-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Yadda Zaku Cike Sabon Tallafin Kuɗi Na Nigeria Youth Futures Fund(NYFF)

Yadda Zaku Cike Sabon Tallafin Kuɗi Na Nigeria Youth Futures Fund(NYFF)

Yadda Zaku Cike Sabon Tallafin Kuɗi Na Nigeria Youth Futures Fund(NYFF)

Wannan wani shiri ne mai suna Nigeria Youth Futures Fund wanda kungiyar (Mcarthur da Ford Foundation) suka dauki nawin gabatar dashi, kuma shiri ne da aka shiryashi domin bayar da tallafi ga matasan Nigeria domin su dogara da kansu.

Manufar Wannan shirin ita ce karfafawa, tallafawa, da ba da damar matasa a Najeriya su shiga cikin jagorancin matasa, fafutuka, da sauye-sauyen zamantakewa ta hanyar tattaunawa da manufofin da za su haifar da sakamakon da zai taimaka wa matasa su tsara da inganta ci gaban matsakaici da dogon lokaci na kasa.

Akwai Bangarori hudu (4) daban-daban wanda wannan shirin ya kasu, gasu kamar haka:

  • 1. Small Grant: $500- $1000 for 60 Targeted individuals
  • 2. Action Grant: $1000- $3000 for 40 Grassroot & Community based organizations
  • 3. Development Grant: $3000-$6000 for 25 Youth-led & Youth Focused Organizations
  • 4. Catalytic Grant: $ 40,000 for 6 Civic and Innovation Hubs

Yadda Zaku Cike Tallafin Kuɗi Na Nigeria Youth Futures Fund

Kamar yadda mukayi maku jawabi a sama cewa shi dai wannan tallafin na kuɗi na Nigeria Youth Futures Fund ya kasu 4 hudu, abinda zakuyi shi ne ku latsa shafin yanar gizo-gizo da ke a kasa

https://nigeriayouthfund.org/grant-application/

Bayan ku latsa sai ku nemi daya daga cikin bangarori hudu da muka zayyana wanda yayi dai-dai da yanayin Kasuwanciku idan kuma individual ne sai ku shiga na farko.

ALLAH yasa mudace baki daya 

0 Response to "Yadda Zaku Cike Sabon Tallafin Kuɗi Na Nigeria Youth Futures Fund(NYFF)"

Post a Comment