Kalaman Soyayya Masu Saka Kwalla
Tuesday, July 5, 2022
1 Comment
Kalaman Soyayya Masu Saka Kwalla
Kalaman Soyayya Masu Saka Kwalla
- Masoyiyata Allah ya halicci zuciya be domin soyayyah zan kasance Mae yiwa soyayyarki bauta tamkar bawa agareta, ina mai matukar godiya ga Allah da hotemin ke amatsayin masoyiya.
- A duniya duk Wanda yasameki a matsayin masoyiya wallahi yagama yin babbar nasara a rayuwa, domin kin kasance mace wadda ta mallaki duk abunda wata mace takeda shi, samunki ba karamar nasara bace.
- Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d'auke da 'korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d'auke da tsintsaye. Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
- Matata Uwar 'ya'yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d'aya, ina cike da zumud'in son dawowa domin cin girkin ki mai dad'l. ki kula min da kan ki, sal na dawo. Ina son ki matata.
- Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za'a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.
- so wani abu ne mai kyawu, kuma wani yanayi ne da mutum zai so ya damke. 'So. shi ne yanayin da kan sa ka ji ka a raye. Ina_fatan kin fahimci cewa zan so ki har karshe, saboda ba kin kasance budurwata kadai ba, ke ce Aminiyata.
- So dayawa wasu masu yiwa soyayya mummunar fahimta sukance mace batada tabbas akasin basu samu wadanda ke kaunarsu da gaskiyaba, nikuma inada ke kuma nagamayin babbar sa'a a rayuwata, ke macece wadda babu irinta a rayuwa.
- Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba.
- Matata Uwar 'ya'yana mai share hawayena tabbas samun ki a matsayin matata babbar nasara ce a rayuwata ga dangina da kuma duniya baki d'aya, ina cike da zumud'in son dawowa domin cin girkin ki mai dad'l. ki kula min da kan ki, sal na dawo. Ina son ki matata.
- Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
- A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.
- Kasancewar ki a tare da ni, ya sa ni jin kaina a matsayin wani mutum mai daraja ta musamman. Ina son ki, so irin wanda kalmomi ba zasu iya bayyanawa ba. Murmushinki Yayi, dariyarki Ba'a magana, Kin iya tafiya, Komai naki mai kyau ne, ina fatan mu Kasance tare. Naso ace inada wani qarfi domin tabbatar miki yadda kike ta Musamman a zuciyata, ke wata kalma ce wacce ke zane a xuciyata.
- Samuwar ki a cikin rayuwata ya samar da gagarumin canji ga ‘karuwar farin-ciki na ta hanyar sauraren muryarki da kuma kasantuwata a tare da ke cikin rayuwarki mai tsari. Ke ce tauraruwar da hasken ta yake haskaka birnin zuciyata, kina d’aya daga cikin mutanen da ba zan taba mantawa da su ba har abada a cikin rayuwata. ki huta lafiya
- Agaskiya ina matuqar sonki saudat wlh sosai sosai fiye da yadda kife ke son ruwa hmm to dan yi murmushi mana (ana furtawa masoyiya irin kalamannan cikin murmushi me dauke da kallon qauna,mace tana iya hadawa da hawayen qauna dan raunata zuciyar masoyinta da qara so da qauna)
- Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyartawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su. Ina son ki sosai da zuciya d’aya
- Haskenki tamkar hasken farin watane mai haskaka sararin samaniya Wanda take dauke wani sanyi mai ratsa jini da jijiya, haskenki tamkar hasken zinariya Wanda yake sheqi da walwalin haske marasa misaltuwa.
- yaune nake so na baiyyana miki irin son danake miki ,kisani shamsiyya wlh bani da wasu kalmomi ko ma auni dazasu iya bayyana son danake miki ,nidai ina sonki ,ina qaunarki ,kece burin zuciyata ,farin cikin raina cikar mafarkina wlh sham siyya matuqar ba zaki'iya qairga ruwan tekuba to bazaki iya qididdi ge son da nake miki ba
- Cutar sonki batada magani agurin likita saidai ke,cancantarki ce tasa hakan zurfa'a ina me tabbatar miki bazan taba jabaya a soyayyarkiba kece farincikin raina burun zuciyata zurfa'ah tawa wai dan Allah zurfa'ah wanna irin so nake miki haka? Pls fadamin dan Allah, Uziri zakiyimin masoyiyata nakan rasa kwanturol dazarar naji dadadan kalamanki masu dake da wani sauti me ratsa zuciyata ,kai lallai nayarda so Aljannar duniya ni gatawa na samu hmm Allah yabani ke hafsat.
- Kasance mai faranta zuciyar wanda yake kokarin faranta taka zuciyar koda kuwa kai zaka shiga cikin damuwa ne, Kasance mai kare mutuncin masoyin ka a lokacin da kuke tare ko bakwa tare da shi, Tirsasawa zuciyar ka son wanda ya nuna yana son ka a zahiri babbane ko yaro, talakane ko mai kudi, mace ko namiji, kyakkyawa ko akasin haka.
- Gajeriyar saƙon soyayya na iya yin silar kara shauƙi a zuƙatan masoya, Gajerun kalaman soyayya Sukan bayyana tare da zayyana abunda zuciya take ƙunshe dashi zuwa ga masoyi ko masoyiya. Don haka idan kuna son nuna soyayyar ku ga masoyan ku, Yana da kyau kuna aika musu da wasu gajerun saƙonni na soyayya masu ban mamaki kuma na musamman!
