-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya Na WhatsApp, Facebook, Tiktok da Twitter

Kalaman Soyayya Na WhatsApp, Facebook, Tiktok da Twitter

Kalaman Soyayya Na WhatsApp, Facebook, Tiktok da Twitter

Sakonnin Soyayya Masu Daɗi Da Sanyaya Zuciya

Na ilmantu da kyawawan dabi'u irin naki shiyasa na himmantu wajan gyara zama acikin kaunarki.  Gabi gabanki yar gata karkive dani kin fasa domin idan jikina ya dauka to tabbas zuciyata bazata jure bah Nida naki ne harkullum kauna agareki  babu ranar fashi koda hakan zai zamo karshen numfashi na. Taya zan rayu batare dake bah akwai amana tsakanin ruhi da soyayyarki shiyasa komai na rayuwata na sallama miki

Ban tsinci kaina cikin wata sabuwar dauniya bah saida nafara tozali da kyakkyawar fuskarki ma abociyar annuri da murmushi mai laushi. Hakika kinada tsanani kwarjini a idanuna shiyasa ban iya zama da tunanin kowace mace a raina inba keba "Xuciyar Da Kika Dauke Mata Duk wani Sansanin Soyayya a Cikinta Itace Take Neman Agaji Da Tallafin Rikon Gaskiya Da Amana a Gareki.

"IYakar Mallakin Matsayi kin Cancanta Da Mallakarsa a Gareni Domin Kin Xame Min Tamkar Mashahurin Hasken Dake Kore Min Duhun Cikin lungu Da SaQon Xuciyata. "Babu Dana Sani Ko Nadama a Duk Lokacinda Na Rusuna a Gareki Sakamakon Kece Sarauniya Mai Martaba  Wadda Ke Taka Rawar Gani A Cikin Babban Birnin Xuciyata.

"Kasancewarki Tare Dani Tamkar Ina Cikin Inuwar Dake Bakin Qorama Ne Da Itace Da Korayen Ciyayi, Rashinki Kuma a Gareni Tamkar Ina Cikin Inuwar Gawo Ne a Lokacin Rani Da Iskar Bazara. "Lallai Xuciya Ta Mace Akan So Da Qaunar Da Babu Hadi a Cikinta Kuma Kece Sanadi Yayinda Kika Janye Ra'ayina Ta Hanyar Hasken Kwalliyarki Da Murmushin Soyayya. "Wajibine Xuciyata Tayi Alfahari Da Kanta Matsayin Mai Cikakken  "Yancin Da Bashi Da Iyaka,

Tunda Ta Samu Mafakar Da Xata  Yi Walwala a Cikin Taki Xuciyar. Dare Da Rana Farin Ciki Yana Qara Wanzuwa a Tare Dani Sakamakon Samun Damar Mallakar Sarauniya Irinki Ba Qaramar Gagarumar Nasarace Bace Ga Kowanne Masoyin Duniyah. "Tunda Har Kika Xamanto Sinadarin Farin Cikina To Ki Rikeni Na Xama Naki Mallakinki Domin Babu Mai Sauya Min Ra'ayina Akan So Da Qaunar Da Xuciyata Take Miki.

Kallonki Shine Muradin Idaniyar Da ta Samu Haske a Lokacinda Xuciya tayi Arba Da Soyayyarki Kece Jinin Jikina Domin Soyayyarki. Tana Xagayawa a Cikin Jini Da 6argon Jiki Shiyasa Farin Ciki Da Kuzari Suke. Qara Wanzuwa a Tare Dani Ina Alfahari Dake   Sarauniyar Dake Dauke Damuwa Da Tunanin Xuciyata. Sakamakon Na Kasance Gasgatacce Kuma Amintacce ga Kyakkyawar Zuciyarki.

Farashin So Da Qaunarki Ne Yake Qara Hauhawa a Kasuwar Xuciyata Dan ina da Tabbacin SOyayyarki. Annashuwace Da Kwanciyar Hankali a gareni Xuciyarki Farace Da Alkunya Akan Fuskarki Sakamakon Duniyar Nan  Kece Tauraruwar Da Nake Kallo a Matsayin kyakkyawa Nasani Cewa Ma'abocin Haske a Xuciyata Shine Sonki, Domin Shine Madubi Kuma Sinadarin Jindadina.


Sakonnin Soyayya Masu Janyo Ra'ayin Budurwa


Idan Na Tuna Dake a gareni Kin Xarce Lailah Da Ashwarya a Fagen Iya Tsara Kwalliya Da Kyawun Fasali Sakamakon Kin Xamo Tamkar Gajimare Saboda Tsawon Gashinki Har Izuwa Gadon

Baya. Amincin allah yatabbta agareki hadaddiya hamshakiyar sanssanyar iska wacce take busawa a sararin samaniya maidauke da kamshin furanni tareda fatan kina lpy Inaso namiki gaisuwa tsaftacciya kuma tabbatacciya zuwaga mace  ingantacce kamarki. Dunbin soyayya da aminci da yarda da murna da farin ciki marasa karewa agareki mace daya tamkar dubu,hakika kece wanda nabawa mulkin zuciyata kece wanda 6acin ranki ke girgizani kuma kece wanda hawayanki kan zamto tamkar ruwan zafi agareni.

musamman lokacinda naji wani wadda kikeso yayi fatali dake nasan kinsha kuka,hakan yasa zuciyata tamkar garwashi acikinta. Sannan ina mika shimfidaddadiyar murnata mai dauke da dauwamammiyar kauna tareda goyon baya cikin soyayyarmu.

