Hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'in Najeriya watau JAMB ta sanar da sakin sakamakon jarabawar bana 2022 da dalibai a fadin tarayya suka rubuta
Saturday, May 14, 2022
Comment
Hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'in Najeriya watau JAMB ta sanar da sakin sakamakon jarabawar bana 2022 da dalibai a fadin tarayya suka rubuta
Shugaban sashen hulda da jama'a na JAMB, Fabian Benjamin, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, rahoton TheNation. Ya bayyanawa dalibai da suka zana jarabawar cewa za su iya duba sakamakonsu a wayoyinsu na tarho.
"Don duba sakamakon UTME, abin da kowani dalibi ke bukatan yi shine tura UTMERESULT zuwa 55019 da lambar wayar da akayi amfani wajen rijista, za'a turo musu sakamakon."
Wannan ita ce hanya daya tilo da aka samar don duba sakamakon a yanzu don wasu dalilai."
ALLAH yasa mudace baki daya
0 Response to "Hukumar shirya jarabawar shiga jami'o'in Najeriya watau JAMB ta sanar da sakin sakamakon jarabawar bana 2022 da dalibai a fadin tarayya suka rubuta"
Post a Comment