- Shin masoyina izuwa yanzu ko ka fara jin gajiya a jikinka kuwa? Saboda ka kasance kana motsi a cikin zuciyata a tsawon dare ka kuma kasance mai zagaya dukkan jikina ta kafar da jinin jikina ne kawai yake gudana a cikin kowace safiya da yini. Ina son ka. Wajen zubin kwalliya Ke gwana ce, kin cinye gasar kyau da zuciyata ta saka, Ina Mata suke, suzo su kalli sarauniya ta!
- sonki yana cikin zuciyata, amma ina kokwanton kada ya zama tsuntsu ya tashi, idan har na ya kasance kin ci gaba da nuna rashin kulawarki a kaina. Kin saye zuciyata ƴar amana, duk sirrika na kin lamishe su, baki rage min komai ba sai zuciyar, dan Allah karki nisa dani!
- Muryarki tamkar sarewa ce wadda idan ana busata tamkar anayinta ne a cikin karkashin zuciyar mai sauraro, ina matukar alfahari da ke a rayuwa. Ina son na kasance a gefen ki kullum, domin na rinƙa sauraron sautin muryar ki mai kama da na kanari , na ringa kallon murmushin ki kamar farin madara!
- Kin dauke makullin shiga zuciyata, dan haka babu wata mace da zata samu damar shiga kece Sarauniyar Zuciyata Kamar yadda ake gane farin fulawa acikin jajayen furenni, haka Soyayyar ki take bata boyuwa a zuciyata, Ina son abubuwa uku agareki, idanun da basa kuka, bakin da baya karya, Soyayyar da bata mutuwa.
- Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni! Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan taba mantawa dake ba masoyiyata, bana fatan ranar da zaki kasance cikin koda kuwa wani ne zai batamiki rai barantama nida kai na.
- Ina son ki zamo mallakina a cikin mafarkina da kuma a zahiri, ki zamanto cikin hirata da sauran dukka zantukan bakina faruwar hakan zai inganta farin cikin zuciyata. Fatana a kullum ki gamsu da cewa, Ina Son Ki.SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d'aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.
- So gamon jinine, hakika sonki ya zamo jinin jikina na godewa Allah Subhanahu Wata’alah da yayi sanadiyar haduwa ta dake kuma hat na iya kasance mai kaunar ki a wannan duniyar ta mu ta Masoya, Ina Son Ki!..
- kyakkyawa mai kyan tsari,a duk lokacin da nake kallonki, tamkar kyakkywar fulawa mai furanni ma'abota debe kewa da sanya nishadi a zuciya ki kan zamo min. Bani da kamar ki a rayuwata, karki gujemin, ki kasance dani, zan zama garkuwa agareki
- Yanayin zafi kan sa mutum yayi gumi amma duk yadda yanayin zafi yayi tsanani da zarar na tina ki Masoyayi ta sai naji wani sanyi a jikina har cikin birnin Zuciya ta, ta yadda zanta dacewa ana cikin yanayin zafi ne ma duk kuma a sanadiyar Soyayyar ki.
- SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matsawar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu? Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya. karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata
- Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare. Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwanki. Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki. Aminan juna nake so mu kasance, ba abokai ba, domi mu kasance da Soyayya ta har abada. Wasu lokutan idanuna suna min gizo da hoton ki, amma nasan zazzafar qaunar da nake miki ne, saboda kece a zuciyata!
- Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA” hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.
- A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba. Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba. Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari. Ina Son Ki kuma ba zan taɓa canjawa a kan hakan ba.
- Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada dadewaba domin ki tabbatar da abun da na ke fad’a gaskiyane dama an ce zuwa da kai ya fi sak’o. Ki huta lafiya farin cikin zuciyata. Ina son ki.
- Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad'uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya. Dadi wuya ni dake babu batun fishi da juna, ko munyi ma mu zamu gyara kammu. Ina Sonki.
- A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin d’aya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki, domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a koda wane lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada. Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
- Ke farar macece wadda ake yiwa alkunya da alkyabbar mata, gaki fara zuciyarki fara gaki da farar aniya, ina sonki kuma ina kaunarki kuma aurenki shine cikon muradin rayuwata. Na yi miki alkawari zan kasance dake har iya tsawon da nunfashi zai zauna a jikina. Bazan yada ke ba!
- Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar 'karshe, saboda kai ba saurayi ne ka. Hankali na zai kasance a kwance ne ranar dana ganki cikin daki rufe da mayafin amarci, na kiraki da amaryata.
- SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai k’ona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi. Idan munyi Aure, bani da wata fargaba, domin naci zabe, mulki kawai zanyi domin saki farin ciki.
- Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya, haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki. Na makance akanki, har nakai matsayin da bana gane kowa idan bake ba, Soyayyar ki ta wuce kima a zuciya ta! Alkawarin mu na nan, ni dake, babu rabuwa, babu yaudara, babu cin amana, kullum Farin ciki Habibina!
- Yau zanyi shela, duniya ta sani cewa kin mallaka min Zuciyar ki, Kuma nafi kowa farin ciki da murna, nagode Aminiyata!, Sautin muryarki nake son nake ji a kullum domin yana sakani shauki, kuma yana sani qara sonki Matata!, Masoyiyata! Qaunata agareki Gaskiya ce, Kalaman dake fitowa a bakina Zahiri ne. Ki yarda dani!, Zan fafa ta da koma wanene indai akan ki ne, na bada rayuwa ta ta zamo fansa. Kece Duniyata!
Wai me yasa baya copying ne?
ReplyDelete