-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) Ta Buɗe Shafin Cike Gasar Rubutu Ga Ɗaliban Sakandare.

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) Ta Buɗe Shafin Cike Gasar Rubutu Ga Ɗaliban Sakandare.

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) Ta Buɗe Shafin Cike Gasar Rubutu Ga Ɗaliban Sakandare.

Gasar Rubutun Shekara-shekara ta NERC: An kara wa'adin cike ƙaddamarda gasar kasidu zuwa 29 ga Yuli, 2022.

Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) na daya daga cikin hukumomin dake bawa ɗalibai tallafi a wannan karon hukumar ta sake buɗe shafin cike gasar rubutu ga hazikan ɗalibai inda a baya ta rufe shafin 24 ga watan yuni amma a yanzu hukumar ta kara wa'adin cike ƙaddamarda gasar  zuwa 29 ga Yuli, 2022.

Wannan gasa tana buɗe ga ɗaliban SS2 KAWAI a Najeriya. Daliban SS2 masu sha'awar su rubuta makalar da bai gaza kalmomi 450 ba kuma bai haura 500 ba, a kan maudu'i mai taken "Benefits of metering in the Nigerian Electricity Supply Industry (NESI)".

Hukumar ta tanadi Kyaututtuka masu ban sha'awa da waɗanda suka lashe matsayi na daya, na biyu da na uku. Don haka muyi amfani da wannan damar mu cikewa kannanmu ko yayanmu domin su kasance acikin wadanda za'a goga dasu acikin wannan gasar.

Yadda Zaku Cike

Domin cike wannan gasar ku aika da kasidar da kuka rubuta zuwa ga email kamar haka: 

electricitychallenge@nerc.gov.ng ko kuma ku rubuta a takarda kuma ku sakata acikin envelop ya kin ku aikata zuwa Nigerian Electricity Regulatory Commission NERC HOUSE, PLOT 1387 CADASTRAL ZONE, A00 CBD. Behind BOA House Abuja.

Dokokin Kaddamarwa

  • Dole ne a ƙaddamar da duk rubutun a cikin tsarin PDF
  • Duk abubuwan da aka gabatar dole ne su ƙunshi SUNAN DALIBAN, BAYANIN GIDA KO MAKARANTA, BAYANIN EMAIL DA LAMBAR WAYA akan takaddun PDF da aka ƙaddamar.
  • Akiyaye cikewa fiye da daya hakan zai janyo fita daga cikin gasar.

0 Response to "Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Najeriya (NERC) Ta Buɗe Shafin Cike Gasar Rubutu Ga Ɗaliban Sakandare."

Post a Comment