Illolin Rashin Baiwa Iyali Lokacinsu
Illolin Rashin Baiwa Iyali Lokacinsu
Kamar yadda mukasani shi aure ibada ne, hanyace ta neman rahamar Allah, natsuwa da kuma kamala. Bayam haka akwai wani bangare na rayuwar aure wanda zai samar da nishadi da kuma shakuwa da soyayya a wurin ma’aurata. Wannan bangaren ya kunshi abubuwa kamar haka;
Fira
Wassanni
Yin ‘yan aikace aikace tare
Fita ziyara tare
Cin abinci tare
Da dai sauransu.
Duk wayannan abubuwan basa yuwuwa idan namiji ya kasance baya ba mace lokacinta. Duk yanayin aikinka ya kasance akwai a kalla awa guda da zaka ware domin kasancewa da iyalinka, sannan dare yakasance natane domin har sallar nafila idan zaka shige hakkin matarka bai halatta kayiba. Domin kuwa rashin samun kula daga wurin miji kan iya jefa mace cikim hadarin aikata aiyuka marar kyau kamar haka;
Zina
Kallon batsa
Madigo
Yawace yawacen banza
Bin bokaye
Sannan yakan yawo kiyayya, domin sai taji ka fice mata aria.
Duk da anacewa idan ba’a fita bid aba kuma rikici ne, amma duk yanayin aikinka kayi kokarin ba iyalinka lokaci. Idan ma’aikacin gwamnati ne akwai dare akwai weekend, idan dankasuwa ne sai ka tsar aka cire koda rana dayane dazaka zauna da iyalinka domin hakki ne akanka ka sauke. Tun farko ma idan kai ba mazauni bane sai ka sanar da ita shin zata iya aurenka domin ga yanayin aikinka idan ta ji ta amince shikenan. Ammafa kusani rashin ba mace lokaci a gida yana daya daga cikin abubuwanda suke wargaza aure.
0 Response to "Illolin Rashin Baiwa Iyali Lokacinsu"
Post a Comment