Zuwa ga masu jiran tantancewa na shirin N-Power Batch C2
Zuwa ga masu jiran tantancewa na shirin N-Power Batch C2
Hukumar N-Power ta sanya ranar 14th zuwa 25th ga wannan watan na Yuni (14th -25th June 2022) a matsayin ranakun da za'a gudanar da tantance waɗanda sunayensu suka fito a wannan kashin na biyu wato Batch C2.
Saboda haka hukumar take kira ga dukkanin waɗanda sunayensu ya fito a kashi na biyun dasu shiga yanar gizon hukumar a https://nasims.gov.ng/login domin duba inda zasuje domin tantance su.
Haka kuma zasu iya amfani da wannan lambar itama domin dubawa*45665#
Ababen da za'aje dasu wurin tantancewa sun haɗa da:
1. Lambar N-Power dinka/ki (N-Power Identification Number)
2. Kati zama ɗan ƙasa ko katin zabe ko katin lasisin tuƙi
3. Takardun shaidar kammala karatu: (Primary certificate, Secondary certificate, NCE, Diploma, Degree da dai sauransu
Allah ya bada Sa'a. Amin
0 Response to "Zuwa ga masu jiran tantancewa na shirin N-Power Batch C2"
Post a Comment