-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Alamomin Matan Aure Masu Bin Maza

Alamomin Matan Aure Masu Bin Maza

Alamomin Matan Aure Masu Bin Maza

A duk lokacin da na ji labarin matar aure na bin maza a titi tana lalata da su hankalina na matukar tashi, saboda dalilai kamar haka.

Da farko kin ci amanar iyayanki da su ke zaton sun fita hakkinki sun aurar da ke, kin ci amanar 'ya'yan da ki ka Haifa,  domin duk ranar da asirinki ya tonu kin hada su da abun kunya kin tozarta su, kin ci amanar addininki da sunnar Annabi Muhammad Sallallahu alaihi wassalam wato aure, babbar cin amana kuma ita ce ta mijinki da ya  biya sadakin auren ki, ya killace ki a zatonsa shi kadai ya mallake ki.

Sai babbar masifa da za ki iya janyowa kan ki da mijinki sune,  za ki iya kawo masa shegu gidansa, ya rayu da wadanda ba muharramsa ba, su ci gadon da bai halatta su ci ba, daga karshe su zamewa al'umma masifa.

Ina son ki sani 'yar'uwa da zarar kin yi aure dole ki hakura da abun da ki ke so, ki koma rayuwa akan abun da ki ka samu, idan ke yar son holewa ce ki hakura da samun mijinki, idan ke mabukaciya ce ki hakura da yadda ki ka samu mijinki, idan kina auran tsoho ki hakura tunda kina sane da hakan ki ka aure shi, amma kina da zabin da ba dole sai kin zauna zaman aure ba, wallahi ya fi abun kunya a gareki ace an kama ki da wani  Kato kuna lalata kina da aure da ace kin nemi mijinki ya sake ki saboda ba ki gamsu da auransa ba 

Akwai matan da ke kafa hujjar cewar mazajansu ba sa zama, ko ba sa iya ciyar da su, ko basa iya sauke hakkin auren da ke kansu, to ki sani ya fi miki alkairi ki kashe auranki wallahi akan ki zauna kina zina da aure, domin wannan bai isheki hujja a gaban ubangiji ki ba.

Yar'uwa ita Zina 'MASIFACE', kuma datti ce, ko ga wacce ba ta da aure balle mai aure, ki sani duk namijin da ya kusance ki ta hanyar zina har duniya ta nade ya daina ganin mutunci ko da kuwa ya aureki, sannan ko za ki saka kaya dubu a jikinki tsirara ya ke kallonki, kuma daga sanda ya gama amfana da kekare ya fiki daraja gurinsa, za ki zaton babu kamarki a gurinsa sanda ya ke amfana da ke, zai iya wulakanta kowa har iyalinsa saboda ke, amma ki sani na lokaci ne kalilan farin cikin, bakin ciki na har abada.

Ki sani 'yar'uwa babu wata mace da ta tara abun duniya da zina ta kare lafiya, idan takamarki neman kudi da abun duniya, ki bincika tarihin matan da su ka yi lalata a baya, sun kare cikin mugun ciwo ko talauci ko su wulakanta,  sannan lokaci kalilan ake daina yayinsu, duk kyansu da kyan jikinsu, kamewa da rike mutunci shine zai dawwamar da ke cikin farin ciki a matsayinki na di ya mace, watarana za ki wayi gari kowa ya watse.

Watarana muna hira da wata Mata da ke cikin masifa, an koreta daga gidan haya babu abun da za ta ci, ga ciwo ga yayan shegu hudu a gabanta ta ce "Hajiya wallah sanda na ke tashen kyauna kamar balarabiya na ke, don haka da masu kudi na ke harka, a shige dani kayataccen gida a hadaddiyar mota masu gadi na durkusa min, na mallaki komai, amma daga baya ta koma sai dai masu gadin masu kudin nan su nemi ni, ta kai yanzu masu ganinma sun fi Karfina korata su ke yi, ban tsira da komai ba sai shegun yara hudu" ta fashe da kuka, mun so taimaka Mata, sai mu ka ji labarin ta mutu da wani mugun ciwo.

 Don haka babu wata hujja da za ki kafawa Allah idan ya dauki rayuwarki kina aikata fasadi,  za ki iya mutuwa a koda yaushe.

Mun sani akwai kaddara da jarabawa ta rayuwa, amma ki sani hakuri da kauda kai, da yawaita ibada da yawaita istigifari da kankan da kai, da kamewa da rike mutuncinki da daina hangen abun da wasu ke da shi,  zai iya taimaka miki, babu wani farin ciki da za ki samu da zina wallahi komai yawansa, na lokaci kalilan ne.

Daga karshe ki sani wallahi duk abun da ki ke da shi, da duk abun da ki ka tara za ki dawwama cikin bakin ciki muddin kina aikata Zina da auranki, ke ko babu aure muddin ba ki tuba ba, sannan duk lokacin da dubunki ta cika kin tozarta kan ki da 'ya'yanki da mijinki da zuri'arki, sai kin yi da na sanin ba ki taba zuwa duniya ba, amma kina da damar tuba a yanzu.

Kuma mazan da ke bin matan aure ku sani kuna da Matanku wani zai iya nemansu, kuna da yaya da 'yan'uwa da Kanne da yayye, yanda ka ke jin dadin bin matar wani, kaima wani zai bi ta ka, don na ji suna cewa wai neman matar aure ya fi sirri (wa'iyazubullah), saboda ba zata gayawa kowa ba, kuma ko ciki ta yi, sai ta kaiwa mijinta ba Wanda zai gane, to Allah yana kallonka, kuma ka sani za ka hadu da masifar da sai ka gwammace ba a haifeka ba, kuma sai an bi matarka ko 'yarka,  kuma sai an jarrabeka da rashin kwanciyar hankali duk abun da ka ke takama da shi, don haka ka kare mutuncin matar wani, sai Allah ya tsare iyalinka.

Dukkanmu masu aikata laifine, amma muna rokon ubangiji ya nisantamu da zuri'armu ga aikata Zina da duk wani sabo, Allah ka tsare imaninmu ka tsare mutunci, Allah ka saka mu yi karshe mai kyau, Allah kar ka kamamu da laifin da wawayan cikinmu ke aikatawa, ba mu karfin jarabawarka ba, amma muna rokonka ka tsare mutunci, Allah mun tuba, Allah mun tuba, Allah ba ma alfahari,  Allah ka shiryemu.

Daga: Fauziyya D Sulaiman

0 Response to "Alamomin Matan Aure Masu Bin Maza"

Post a Comment