-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Zama Da Masifaffen Miji

Yadda Ake Zama Da Masifaffen Miji

Yadda Ake Zama Da Masifaffen Miji



Da farko dai magana ta gaskiya Zama da masifaffen miji akwai wahala kuma bashida dadi saboda kullum mutum zai zauna a takure abu bai taka kara ya karya ba a dinga masifa kuma shi masifaffen mutum bawai sai anyi masa laifi yake masifa baa aa abunda ya riga ya Zama mishi jiki wanda ko baayi laifi ba zai zamana maganarsa ta kirki ma sai ya saka fada a ciki wanda hakan sam bai dace ba. Masifa batada Dadi idan Allah ya hadaki Zama da Miji Mai masifa yar uwa Kiyi hakuri duk da nasan cewa akwai bacin rai sosai a tare da hakan Amma hakuri a kullum shine gaba a zamantakewa ta rayuwar aure Kiyi masa addua Allah yyi masa saukin masifan dayake sannan ki dinga yi kina dorashi akan hanyar daidai kina masa nasiha da cewa abunda yakeyi bai dace ba har Allah yasa ya daina  sannan kada kice a ranki wai kin gaji da yimasa nasiha da azashi kan hanya aa ki dage ki jajirce ita shiriya tana gurin ubangiji kuma shike shieyarsuwa a lokacin da yaso kuma yaga dama don haka shine tun a farko nace sai anyi hakuri mai tarin yawa sannan bawai kama biyemishi zakiyi ba idan ya fadanshi aa ki mai ladabi sannan kada ki tanka shi har sai yakare domin idan Yana masifa kekuma Kika biye masa tor abun zai wuce inda baayi tsammani ba ko Allah Yana cewa idan dayanku yazama wuta tor daya ya Zama ruwa masu sanyi so that a samu damar kashe wutar da dayan ya kunna.. ma'ana a nan shine domin a samu maslaha da kuma zaman lafiya bazaa taru a Zama daya ba kowa ya kunna wuta ba mai kasheta shiyasa hakurinnan wajibi ne kuma idan ana addua Inshallah komai zaiyi sauki kuma yazo ya wuce Kamar baayi ba  sannan kada kice masifar Mijinki tayi yawa ke bazaki iya Zama dashi ba ya rubuta miki takardar ki aa idan kinyi hakan bashine mafita a gareki ba Kiyi hakuri ki zauna a gidanki keda yayanki ki gayawa Allah damuwarki shine kadai zaiyi miki magani.

Sannan kada kice don fadanshi ko masifarshi bazaki yimishi biyayya ba ko ki sauke nauyi na hakkokin aure da Allah ya dora miki Kiyi masa, kada ko da wasa ki gwada wannan domin idan kinyi hakan ko kina ga hanyar sabawa mahaliccinki ne kedai kawai duk abunda zakiyi kisa a ranki danallah kikeyi ba danshi ba kuma ba dan halinshi ba idan kinyi hakan ko kinayin hakan to ba shakka Inshallahu Allah zai duba irin biyyarki a gareshi dakuma hakurinki da Mijinki yayi miki zabi da mafita ta alkhairi domin kuwa Allah yanason bayinsa masu hakuri sannan banda daukar shawarar kawaye domin wata zata iya kashe miki aure koda kuwa kinason Mijinki a Yanda yake masifa din. Allah ya karemu da maza masu masifa sannan wanda ke da sarar yin masifar Allah ya shirya su yakuma sa subari sugane ba abu bane mai kyau .

Allah yasa mudace Amin.

0 Response to "Yadda Ake Zama Da Masifaffen Miji"

Post a Comment