sannan kuma kamar sa tufafinsu musamman y'ay'a Mata wani lokaci idan mahaifiyarsu tananan zakaga sun sa kayan kwarai amma idan bata nan sai kaga sunsa sutura wadda ransu kesu ,wadda zata zubarda kimar gidan don sunsan iyayen basu nan musamman baban nasu tunda kocen namiji ba cika zama giyakai ba .Bayan haka kuma mata yarkasuwa baga y'ay'an kadai matsalar ta shafa ba harma ga mijin don ko ba kodayaushe idan yadawo dawurin neman abinci yake samun ta agida ba koma abinci yar aiki keyi ko kuma y'ay'anta sukeyin abincin dole ya hankura duk yadda sukayi shi yaci shi hakanan donko baganta ba balle yace ga abinda yakeso adafa mai ba ,to don haka mata yarkasuwa kula a gyara inda matsaloli suke domin asamu aci amfanin kasuwanci.
0 Response to "YADDA AKE ZAMA DA MATA YAR KASUWA"
Post a Comment