-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

www kalaman soyayya com

www kalaman soyayya com

www kalaman soyayya com

Yi murmushi idan kaga mai sonka, zai ji dadi. yi murmushi idan kaga mai kinka, zaiji tsoro. yi murmushi idan kaga wanda yabarka, zai yi dana sani. yi murmushi idan kaga wanda ka sani da wanda baka sani ba. murmushi kwarjinine ga namiji, adone ga fuskar mace. ku kasance masu yawan yin murmushi saboda nuna farinciki a rayuwa. banda yawan dariya domin tana kashe zuciya. Allah Kasa Mu Dace Ameen,

Masoyiyata abar kaunata ki sani ina sonki ina kaunarki son da nake miki har ya kai ga…..ko da idanuwana a rife suke ke nake gani idan na bude su ke nake son gani. Ko da ba na tare da ke ina jin motsinki a cikin jikina Lokachin da nake tinaninki, kadaici shi ya fiye min komai dadi. Me ya sa kina rayuwa a cikin jikina ni ma ina rayuwa a cikin jikinki amma duk da haka nake jin tsakaninmu da nisa?

Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraro da duk wani haske. Haske a idanuwa na, Ina fatan dai ba fushi kike da ni ba. Zan iya manta komai amma ka sani ba zan iya mantaka ba haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka ba, hakika daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa, bakin ciki y ziyarci zuciya ta wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala.

Idan har na ce zan iya na yi karya domin ni kadai na san irin halin da nake ciki na rashin jin dadin tafiyarka. Zuciyata na tafasa har nakan ji tamkar na fashe da kuka ka sani cewa, wannan sakon duciyata na sanar da kai, hannu aikinsa rubutawa ba wai ina fada ne don tsari ko don ka ji dadi ba.

Amincin Allah ya tabbata a gare ki ya ke wacce ta fi tauraro da duk wani haske. Haske a idanuwa na, Ina fatan dai ba fushi kike da ni ba. Zan iya manta komai amma ka sani ba zan iya mantaka ba haka kuma zan iya jure rashin komai amma ba zan iya jure rashinka ba, hakika daga jiya zuwa yau ina cikin kunci mara misaltuwa, bakin ciki y ziyarci zuciya ta wanda har kawo i-yanzu ba na jin zan iya kula wani cikin walwala.

A duk inda kika je ki tabbatar da cewa ina biye da ke, ko da ban zo a zahiri ba to kuwa zan zo miki a cikin bacci, ke ma za ki bayyana a cikin mafarki na, mu kasance a tare da juna, cikin wani lambu mai cike da furanni mabambanta launi. Begenki shi ne abun yina a kullum. "

"A lokuta da yawa, kalmomi sukan gagari furtawa, domin bayyanar miki da adadin yadda sonki yake kara mamaye zuciya ta a kullum. Bana fatan zuwan ranar da zan gaza wajen nemo kalmomin da zan furta miki cewa INA SON KI. Hmm! Karda Ki Manta Da Ni a Rabon Naman Sallah. Barka Da Babbar Salla Masoyiya ta."

"A lokacin da na fara ganinki, sai da na rintse idanuwana domin fahimtar cewa, shin a zahiri nake ganin ki, ko kuma kawai kin gifta ne ta cikin tinani na. Lallai ke din ta daban ce, kina da wata baiwa wadda ba kowa ne zai gane hakan ba, daga ciki akwai ta zazzakar murya da tattausan murmushi. ina kaunarki"

"Ina son wasu abubuwa guda uku a rayuwata:- Rana da wata sai kuma mafi soyuwa daga cikinsu a gare ni shine ke. Ina son rana ne domin ta haskaka mini safiya, ina son wata domin ya haskaka min dare, ina sonki ne domin mu rayu tare har abada. Barka Da Babbar Sallah Masoyiya ta."

"Ke tauraruwa ce a cikin duniya, haka kuma ke duniya ce ga wani tauraro, zan so ki amince mu rayu a tare cikin shauki da ‘kaunar juna. Hmm! Zan kuma zo na kar6i nawa naman sallar. Barka Da Babbar Sallah. "

"Farin ciki mara misaltuwa kan ziyarci zuciyata a dukkan lokacin da na ji sautin muryarka, murmushinka babban abu ne da yake yaye damuwata, bana kasancewa dai dai da shakar numfashi ba tare da tinaninka ba a cikin zuciyata, kaine d’aya tilo da na damkawa ragamar zuciyata. Ni taka ce har abada, Ina sonka."

"Nawaan ko ka san cewa cikin kowace rana kyawunka da d'akaruwa yake a cikin idanuwana? Tabbas ba zan dakata daga begen kallon kyakkyawar surarka a zahiri da kuma cikin zuciyata ba har sai gobe hasken idaniyata, hmm! karda ka manta a goben ma sai gobe. Ina sonka Nawaan "

"Tabbas Furanni suna da ‘kamshi, Zuma kuma tana da za’ki launin ciyawa kuma kore ne, amma ke babu wata kalma da zata iya bayyanar da zahirin siffarki sai dai kawai na ce ke kyakkyawa ce. Ina sonki Babyna"

Masoyi in ina ganinka sai na runka jin wani farin ciki mara misaltuwa yana zaga ko’ina cikin zuciya ta, Ji nake tamkar babu mai jin wani farin ciki a duniya sama da ni. Saboda kasancewna da kai, A kullum nakan tsara fasalinka da kallonka da murmushinka amma fa duk da idanuwana yayin dana bude sai na ga kana mun gizau tamkar kana tsaye a gabana.

Ashe ba ni daya ba, In ina tare dake mantawa nake da kaina ma balle na kusa dani, tsabar farin ciki mantawa nake da wani abu bakin cik.

Ai ni tuni mun yi hannun riga da wani bakin ciki sabida kasancewarka tare da ni Ina alfahari da zamowa ta taka wadda ta take sauran ‘yan matan da suke rubibin zamowa naka, na zama ni day kwal gare ka.

Sufar ki zanariya ce a idanuwana irin zanen dutsin nan da ba batun gogewa, Nakan zama kamar zautace a duk sanda na ke ba dan mutane sai su zata ni kadai nake magana. Alhalin kuma a duk sanda na shiga irin wannan yanayi ke nake gani zaune gabana muna hira kina sakar mun tausasan murmushi masu mantar dani inda nake,

Ina so ka sani komai nawa naka ne, kallo na nakane, murmushina naka ne, duk wani motsina naka ne dan babu wanda ya dace na mallakawa su face kai daya. Ka kan dada sani nishadi a duk sanda naji kalamanka dan babu irinsu, godiya nake ga Allah daya mallakamana zukatan junan mu ina alfahari da kasancewar mu tare da juna.

Na tabbata ni nayi tsuntuwar soyayya, wacce nasan cewa ba azanci da dabara na ne suka ban ba. Ke kyauta ce daga Allah, Ki gode wa Allah don ya ba ki bàbbàr baiwa ta sarrafa zuciyoyin ba iya na maza ba har matan ba.

0 Response to "www kalaman soyayya com"

Post a Comment