Yadda za a yi rajistar katin zabe INEC da wayar hannu
Yadda za a yi rajistar katin zabe INEC da wayar hannu
1. Masu son rajistan su ziyarci https://cvr.inec.gov.ng or https://cvr.inecnigeria.org a na'urar da suke shiga yanar gizo don fara rajistan.
2. Mai son rajistan ya fara bude asusu da shafin ta hanyar amfani da adireshin imel domin fara rajistan.
3. Bayan bude asusun, za a tura maka sako cikin imel din da ka yi rajista da shi.
4. Ka bude imel din ka, ka latsa sakon don tabbatarwa sannan ka cigaba da rajistan
5. Mai yin rajistan zai cike bayanansa a shafin da ya bude.
6. Bayan cike bayanan cikin fom, sai ka zabi rana da cibiyar rajista da kake son zuwa domin a karasa maka rajistan a kuma dauki hotonka da na zanen yatsu.
7. Mai rajistan zai latsa 'submit' bayan an karasa maka rajistan, daga nan za ka fitar da takarda mai dauke da bayanan ka.
8. Sai ka yi printing din takardar mai dauke da bayanan ka.
9. Ka ziyarci cibiyar rajista na INEC da takardar ka a ranar da ka zaba domin a dauki bayanan ka.
10. Za a baka takardar shaidar cewa ka kammala rajistar wadda za ka yi amfani da shi ka karba katin zaben idan ya fito.
KARIN BAYANI#
- Duk wanda yayi rasjistan zaya iya zuwa ofishin INEC a jiha ko karamar hukuma su karasa yin rajistan daga ranar Litinin 19 ga watan Yuli da aka sa ran fara karasa rajistan a ofisoshin INEC.
0 Response to "Yadda za a yi rajistar katin zabe INEC da wayar hannu"
Post a Comment