Ya wanda sautin muryarta take rikitar dani takuma gigitani saboda tsananin ƙaunarki danake mai sona. Ina so infadamiki irin ribar danaci sakamakon haduwa ta

dake Bari nadakata anan domin naga kamar ranki bayaso Dan kinsan naki jinin 6acin Ranki. zan rikeki amana bazan yada keba har abada inshaallah.  Naturo maki sakon gaisuwane kafin muyi waya,kuma ina mai jaddadamaki cewa ina alfahari dake abin kaunata.

QALBI NA Samun ki a rayuwata ya bani k’warin guiwar tunkarar matsalata da samun nasara a kan dukkan abun da na sa a gaba. Kulawarki a kaina na k’ara min jarumta, soyayyarki a gare ni na sanyawa na ji ni a matsayin cikakken mutum. Nagode mosoyiyata, ina alfahari da samun ki a rayuwata.

A gare ki nake samun bargo, a dukkan lokacin da sanyi ya  rufe ni. Ina samun tsaro, a dukkan lokacin da hatsari ya tinkaro ni Ina samun farin ciki, a dukkan lokacin da damuwa ta lilliɓe ni fatana da burina mu mutu tare mu tashi tare mu rayu tare a gidan Aljanna ina Son Ki Mai sona Fiye Da Yadda Nake Son Kaina.

Sakonnin Soyayya Masu Saka Kauna Tsakanin Masoya


Ina son ki kuma zan cigaba da son ki na tsawon rayuwata mai sona. Ni da ke tamkar k’ashi ne mai k’warin da bana fatan ganin ranar da zai yi targaɗe balle har ya kai ga ya karye. Ina Son Ki. Daga cikin biliyoyi da Miliyoyin yammata na zaɓo ɗaya tamkar da dubu. Tabbas na yi nasara na samun ki a matsayin mosoyiyata abun alfaharina. A tsawon lokacin da zan rayu ina numfashi, ina son ki so mara iyaka.

saƙon murmushi zuwa ga wacce zuciyata keda burin mallaka akoda yaushe, saƙon farin ciki nake isarwa zuwa ga wacce dake da isa mafi isa daga cikin masu isa afadar zuciyata, me kyau nakasa misalta irin yanda nakejin sonki acikin jijiyar dake aika jini dukkan sassan jikinah,  a kowane lokaci da kowani yanayi kece abar tinanin kwakwalwata, me kyau soyayarki daɗa ƙaruwa take akowanni sa'a na agogo, kin kasance wani bangare daga cikin jikina wanda yafi komai muhimmanci shiyasa baki da tamka ackinta, na mallaka miki zuciyata da dukkan soyayyata domin kece wacce kikapi chanchanta dana mallakawa, ina mutukar alfahari dake, kuma ina fatan zaki kuladani kuma kikulaman da kanki sarauniyata,  

Dear Hubbina kisanar da zuciyar ki cewa ina gaisheta, sannan ki sanar da ita cewa a ko yaushe bani da burin da yawuce na ƙosar da ita da kalamai waɗanda zasu ratsa duk jiki da jinin jikin ki. domin ki samu tabbaci kuma kiji a jikin ki cewa kina dani a duniyar masoya abar kaunata, zuciyata takamu da kaunarki matuka masoyiyata. 

Ana gane kyawun shuka ne idan har an gama ta da taki Tayaya za a gane sama idan har babu ‘kasa? Kamar haka ne, farin-cikina zai yi wuyar bayyanuwa matu’kar ba ma tare da juna. Na kan shiga damuwa a dukkan lokacin da na duba gefena ban gan ki ba. Yau rana ce ta farin-ciki gare ni da kuma ke da sauran danginmu.

abar qaunata, tauraruwar dake haskakamin zuciya ta,ina Alfahari dake dare ko rana Sonki ba zaitaba gushewa azuciyata ba.Ganinki cikin farin ciki shine burina,kasan cewar ki cikin annushuwa shine fatana. Dawwamar sonki azuciyata shine roqon danake har kullum agurin Allah (S.W.A).

Aduniyar masoya kinciri tuta domin kece kadai kike da hasken idaniya annurin fuska dakuma sautin murya mai dadin saurara. Zuciyata tana tare dake sarauniyar mata ma'abociyar soyayya Wacce Sonta ya zama tamkar jinin ji kina, tunanin ki yazama abokin rayuwata. Tabbas da da abin da yafi Kalmar so da qauna dasu zanfada agareki,soyayya rmu dake wata baiwace daga Allah kuma ni'imace agaremu.

