Abubuwanda Yadace Kiyi Kafin Aure
Abubuwanda Yadace Kiyi Kafin Aure
Da farko dai shi aure abu ne wanda keda matukar muhimmanci a rayuwa ta dan adam kuma sunnah ce ta fiyayyen halitta (S A W) wanda ya kasance idan mutum yanada aure ana matukar daraja shi a cikin mutane wanda kuma bayada auren zakaga kimarshi ta ragu a idanun jama'a. Akwai abubuwa da dama dayakamata mace tayi kafin tayi aure. Farko dai yakamata ace kinyi ma kanki tanadi namusamman kafin Kiyi aure anaso kiyi gyare gyare na jikinki domin ki shiga dakinki kina sheki a misali Kamar zaayi miki dilka ma'ana wato gyaran fatar jikinki sannan zakiyi gyaran kai ado Kiyi lalle Kiyi kwalliya sannan Zaki yi kayan mu irin na mata ma'ana wato hakin maye Kamar su gumba tsimi da dai sauransu domin ki kara samun ni'ima a jikinki. Na biyu shine kayakamata ki kare mutuncin kanki kafin Kiyi aure da kuma ma bayan auren domin shine abu mafi mutunci a tare dake idan baki shiga da mutunci a dakin aurenki ba bakida sauran daraja a idanun Mijinki dole sai kin kula sosai da wannan sannan yakamata ki koyi yadda ake zaman hakuri kafin ki shiga naki gidan kisan yadda ake Zama da mutane domin shi aure koina yakan jefa mutum sannan bakisan a kowane wuri zai kaiki ba it maybe gidan taro ne ko kuma bariki ne da dai sauransu so dole ki iya Zama da mutane domin kiji saukin rayuwar aurenki sannan ki koyi girki domin maigidanki ki koyi tsafta ki koyi kissa da kisisina irin namu na mata Kiyi kokarin sanin halayen wanda Zaki aure domin kisan abunda yake so da wadda bayaso. Kiyi kokarin sanin hakkin aure. Allah yasa mu dace Amin.
0 Response to "Abubuwanda Yadace Kiyi Kafin Aure"
Post a Comment