Kalaman Soyayya Mafi Daɗi
Kalaman Soyayya Mafi Daɗi
Sarautar da zuciyarki tabani tasa inajina tamkar wani gawurtaccen jarumin da zai iya yaki cikin duniyar nan nikadai batare da ansamu nasara akaina ba
Idan nayi duba yazuwa wasu bangaren sassan jikina sai inga dukkan jikina ya fara rikedewa zuwa irin suffar jikinki
Sonki yakwace dukkan wasu madafan iko nacikin zuciyata shiyasa yanxu banida burin daya wuce naganki nayi miki kallo irin na kasaita
Cikin mafarkina nake ganinki akowace rana kinyi shiga irinta manyan sarakai kina takawa daidai cikin tafiyar kasaitar sarauniya mai karfin ikon mulkin dakowa yake miki ladabi
Kina zuwa ta gabana kinyi ado da kayan sarauta na musamman kyakkyawar murmushinki yana kara ta,azzara zuciyata zuwa cikin wata duniya ta musamman
Kinada tsayi da kyan diri namusamman gashin kanki ya tsaru yasha tsafta gashi baki kaman gashin kan larabawa.
0 Response to "Kalaman Soyayya Mafi Daɗi"
Post a Comment