Ya ake gyaran nono
Ya ake gyaran nono
Barkarmu da sake saduwa acikin wannan shafi mai albarka mai suna Haskenews yau mun samu sakonku na ya ake Gyaran nono ga budurwa ko musamman bazawara ko matar aure.
Dafarko dai ya kamata mu sani mu mata gyaran jiki wajibi ne ga kowace ya mace kuma darajace a wajan mijinta maza da yawa ALLAH ya kaddarta masu shawar son nono, don haka ya zama dole garemu ku kiyaye wannan.
Kamar dai yadda malamai suke ta fada cewa akwai hanyoyin gyaran nono da Budurwa, Bazawara ko Matar Aure zatabi domin dawowa da ni'imarta. Acikin wannan kasidar zamu kawo maku hanyoyi uku da zakibi domin dawowa da ni'imarki.
Nono babbar kadara ne kuma kyawunsu yana kara miki kyau da kima gurin miji idan sun lalace kuma ke da kanki baki son ganinsu balle mijinki saboda haka dole ki dinga kula dasu. Alwai hanyoyi da dama na kula da lafiyar nono, ga wasu daga cikinsu: Karin girma da rashin faduwa:
HANYA TA FARKO
- kankana
- gwanda
- abarba
ayanka kanana a zuba aruwan zafi idan yayi laushi sai a shanye.
idan shayarwa akeyi man hulba cokali2 abi da zuma cokali1.
Idan ya zube ne a dafa hulba da yansun idan ya dafu atace,asha,sannan a kwaba hulbar da kwan salwa arika.Kafin shafawa.
HANYA TA BIYU
shima wanna wani hadine da akeyi don gyaran nono kuma yanada muhimmanci sosai , yanda akeyi shine za'a Samu
- kindirmo
- tumatur
- lemun tsami
- garin kubewa
- da garin sallaja
Sai ki hadasu guri daya ki kwabasu ki rinka shafe nonon dashi, bayan kimanin 1hr ko minti 30 sai ki wanke ki shafe nonon da man ridi.
HANYA TA UKU
- Farar shinkafa
- Garin Alkama
- Garin habbatus sauda
- Garin Ayaba (Plantain).
- Gyada mai malfa (mai zabo)
- Aya Madarar gari.
- Zuma
Zaa bare bayan plantain sai a yanka shi, a shanya ya bushe, sai a daka, a hada da garin alkama da garin farar shinkafa, sai a hada aya da gyadar a markada a tace ruwan. Bayan nan, sai a dora kan wuta a zuba garin Plantain da alkama da farar shinkafar da muka hade a guri daya, sai kuma ku zuba garin madara da zuma, ku dama ya yi kauri sai a rika sha safe da yamma. Idan kina shirin yin yaye ne, to ki sha sati biyu kafin yaye, kuma ba kya shayarwa, za ki iya sha, sai ki tanadi rigar mama, wato Brazier mai kyau, wanda zai rika tallafawa mamanki su tsaya sosai, ki rika sakawa.
Ki yi haka na tsawon sati biyu, da yardar ALLAH ni'imarki zata dawo fiye da yadda kikeda a baya
Idan kuma baki da halin siyan duka wadannan kayayyakin da aka ambata to kina iya yin kunun alkama ki rika sha sau biyu a rana, amma za ki rinka sa madarar gari, wato kunun alkama da madara ke nan.
HANYA TA HUDU
IDAN nononki kanana ne kina so suyi man ya kamar yadda kikeso dai-dai kina iya yin wannan hadi domin samun lafiya nononki
- cukwul
- garin alkama
- aya
- nonon saniya
- madara
- garin hulba.
Cukwul wanda yawansa zai Kai guda uku sai ki samu garin alkama gwangwanin daya sai aya itama gwangwanin daya sai ki daka su zasu zama gari ki tankade ki samu nonon saniya idan kuma bakyashan nonon saniya ki samu madara ki zuba wannan garin kamar cokali 3 ki dama kina shan kullum Sau 1 sannan ki Lura lokacin da zakiyi wanka ki tafasa ruwa da garin hulba a ciki ki Bari yayi sanyi sai ki wanke nonon da shi sannan Kiyi wankan.
HANYA TA BIYAR
wanna wani hadine da akeyi don gyaran nono musamman ga budurwa, shi wanna hadi kuma kowace mace inda tana da bukata zata Iya amfani dashi saboda tasirinsa, yanda akeyi shine.
- garin waken soya.
- garin alkama.
- garin zogale.
- garin bawon lemun Zaki.
Kuci gaba da kasancewa da wannan shafin mungode da ziyartarku.
Allah yada mudace baki daya
0 Response to "Ya ake gyaran nono"
Post a Comment