-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Ake Zama da Kishiya 2023

Yadda Ake Zama da Kishiya 2023

Yadda Ake Zama da Kishiya 2023

A cikin wakar Sa’adou Bori, ta ‘Hadiza yar malamai’ ya yi bayani a dunkule na kan irin tashin hankalin da mata ke shiga idan aka yi batun kishiya, inda yake cewa: “Zama Da Kishiya Tilas ne ba don uwargida na so ba.”

Ba a fiya samun gidan da kishiyoyi ke zama lafiya da juna ba. Tun muna yara muke jin labaran fadan kishiyoyi da tashin hankalin da suke yi.

Mun girma a inda ake ganin kishiya wata babbar bala’i ce da take iya hada maka tuggun da zai yi wuya ka fidda kanka.

Tsanar da muka yi wa kishiya ke sa muke tsanar matan uba ma sosai.

Mafi yawanmu mun tsani zancen kishiya balle har mu kira ta a matsayin abokiyar zama.

Sai dai, daga cikinmu mata akwai wadanda suka rungumi kishiya a matsayin ”yar uwa kuma abokiyar zama. Na san wani gida a Kaduna, inda matan gidan suka shaku da juna ta yadda da wuya ka gane bambancin ‘ya’yansu.

Yaya aka yi wasu matan suka samu fahimtar juna tsakanin su da kishiyoyinsu? Mene ne sirrin zaman lafiya da samun fahimtar juna tsakanin kishiyoyi? Shin zai yiwu mace ta so kishiyarta har ga Allah?

A shirin namu na wannan mako, mun tabo wadannan tambayoyi da ma wasu da dama. Wadansu matan da na tattauna da su sun ce min zai yi wahala a samu zaman lafiya da kishiya idan har mijin ba ya adalci a tsakanin su.

Ga alama dai rashin adalci wajen fifita wata matar a kan wata shi ne jigon da ke sa mata matsanancin kishi a tsakanin su. Wannan ba sabon abu ba ne, saboda ko a wakar Sa’adu Bori, ai mun ji inda ya koda amaryarsa Hadiza ba tare da ambato uwargidansa ba. Kun gani ba?

Ga mata da yawa dai, wannan fifiko ke haukata su da rura wutar kishi a tsakanin su.

Ga sauran kuwa, zaman lafiya da kishiya ya danganta ne da irin halayyar kishiyar. Idan mai kirki ce da iya zama da mutane kuma wacce ta samu tarbiyya mai kyau, sun ce to zama da irin su yana da sauki da kuma kyau. Amma idan mara tarbiyya ce kuma mai munanan dabi’u to fa da wuya a samu zaman lafiya da fahimtar juna.

Me ya sa mata ke tsoron mazajensu su kara aure? Wannan tsoron ba abin wasa ba ne. Mata na yin duk bakin iyawarsu wani lokaci ma su kan wuce gona da iri a yayin da mazansu za su sake aure.

Wannan muguwar dabi’a ta sa mata na yin tsatsube-tsatsube don kawai ka da su zauna da kishiya.

Kun yarda cewa ba za a taba samun zaman lafiya da kishiya ba? Wacce hanya ce mafi kyau da mace za ta bi wajen zama da kishiyar

SIRRIN ZAMA DA KISHIYA(ABOKIYAR ZAMA)

Iya zama da yar gari(KISHIYA).

  • 1.karki shiga hakkinta ko ya za’ayi, kiji tsoron Allah.
  • 2.ki sama ranki bata isa tayi maki komai ba face abunda Allah ya kaddara(ki rike Imani).
  • 3.ki kasance mai bin dokan miji akoda yaushe.
  • 4.Tsaftan jiki, gida, yara ki zamo gwana.
  • 5.Karki yarda tasan abun da ke bata miki rai(KO RAI YA BACI,SHIGE DAKI KIYI KUKA,KI YI WANKA KI DAU KWALLIYA)
  • 6.Karki taba kai kararta gurin miji.
  • 7.kizama kullun acikin fara’a(BA’A DAKEMA KISHIYA).
  • 8.Kizama Kamar doki a gado (Itakuma nunamata miji bai damekiba)
  • 9.Ki mata marhaba a farkon haduwanku(KO AN SAMU MATSALA, ZA’ACA BAKI KITABA TUN FARKO)
  • 10."yayanki natane, karsu zamo kishiyoyinki.
  • 11.Intamiki magana, karkiyi gaggawan ansata, bada kamar sec 30,kinga kin yi tunana kuma zaisa tana shakkanki(AJI)
  • 12.IYA GIRKI BABBAN MAKAMI NE.
  • 13.Ki zamo mai tattali bamai rowaba(DABARA)
  • Ki cireta a ranki
  • Kizama yar kwalisa a kullun(Under 12).Kar a gana ranar girkinki da akasinsa.
  • 15.Ki rage yawan hira(KE BA RADIO BACE).    Ranan kwananki ke actor ce, ran nata boss(Rakashi da kiss ma zafi inzai tafi can). Karki nuna kishinki a fili.
  • 16Inya kiraki da sunanta, amsa,zai rasa abunda ya furta(IN YAKIRATA DA NAKI MASIFA)ita   gasarkin yaki.
  • 17.karkina magananta da wasu(BATA DAMEKI BA)
  • 18.SHAGWABA amma a DAKA.
  • 19.komin zafin abu,baki ba dambe ko cacarbaki da ita(KE TSARARTACE?)
  • 20.YAR UWA MIJI SAI SIYASA.


0 Response to "Yadda Ake Zama da Kishiya 2023"

Post a Comment