Sakonnin Soyayya Da Budurwa Zata Turawa Masoyinta


Nakan tashi da buqatar ganinki kusa dani amma da munhadu kunya takan hanamu hada ido da junammu.sonki sinadarin rayuwata ne kuma jigo ne gareta. Bazan gusheba ina mai cewa ina matuqar sonki da qaunarki kamar yadda naga kina alfahari dani a matsayin masoyinki. Kaso mafi tsoka na farin ciki na kece abar qaunata.

Nikuma inanan ina miki tanadin farin ciki da annushuwa da walwala bayan auren mu dake. Hotonki Ne a Cikin Madubin Xuciya Shiyasa A Duk Lokacinda Na Kwanta Bacci Sai Nayi Mafarki Da Kyawun Surarki Lallai Matuqar Mafarkina Xai Xamo

Gaskiya To Ba Shakkah Sarki Mai Fadawa Da Rigar Alfarma Baxai Kai Ni Matsayi Ba Domin Xan Kasance Sadauki Jarumin Masoya Idan Na Mallaki Sarauniya irinki.

Ta Kowanne 6angare a Cikin Jikina Babu Wata Sai Ke, Sakamakon Gangar Jikina Tasan Da Xamanki A Matsayin Inuwar Farin Cikina. Mafarkina Wani Babban Sirrin Ne A Rayuwata Domin Idan Na Bayyana Shi Kowa Yasan Kece a Cikinsa, Ba

Lallai Bane Masoya Su Barni In Xauna Dake a Soyayya Sakamakon Kece Tauraruwa Kuma Malama a Cikin Fadar Masoya Mafarkina Shine So Da Qaunarki Dake Bayyana a Cikin Idanu, Idan Har Kika Gasgata, To Xanyi Alfahari Dake Matsayin Mai Tausayi Da Tallafi A Cikin Xamantakewata Dake.

Mafarki Da Kyawun Surarki Yana Kore Min Soyayyar Wata "Ya Mace A Fadin DUniyar Nan, Dan Ina da Tabbacin Duk Irin Kyawun Wata "Ya Mace Baxata Kai Kwatankwacin Irin Naki Ba A Duk Lokacinda Nayi Murmushi To Mafarki Nake,Sakamakon Babu Wani

Sindari Dake Tunxura Ni a Cikin Shauqi Sai Soyayyarki Xuciyata Begenki Ne Nishadinta Kuma Tana Qaunar Duk Wani Mai Yabonki Wani Lokaci Ma Ina Bada Kyautar Duk Abinda Na Mallaka Idan An Ambaci Sunanki Ki Rike Xuciyata Matsayin Amanar Da Baxa Ta Guje Miki Ba Domin Nayi Alkawarin Mafarkin Aurena Dake Sai Ya Xamo Gaske insha allahu.

Jinjina Ma'abociyar Sarauta Da Takun Qasaeta Su Kasance Linzamin Bayyana Cikakken Iko Da Matsayinki Na Sarauniyar Masoya Fadar Dake Cikin Masarautar Zuciyata Tana Qara Ninkaya Acikin Alaqaryar So Da Qauna Yayinda Kika Kusanceta Da Kalamanki Cikin Tattausar Murya Tilass In Buga Tambarin Soyayyata Mai Dauke Da Kirarin Yabo Da Jinjina A Gareki Ma'abociyar Hasken Kwalliya Da Kyakkyawar Xuciya Zan Sanarwa Duniya Cewa Ko Bayan Raenah Dukkanin Abubuwan Dana Mallaka Sun Xama Naki Ke Daya Tilo, Domin Kece Nakeji Acikin Jikina Kina Yawo Yayinda Farin Ciki Ya Wanzu Cikin Xuciyata.

Ko Kadan Bazan Miasaltaki Da Kowa Ba Sakamakon Kina Daya Daga Cikin Nasararorin Da Rayuwata Xata Yi Alfahari Yayinda Kika Zamo Tawa Ni Kadai. Tabbass Kin Shiga Jini Da Jijiyar Dake Cikin Gangar Jikina Shiyasa Koda Acikin Mafarki Ina Yawaita Ambaton Sunanki Da Tattausar Murya. A Duk Bayan Dakika Daya Hasken Kyakkyawar Fuskarki Ne Yake Qara Bayyana Acikin Mudubin Zuciyata Domin Ina Da Tabbacin Cewa A Duk Inda Kike Ba Shakka Kina Kusadani.

Kin Xarce Duk Wata Basarakiyar Dake Rayuwa a Doron Duniyar Nan Domin Samun Kwatankwacin Irinki Shine Mafi Wahalar Nema Ga Duk Wanda Ya Rasaki Zan Iya Yin Komai Akanki Kuma In Rasa Komai Akanki Saboda Inasonki.

Kece Mallakin.

0 Response to "Kalaman Soyayya Na WhatsApp, Facebook, Tiktok da Twitter"

Post a Comment