Ba Kayanmata Kawai Kike Bukata Don Gamsarda Maigidaba/Mijinkiba
Ba Kayanmata Kawai Kike Bukata Don Gamsarda Maigidaba/Mijinkiba
Kayan mata wasu nau’uka ne na hadadden ganyayyaki, itatuwa, sakasakai, da dai sauransu da akan harhada asha domin samun gamsuwa a wurin jimai’i. dayawan mutanen mu suna alakanta samun gamsuwar jimai’i da shayeshayen wayannan kayayyaki. A gaskia kayan mata basune zasu samar miki daraja ta auratayya awurin mijinkiba.
Akwai sirrika guda biyar (5) da zasu taimaka maki wurin gamsar da mijinki kamar haka;
Ki kasance kinaso da shaukin mijinki, ya zamana akwai shakuwa atsakaninku.
Ki kasance kina cin abinci mai kyau gwargwadon hali, musamman irinsu ‘ya’yan itace, zuma, da sauransu domin su zasu taimaka wurin dwwamar da ni’ima atare da ke.
Ki kiyaye tsaftar jikinki, ko’ina wanda ya hada da suma, baki, da gabanki da kowane lungu da sako na jikinki. ki kuma kasance koyaushe a cikin kamshi.
Ki kasance mai amfani da ingattattun turaren hayaki na jiki sannan kina tsarki da ruwan bagaruwa ko magarya masu dumi, basai kinyita cusa wa jikinki abubuwand bakisan asalinsu ba.
Ki kasance mai mayarda martini aduk sanda kuke auratayya, ba ki zama tamkar gunkiba. Ba sai yace yimin kaza ba ke da kanki kina mai bullo da salo sababbi lokaci zuwa lokaci. kuma kar kiyi gum, ki yawaita ‘yan maganganu kina karamasa kwarin gwuiwa.
Wadannan abubuwa biyar idan zaki kiyaye zai taimaka maki sosai, ki kiyayi shayeshayen kayanmata da bakisan abubuwanda akayi amfani dasu wurin hada suba domin kuwa cutuka sun yawaita.
0 Response to "Ba Kayanmata Kawai Kike Bukata Don Gamsarda Maigidaba/Mijinkiba"
Post a Comment