Soyayya Ruwan Zuma "KECE ABAR TINANINA, KECE ABAR TINANINA, FUREN SOYAYYA
Friday, April 29, 2022
Comment
Soyayya Ruwan Zuma "KECE ABAR TINANINA, KECE ABAR TINANINA, FUREN SOYAYYA"
Kalmomi uku na yin sanadin karuwar bugun da zuciyata ke yi, kalmomi uku na sanya kafata karkarwa, kalmomi uku na sanya kaina ya yi ta faman rangaji, bari dai na furta su yau a gare ki ko na huta da azalzalar da zuciyata take yi mini a dangane da hakan, kalmomi uku: INA SON KI!!!
KECE ABAR TINANINA.
Damuwa? A’a sam, tayaya zan kasance cikin damuwa bayan a ko yaushe ke ce abar tinani na? Da ke nake kwana sannan kuma da ke nake tashi a cikin zuciyata. Ina kaunar ki!!
FUREN SOYAYYA.
Idan har ya kasance zan ke samun kyautar furanni a dukkan lokacin da na hadu da ke, to kuwa ni zan kasance mai ziyartar dausayi ma’abocin firanni masu kamshi na mallaka dukkan lokacina na wannan rana domin girmamaki. Ina son ki sosai a cikin zuciyata.
0 Response to "Soyayya Ruwan Zuma "KECE ABAR TINANINA, KECE ABAR TINANINA, FUREN SOYAYYA"
Post a Comment