Wani Matashi Ya Auri Mata Biyu A Rana Daya [Hotuna] - Ko a Dakin Wa Zai Kwana?
Wani Matashi Ya Auri Mata Biyu A Rana Daya [Hotuna] - Ko a Dakin Wa Zai Kwana?
A cewar hoton da ya yadu a yanar gizo, wannan matashin da aka bayyana a matsayin Muhammad ya auri wadannan kyawawan matan a rana guda. An tattaro cewa an daura auren ne a yola babban birnin jihar Adamawan Najeriya.
Bayan bikin na baya-bayan nan, hotunan auren nasu ya rika yaduwa a shafukan sada zumunta daban-daban wanda ya jawo cece-ku-ce daga ‘yan Najeriya.
Matar ta farko dai ana kiranta da Maryama yayin da matar ta biyu mai suna Aisha kuma a halin yanzu suna zaune cikin jin dadi a gidan aurensu. Sai dai kuma jama'a a fadin kasar na ta yabawa kokarin matashin, yayin da wasu kuma ke sukar sabbin ma'auratan. A ƙarshe, mafi kyawun abin da ya kamata mu yi duka shine taya su murna da kuma yi wa dangi addu'a Allah ya albarkace su da kyawawan ƴaƴa.
0 Response to "Wani Matashi Ya Auri Mata Biyu A Rana Daya [Hotuna] - Ko a Dakin Wa Zai Kwana?"
Post a Comment