-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Kalaman Soyayya 2022

Kalaman Soyayya 2022

  Kalaman Soyayya 2022

  1. My Inason ganin fuskar ki ta cika da farin Ciki, inason naga
  2. annashuwa a tare dake, inason naga kina walwala na jin
  3. daɗi, banason naga bacin rai naki, bana son kiyi kuka, kukan
  4. ki tayar min da hankali yake, hawayen ki zazzabi suke
  5. sakani, nakan dimauce idan bakya farin ciki. Burina ni dake
  6. mu Kasance abokai na har abada, mu Kasance Aminai, mu
  7. Kasance ma'aurata, ni dake mu Kasance hanta da jini. Mu
  8. Kasance kamar ƙarfen jirgi dan ƙarfi, mu zamo kamar zinare
  9. ko ina aka kalle mu an ga mata da miji cikin Soyayya. Mu
  10. kasance masoyan juna na haƙiƙa.
  11. Kyautar Kalaman So Daga Bakinda Baya Gajiya Da Ambaton Furucin Harafin Dake Fitar Da Sakon Gaisuwar Girma Agareki
  12. Budemin Nashigo Kofar Zuciyarki Da Sannu Zan Zamo Dauwamammen Farin Cikin Da Zai Bunkasa Dukkan Wani Farin Cikin Rayuwarki
  13. Assalamu Alaiki Yake Hakikar Halittar Da Bayananina Suke Nufi. Nazo Da Murna Zuwa Murmushi Da Farin Cikin Shaukin Samun Damar Ganin Kyawun Nasabarki
  14. Kicemin Marhabun Yaka Taho Dan Gata Zuciyata Kazo Zan Baka Ruwan Hawayen Idanuwana Suna Kwaranyane Sanadin Nemanka
  15. Annashuwa Da Shauki Ne Zasu Biyo Baya Farin Ciki Marar Misalin Adadi Shine Zai Rufe Dukkan Wasu Kofofin Damuwata
  16. Zuciyata Tana Miki Sallama Ta Masoya Jinin Dake Kara Kuzari Ajikina Shima Yana Ladabin Gaisuwa Agareki
  17. Yar Asalin Kyau Mai Dirar Hanci Siriri Matsakaici Kinada Kyawun Halitta Da Tsarin Iya Kwalliya Akan Burgewa
  18. Sonki Ne Kadai Akan Tsarin Dukkan Tunanina Komai Nisan Dare Da Tsawon Wuni Iya Wuya Tunaninki Ne Akan Kwakwalwata
  19. Kallon Tsakiyar Idanuwanki Suna Saukar Da Sabuwar Ni,ima Acikin Jikina Ta Hanyar Hakane Nake Kara Kaimi Wajen Ganin Nasamu Ganinki Akowace Rana
  20. Dauki Ki Amsa Sunankine Nake Ambato Tsananin Sonkine Yake Tsuma Zuciyata Shiyasa Bana Gajiya Wajen Yaki Da Dukkan Wata Damuwarki
  21. Alokacinda Hasken Wata Ya Keto Gabatowar Asbahi Wani Sauyin Yanayine Yake Sauka Mai Dadin Sanyi Dake Ratsa Fata
  22. Gamsuwar Jiki Da Yanayin Annashuwar Ruhi Yana Haifar Da Tsantsar Kwanciyar Hankali Adaidai Lokacin Nutsuwa Tana Kara Samun Ma,abocin Kasantuwa Alokacin
  23. Kwatankwacin Debewar Kewar Irin Wannan Lokacin Nakeji Ajikina Aduk Lokacinda Nakejin Sautin Muryarki Tana Ratsa Kunnuwana
  24. Makurar Kalmomin Baki Sun Kure Wajen Kurewar Rerawa Dakuma Rubuta Sakonnin Dazasu Fahimtar Dake Irin Son Danake Miki Amma Har Yanzu Basu Ambaci Komaiba
  25. Hasken Zuciyarki Yana Kan Idona Idan Nayi Bacci Sannan Nayi Mafarkinki Hakan Yana Wadatar Da Zuciyata Samun Walwala Iya Tsawon Lokaci Mai Nisa
  26. Sallama Agareki Tareda Sako Na Musamman Wanda Yataso Daga Farkon Numfashin Zuciyar Dake Kiran Sunanki Akowane Bugun Numfashi
  27. Kin Isa Ayi Miki Komai Shiyasa Na Mallaka Miki Abinda Yafi Komai Muhimmanci Acikin Jikina Wato Zuciyata
  28. Na Gamsu Kuma Na Aminta Da Yawan Amanarki Shiyasa Na Damka Miki Amana Mafi Girma Acikin Rayuwata
  29. Kici Gaba Da Bani Kulawa Nikuma Zan Cigaba Da Kyautata Miki Iya Tsawon Adadin Kwanakin Numfashin Raina
  30. Kin Samu Kyakkyawan Matsuguni Acikin Raina Ina Alfahari Da Kasantuwata Acikin Rayuwarki Komai Wuya Zan Cigaba Da Kyautata Miki.
  31. Rabbi Sarki Mahallicin Bayi Nake Roko Yasanya Kina Cikin Koshin Lafiya
  32. tsamanin Sonkine Yake Dauke Da Al"audun Kafuwar Tarihin Rayuwar Kaunarki Wadda Ta Nashe Xuciyata Nakamu Da Tsananin Xillar Axabar Xumudin Sonki Wadda Hakan Ya Haifar Da Aukuwar Karuwar Begenki.
  33. Y'a masoyiyata Hauwa Mai kyakykyawan suna.
  34. Lallai Ba Shakka Sonki Xai Iya Xama Ajalina
  35. Musamman Idan Xuciya Ta Rasaki Babu Makawa
  36. Xan Bar Duniya Da Xanen Hotonki a Bangon
  37. Xuciyata.
  38. Ganin Kyakkyawar Fuskarki Kan Iya Samar Min Da
  39. Warakar Damuwa Da Bakin Cikin Xuciya, Duk Da
  40. Cewa Kyakkyawan Lafaxin Bakinki Shine Linxamin
  41. Dake Janye Ra'ayina Wajen Sha'awar Xama Kusada
  42. Ke.
  43. Ki Yarda Da Cewa Inasonki Kuma Baxan Sauya
