Cikakken Tarihin BBCHAUSA
Cikakken Tarihin BBCHAUSA
BBC Hausa kafar yaɗa labarai a harshen Hausa ce, mallakin tashar labarai ta BBC da turanci wato British Broadcasting Corporation (BBC) World Service wadda take watsa shirye-shiryen ta a harshen Hausa musamman ma labarun da suka shafi ƙasashen Nigeria, Ghana, Niger da kuma sauran masu jin harshen Hausa dake a yankunan Yammacin Afrika. Bangarene na harsunan da BBC ke watsa shiryeshiryen ta guda 33 wadanda guda 5 daga cikin su yarukan Afrika ne. Ana watsa shirye shiryen sashen na Hausa kai tsaye daga babbar tashar ta BBC dake birni Landan wato Broadcasting House da kuma tashar ta dake babban birnin taraiyar Najeriya Abuja dakuma shafinta na yanar gizo wanda ake wallafawa duka dai a birnin na Abuja(https://ha.m.wikipedia.org/wiki/BBC_Hausa#Watsa_shirye_shirye).
Tashar BBC Hausa itace sashen farko da BBC ta fara gabatar da shirye shiryen ta daga cikin harsunan dake Afrika kuma daya daga cikin biyar na harsunan Afrika da BBC ke watsa shirye shiryen ta. An kaddamar da tashar ne a ranar 13 ga watan Maris din shekara ta alif 1957 da karfe 9:30 agogon GMT da shirin minti 15 wanda Aminu Abdullahi Malumfashi ya gabatar. Daga baya kuma Abubakar Tunau yacigaba da kawo labaran fassara a shirin BBC na Labarun yammacin Afrika wato West Africa in the News. Ana gabatar da shirye shiryen sashin Hausa na BBC na farko farko a ranakun Laraba da Juma'a ne kawai, bayan shekara daya kuma akaci gaba da gabatar da labarun kullum kullum.ranar 1 ga watan Yuni shekara ta alif 1958.
A watan Mayu na 2017 ne BBC Hausa tayi bikin cika shekara 60 da fara watsa shirye shirye. Bikin ya samu halartar daraktar BBC wato BBC World Service Group, Fran Unsworth(https://ha.m.wikipedia.org/wiki/BBC_Hausa#Watsa_shirye_shirye)
Watsa shirye shirye
A yawancin lokuta BBC nada babban edita da masu gabatar da shirye shirye da mataimakan editoci da babban mai gabatar da rahoto. Sannan kuma tafi karfin gabatar da labarunta game da al'amuran da suka shafi biranen Kaduna, Kano, Jos, Enugu, Abuja da Sokoto da kuma kasahen Niger republic, Ghana da kasar Sin.
Shugaban Sashen Hausa: Aliyu Abdullahi Tanko
Manyan masu tsara shiri:
Ahmed Abba Abdullahi
Aminu Abdulkadir
Masu tsara shirye-shirye:
Aichatou Moussa
Ibrahim Mijinyawa
Ma'aikaci mai zaman kansu:
Elhadji Diori Coulibaly
Ma'aikatammu a Nigeria
Ma'aikata a Abuja
Abdou Halilou
AbdusSalam Ibrahim Ahmed
Abdulbaki Jari
Aisha Sharif Baffa
Auwal Ahmad Janyau
Badariyya Tijjani Kalarawi
Bilkisu Babangida
Buhari Muhammad Fagge
Fatima Othman
Fauziyya Kabir Tukur
Habiba Adamu
Halima Umar Saleh
Haruna Shehu Tangaza
Haruna Ibrahim Kakangi
Ibrahim Isa
Imam Saleh
Ishaq Khalid
Jabir Mustapha Sambo
Madina Dahiru Maishanu
Mukhtar Adamu Bawa
Muhammad Abdu
Muhammad Annur Muhammad
Mustapha Musa Kaita
Nabeela Mukhtar Uba
Nasidi Adamu Yahya
Raliya Zubairu
Sani Aliyu
Umayma Sani Abdulmumin
Umar Rayyan
Umar Mikailu
Usman Muhammed Minjinbir
Yusuf Ibrahim Yakasai
Yusuf Tijjani
Zahraddeen Lawan
Masu hada sauti:
Lawal Nuhu Sulaiman
Ahmed Wakili Zariya
AbdusSalam Usman Abdulkadir
Masu aiko da rahotanni daga Najeriya:
Kano/Jigawa: Khalifa Shehu Dokaji
Lagos: Umar Shehu Elleman
Mai aiko da rahotanni daga Nijar:
Tchima Illa
Mai aiko da rahotanni daga Kamaru:
Muhamman Babalala
Tashoshin FM da suke gabatar da shirye shiryen BBC Hausa a Najeriya
Ana sake watsa wasu shirye shiryen na BBC Hausa a kafafen Radiyo da Talabijin dake Najeriya da hadin gwiwar kafar BBC wato BBC World Service. Ga wasu daga cikin su[4]
Yola, Adamawa State –Radio Gotel - 917kHz AM
Maiduguri, Borno State –BRTV - 94.5FM
Kano, Kano State –Freedom Radio - 99.5FM
Dutse, Jigawa State –Freedom Radio - 99.5FM
Kaduna, Kaduna State –Freedom Radio - 99.5FM
Jos, Plateau State –PRTV - 88.65 FM, 92.1 FM, 90.5 FM, and 1313 kHz AM
Sokoto, Sokoto State –Rima Radio - 97.1FM, 540kHz AM
Reference
Domin Zurfafa bince kan Tarihin BBCHAUSA ku ziyarci shafuka kamar haka
"Game da mu". bbc.com/hausa. BBC. Retrieved 23 September 2019.
"BBC Hausa marks 60th anniversary with lectures". dailytrust.com.ng. Daily Trust. Retrieved 23 September 2019.
"Ma'aikatan Sashen Hausa". bbc.com/hausa/staff. BBC Hausa. Retrieved 23 September 2019.
"Abokan huldar BBC Hausa". bbc.com/hausa. BBC. Retrieved 23 September 2019.
"Radio's Popularity Declining Unevenly". nytimes.com. The New York Times. Retrieved 23 September 2019.
"BBC's Hausa service has started to host advertising". thenigerianvoice.com. The Nigerian Voice. Retrieved 23 September 2019
0 Response to "Cikakken Tarihin BBCHAUSA"
Post a Comment