Kalaman Soyayya Ga Masoyanda Basa Gari Daya
Kalaman Soyayya Ga Masoyanda Basa Gari Daya
Sako rubuce yafi sako da baka tasiri musamman ga mata. A kullum zaka kira budurwa ka soma 10 kanace mata kana sonta bata jin Kalmar da bauyi ko daraja akan ka tura mata sakon soyayya. Wannan yasa muka zakulowa masoya mata kalaman da zasu rika turawa masoyan su ta waya. Musamman ma ace ba gari daya kuke ba.
1:💕 Tabbas rashin ka kusa dani yana cutar da lafiya ta, Amma idan na tuna nice zan zama uwar yaranmu, sai naji zuciyata ta cika da kaunar, nan take ya dauke mini kadaicin da nakeyi na rashinka a kusa.
2:💕 Idan mace na son namiji Bata ganin nisan inda duk yake a duniya ganin tana fatan cimma burinta na auren namiji irinka.
Ina sonka masoyina.
3:💕 Duk da kayi nesa dani, hakan bai yiwa zuciyata ganinka kusa dani ba.
Da fatan komai yana gudana yadda ake fata.
4:💕 Yanzu haka a waje biyu nake a bayyane, anan inda nake, da kuma inda kake. Hakan ya tabbatar mini ba nesa dani kake ba.
5:💕 Duk macen data kalli nisan garin da wacce take so yake, wannan ba masoyiyar gaske take ba.
Jarumina nesan ka dani bai sawa naga nisan inda kake ba.
6:💕 Abunda ya hadamu soyayya bazai bari saboda nesa da kake ya shafi soyayyar mu ba. Burina shine ganin kaina a matsayin matarka.
7:💕 Nisanka dani, da yadda hakan yake sani kewarka. Bazai sani karaya ba akan soyayyan da nake maka..
Ina sonka har ga Allah. Burina na mutu a akan cinyarka.
8:💕 Rayuwa na, zuciya ta, addinina da son da nake maka, sun hanani ganin ka mini nisa.
A kullum ina sauraron sakonka na ranar dawowanka.
9: Matsalar soyayyar nesa da namiji shine rashin sanin matsayinta a gunka shi na rashin tabbacin kana kewana ne ko kuma ka manta dani wannan ne ban sani ba. Sai dai ina tabbatar maka cewa, zuciyata a cike take da kaunarka na babu wurin ajiye wani da namiji da ya wuce kai. Ina tabbatar maka da na sadaukar da zuciyata a gareka.
10: Baka sanin mace mai rike alkawari ba irin budurwar da take soyayyar nesa na gaskiya. Wannan yasa na turo maka sakon sanar da kai, har yanzu kai nake so kuma kai nake jira, kuma kaine zaka aureni kai ne kuma zaka mini cikin da zan haifa maka yara da kuma samarwa iyayenmu jikoki .
Ina tunatar da kai, nisa da kayi dani bazai iya yiwa son da nake maka kwarzane ba.
Kaman yadda muka sha fadi a baya, irin wadannan sakonnin da masoya suke rainawa, sune kuma suke Karawa masoya son juna.
Masoya suna kafa irin wadannan sakonnin a matsayin hujar da zasu tabbatar wa duk mai neman sanin ga abunda take so. Da fatan masoya zasu yi amfani dasu ta hanyar daya dace.
0 Response to "Kalaman Soyayya Ga Masoyanda Basa Gari Daya"
Post a Comment