  44. Ra'ayina Va Koda So Da Qauna Xasu Ratsa Jiki Da
  45. Jijiyar Jini.Kece Daya Tilo.
  46. Tarihi a Cikin Fadar Masoyan Asali.
  47. MY Zanzo gareki domin warkar da raɗaɗi da xogin da zuciyata
  48. keyi akan kaunarki, ciwon ƙaunarki ne abinda ke fisgar
  49. xuciyata ta jefani cikin duniyar tunaninki, Shalele ƴar lele
  50. sarakiya mamallakiyar xuciyana mai sarautar zuciyata sakon
  51. ƙauna mai ɗauke da tambarin zuciyata zuwaga Queen ɗina kina Zuciyata.
  52. Masoyiyata abar kaunata ki sani ina sonki ina kaunarki son da nake miki har ya kai ga…..ko da idanuwana a rife suke ke nake gani idan na bude su ke nake son gani. Ko da ba na tare da ke ina jin motsinki a cikin jikina Lokachin da nake tinaninki, kadaici shi ya fiye min komai dadi. Me ya sa kina rayuwa a cikin jikina ni ma ina rayuwa a cikin jikinki amma duk da haka nake jin tsakaninmu da nisa?
  53. Sarauniyata taho gare ni ki kama hannuna ki furtamin kalmar kauna a cikin kunnuwana…na rayu saboda ke ki zo ki mutu a kai na…ki sani ni fa ko a lahira idan an tashe mu to ke nake so a matsayin matata….na samu biyayyarki me kuma ya rage zan roka a wajen ubangiji?
  54. kawai numfashi nake so ga ubangiji don mu yi soyayya mai dorewa ni da ke….fatana Allah.ya tsawaita mana rayuwa ya ke abar kaunata…wacce nake ganin sunan ‘ya’yan da zan haifa a cikin idanuwanki….fakina da idanuwana ba za su iya fada miki ko kwatanta miki adadin son da nake miki ba don tuni na shide a cikin sonki, na zama ke. I Love You Mai Sona
  55. Kece kadai acikin zuciyata,kece waddarashin ganinki kemai dani maraya.
  56. Tunda idanuna suka kalli kyakkyawar fuskar ki,kunnuwana sukaji daddadan sautin muryar ki zuciyata ta fantsama cikin kogin kaunar ki ya sahibata abin alfaharina.
  57. Idan ina tare da ke ko,online ko a Gidan ku ko a
  58. Gari farin cikina bayamisaltuwa na kanjikamar kada na tafi gida domin
  59. irin yadda nake son kasancewa tare da ke a kowanne lokaci ya mamaye dukkan wani burina.  Hakika yawan sauraron muryar ki kadai ka
  60. iyasawa naso abani daki na tare a gidan ku, bana tunanin matsalar komai in har
  61. idanuwana nayin arba da kyakkyawar fuskar ki mai
  62. cike da annuri da haske kamar wata dan daren 14,
  63. ki kasance tauraruwa mai haskake gani na, nakan ji
  64. dadin muryar ki a duk sanda kika furta man Kalmar so.
  65. Lallai ni yau na zama bawan soyayya wanda nake ta fangima da fangan
  66. fangan a cikin tafkin dausayin soyayyah wadda rasa ta zai iya tarwatsa dukkanin wani fatana da farin cikina.
  67. A duk sanda na kwanta bacci zuciyata zata shiga shiryo mani irin daddadar soyayyar da ya wakana a tsakanin nida ke, sai kawai in ga ina wani irin murmushi jin dadi saboda dace da nayi dake a matsayin masoyiyata.
  68. Amincin Allah ya tabbata ga amintacciya, Wacce zuciyata ta
  69. aminta da amincinta, Wacce nakeyiwa SON da bana yiwa
  70. kaina, wacce tazamto sarauniya me isashshen iko datake
  71. tafiyar da mulkinta a yalwatacciyar fadar zuciyata, Ina
  72. Tabbatar miki bawata bayanki, Ke kaɗai ce tawa.
  73. Soyayya na iya chanja mutum, domin ita Soyayya ba'a ganin,
  74. balle a koreta ko a hana ta shiga zuciya. Ba'a Cewa Soyayya
  75. ga yadda ake so, sai-dai kayi yadda take so. Ba'a Shiri wa
  76. Soyayya, ko babu shiri Idan taxo kamar mutuwa haka zata
  77. shiga Zuciyar mutum. Duk wanda yayi so dan Allah to shine
  78. keda riba, cikin Soyayyar ki babu sirki, na gani kuma na
  79. gamsu kuma na Tabbatar da ke me ƙauna tace ta hakika, ki
  80. sani, ni bazan taba son wata ƴa mace wacce bake ba, domin
  81. zuciyata bazata taba jindadin zama da wata ƴa sama dake
  82. ba, duk wani jin daɗin duniya bai damen ba indai babu ke.
  83. Rayuwata Fansarki ce, Zuciyata Tini ta Rikirkice, Kunnuwana
  84. Sun ƙi Karban zance, idanuwa na sun so su makance, duk
  85. sanadin Soyayyar da kika amince mini, Mulkin zuciyar Shine
  86. aiki na, samun farin cikin ki jindaɗi nane, Murmushinki
  87. Annashuwa Ce ga zuciyata, Duk ranar da kikai fishi Dani
  88. banida kwanciyar hankali, Ni Bawa ne ga Zuciyar ki.
  89. Kalaman Soyayya Ga Masoyanda Basa Gari Daya

