Illolin Auren Bazawara Ko Macen Da Ta Girmeka
Illolin Auren Bazawara Ko Macen Da Ta Girmeka
TAMBAYA
Assalamu alaikum malam menenee illa da kuma amfanin auren bazawara ga namiji saurayi wanda bai taba yin aure ba? Sannan kuma me yasa iyayenmu mata da abokai da sauran yan uwa suke nuna kyamarsu tare da tsoratar da saurayi idan yace zai auri bazawara?
AMSA
Babu wani illa ga saurayin da bai taba aure ba idan ya auri bazawara. Sai dai zaurawan sun kasu Kashi daban daban._ _Akwai mai shekaru akwai mara su. Akwai wacce take da yara akwai wacce bata taba haihuwa ba don haka ya dangancin wacce kake son ka aura kuma da yawan kai naka shekarun.
Auren bazawara ga saurayin ba ace masa yana da illa sai dai ace akwai wasu matsalolin da suke iya biyo bayan aure. Idan mace mai 'ya'ya ce kuma manya dole ne ka iya jimre gani ganin da zasu rika yi maka. Saboda ba dukanninsu suke ganin ka cancanci auren mahaifiyarsu ba. Idan kuma kanana ne kuma a gabanta suke dole kayi jimirin daukar dawainiyar su daidai karfin ka. Idan a gaban mahaifinsu suke to ka sani dole watarana zasu kawo muku ziyara na kwana ko na yini yana da kyau ka amshe su hannu biyu biyu.
Idan kuma irin wacce ake cewa sauta ga wawa ce wannan ba ta da matsala sosai.
Babban matsalar auren bazawara ga wanda bai taba aure ba shine ta riga ta ginu akan wani tarbiya data samu wajen mijinta na baya. Kai kuma sabon shiga ne, don haka yanada wuya ka iya sauketa daga kan wannan layin.
Alfanun auren bazawa ga Wanda Bai taba aure ba shine ta riga ta san gwagwarmayen rayuwar aure. Tasan yadda zata kula da miji da abunda ke kewayen mijinta.
Sai dai muddin zaka auri bazawarar da mijinta ya mutu ya barta sai ka hada da hakuri, domin duk abunda zaka mata sai ta nuna maka wancan ba haka yake Mata ba koda kuwa bai mata kamar yadda kake Mata.
Akwai wasu dabi'un mutane da suke yi ba tare da hujja ba. Kushe auren bazawara yana cikin su.
Mutane suna amfani ne da ance kace ba da hujja ba. Sau da dama ana tsoratar da samarin da ke son auren zaurawa ba da hujja ba. Kamata yayi kamin ka kushe bazawarar da saurayi ke son aure, ka tabbatar wacce yake son auren itace take da wani illa amma ba wai ka yanke mata hukunci da wata bazawarar data yi wani laifi a can ba.
Suma zaurawa mutane ne. Don haka kowacce da hakinta da dabi'unta su za a duba amma ba zawarcin nata baA takaice kenan.
0 Response to "Illolin Auren Bazawara Ko Macen Da Ta Girmeka"
Post a Comment