-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Abubuwan da zakiyi lokacin da kike dauke da juna biyu

Abubuwan da zakiyi lokacin da kike dauke da juna biyu

Abubuwan da zakiyi lokacin da kike dauke da juna biyu

A duk lokacin da Mace tasamu juna biyu wato ciki anaso ta gare yawan aikace aikace bawai ance ta daina aiki gabadaya b ne aa Yar shara haka a cikin gida duk Zaki iyayi ko dan wanke wanke haka a cikin kitchen, mai ciki baa cika son tana daukar abu mai nauyi b ko kuma ta dinga yawo da jikinta anyhow saboda any slide mistake cikin kan iya faduwa more especially idan cikin sabo ne ma'ana bai haura wata hudu b shiyasa akeso mutum yayi  hattara babu dogon aiki sosai sannan bazaki kuma baki motsa jikinki b Zaki daiyi tsaka tsaka  anaso mace mai juna biyu ta dinga cin abubuwa wadanda zasu kara mata jini a jiki saboda ta samu lafiya kuma abinda ke cikin cikinta yasamu lafiya ingantacciya shima baa so jini yayi karanci a tare da mai juna biyu domin hakan kan iya haifar da wata matsala a tare da ita ko kuma abunda ke cikin cikinta ..idan kin samu juna biyu ana so ki dinga cin kayan lambu a misali Kamar su lemu, kankana , ayaba da dai sauransu sannan anaso mace mai ciki ta rage Shan kayan Zaki duk da dai masu ciki Allah kan jarrabe su da son kwalama ya danganta wani zakaga da zarar ya dauke ciki shikenan abinci yafita ransa saidai yan kayan makulashe da baa rasa wani kuma ya daina son kamshin turare kenan wani kuma abu mai barkono a ciki kawai yakeso ya danganta da irin Yanda Allah ya jarabci kowa anaso idan mace nadauke da ciki ta rage Shan Milo wanka ake tea dashi saboda hasashe Yana nuni dacewa Yana sa jariri girma a cikin ciki wanda hakan zai iya sa mace Tasha wahala wurin haihuwa saboda yaron ya girma sosai a cikin mahaifa.

Idan mace ta samu juna biyu zata tarairaye shine har tsawon wata Tara zata bashi Kulawa har lokacin da Allah ya sauketa lafiya. Sannan mace mai ciki bazata kama Shan magani anyhow b ko mutum yaji kanshi na ciwo ya dauki magani yasha ko makamancin hakan kafin ki dauki kowane irin magani kisha kiyi consulting doctor ya gayamiki irin maganin da yadace kisha wanda bazai taba lafiyar jaririn dake cikin cikinki b akwai magani da ake bawa masu juna biyu idan aka fara zuwa awo wannan maganin zai kara miki lafiya ke da jaririnki ne kuma ya kara miki jini kuma Zaki cigaba da shansa har sai lokacinda kika haihu akwai folic acid akwai fessolate  sannan akwai wani wanda yayi combining duka guda biyu ana kiranshi women's prenatal zakisha daya a kowace rana har lokacin da kika haihu.

Sannnan zuwa awo ga mai juna biyu is very important akwai easy matan dazasuce ai basai sunje awo b suyi zamansu a gida idan mutum baya zuwa awo kuwa bazai san lafiyar jaririnsa b Amma da zarar kina zuwa awo duk wata zaa duba lafiyarki da ta jariri idan da wata matsala Zaki Sani sai a dauki mataki tunda wuri  Amma idan bakya zuwa it maybe ma ko kwancin baby ki a cikin ciki b daidai bane kuma bakisani b kunyi zamanki a gida sai anzo haihuwa wata matsala kuma ta biyo baya a rasa menene bayan kuma bakya zuwa ana duba lafyar cikin

Mace mai ciki anaso ta dinga sa kaya masu walwala hardai ake cikin ya tsufa Kamar 6month upward domin idan kaya sun matse ta zata tauye kanta dakuma abinda ke cikinta kuma anaso mai ciki ta dinga cin nama haka ko kifi idan maigidanta yanada halin saya domin kara lafiya da karfin jiki 

A lokacin da ciki ya kusa isa haihuwa ana bukatar mai juna biyu ta dinga yin excercise ma'ana tana motsa jinkita bawai ta zauna wuri guda b amfanin excercise din shine zaisa abunda ke cikinta ya dinga motsawa Yana kokarin saukowa gravity nashi Yana sauka so that koda haihuwan zatazo yaron zaiyi helping naka wurin fitowarsa.

Allah yasa mudace

0 Response to "Abubuwan da zakiyi lokacin da kike dauke da juna biyu"

Post a Comment