    Sako rubuce yafi sako da baka tasiri musamman ga mata. A kullum zaka kira budurwa ka soma 10 kanace mata kana sonta bata jin Kalmar da bauyi ko daraja akan ka tura mata sakon soyayya. Wannan yasa muka zakulowa masoya mata kalaman da zasu rika turawa masoyan su ta waya. Musamman ma ace ba gari daya kuke ba. 

    1:💕 Tabbas rashin ka kusa dani yana cutar da lafiya ta, Amma idan na tuna nice zan zama uwar yaranmu, sai naji zuciyata ta cika da kaunar, nan take ya dauke mini kadaicin da nakeyi na rashinka a kusa.

    2:💕 Idan mace na son namiji Bata ganin nisan inda duk yake a duniya ganin tana fatan cimma burinta na auren namiji irinka.

    Ina sonka masoyina.

    3:💕 Duk da kayi nesa dani, hakan bai yiwa zuciyata ganinka kusa dani ba.

    Da fatan komai yana gudana yadda ake fata.

    4:💕 Yanzu haka a waje biyu nake a bayyane, anan inda nake, da kuma inda kake. Hakan ya tabbatar mini ba nesa dani kake ba.

    5:💕 Duk macen data kalli nisan garin da wacce take so yake, wannan ba masoyiyar gaske take ba.

    Jarumina nesan ka dani bai sawa naga nisan inda kake ba.


    6:💕 Abunda ya hadamu soyayya bazai bari saboda nesa da kake ya shafi soyayyar mu ba. Burina shine ganin kaina a matsayin matarka.

    7:💕 Nisanka dani, da yadda hakan yake sani kewarka. Bazai sani karaya ba akan soyayyan da nake maka..

    Ina sonka har ga Allah. Burina na mutu a akan cinyarka.

    8:💕 Rayuwa na, zuciya ta, addinina da son da nake maka, sun hanani ganin ka mini nisa.

    A kullum ina sauraron sakonka na ranar dawowanka.

    9: Matsalar soyayyar nesa da namiji shine rashin sanin matsayinta a gunka shi na rashin tabbacin kana kewana ne ko kuma ka manta dani wannan ne ban sani ba. Sai dai ina tabbatar maka cewa, zuciyata a cike take da kaunarka na babu wurin ajiye wani da namiji da ya wuce kai. Ina tabbatar maka da na sadaukar da zuciyata a gareka.

    10: Baka sanin mace mai rike alkawari ba irin budurwar da take soyayyar nesa na gaskiya. Wannan yasa na turo maka sakon sanar da kai, har yanzu kai nake so kuma kai nake jira, kuma kaine zaka aureni kai ne kuma zaka mini cikin da zan haifa maka yara da kuma samarwa iyayenmu jikoki .


    Ina tunatar da kai, nisa da kayi dani bazai iya yiwa son da nake maka kwarzane ba.

    Kaman yadda muka sha fadi a baya, irin wadannan sakonnin da masoya suke rainawa, sune kuma suke Karawa masoya son juna.

    Masoya suna kafa irin wadannan sakonnin a matsayin hujar da zasu tabbatar wa duk mai neman sanin ga abunda take so. Da fatan masoya zasu yi amfani dasu ta hanyar daya dace.



0 Response to "Kalaman Soyayya 2022"

Post a Comment