Sabin Alamomin da Zaka Gane Wacce Ke Sonka Da Gaske
Sabin Alamomin da Zaka Gane Wacce Ke Sonka Da Gaske
A lokacin da kake ‘ko’karin gano matsayinka a
zuciyar budurwarka shin tana son ka ko akasin
haka da akwai bu’katar ka nazarci wasu
abubuwa wad’anda wasu sun kasance waiwaye
ne wasu kuma suna kan faruwa.
FARKON HA’DUWAR KU.
YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA.
FARKON HA’DUWAR KU
A yayin gabatar da soyayyarka gare ta ka yi
amfani da salo ne mai karsashi wato sai da ka
gama jan hankalinta da ra’ayinta a kan ka
sannan ka bayyana a gareta da lamari na
soyayya? Furta kalaman amince wa na soyayya
ga wanda suke so abu ne da mata suke jin
kunyar furta wa a karon farko ga samarin na
su, sai dai duk da haka zata ke nuna maka
alamun tana son ka kuma zata ke nuna maka
wasu alamomi da suke nuni da SO. Salon da
kake bi wajen gudanar da soyayyar ta ku shi ne
sikelin auna ci- gaba ko ci-bayan soyayyar ta
ku, misali a lokacin da kuke tsaka da soyayya
sai ta samu wani da ya fika iya kalaman
soyayya da barkwanci da rashin yawan mita da
dai duk wani salo mai burge wa to babu
shakka ko kafi ‘karuna dukiya zai iya d’auke
hankalinta da ga kan ka, sai dai ta tsaya da
kai dan kud’inka.
A saboda haka akwai bu’katar ka kasance mai
sabunta salonka na soyayya tun daga kan
kalamai da yanayin yadda kake bata kulawa da
sauran su lokaci bayan lokaci. A dukkan
lokacin da ka bu’kaci mace ta baka amsar
amince wa tana son ka sai ka ga ta yi
murmushi ko ta kasa furta hakan a karo na
farko to hakan yana daga cikin alamu na SO
domin kuwa wanda ake so ake jin kunya.
Karda ka damu da sai ta furta maka kalmar
tana son ka kai dai lura da wad’annan
abubuwa kamar haka;
✓ Sau nawa kake kira kafin ta amsa?
Idan har da so zata amsa a kira na farko idan
kuma bata amsa ba zata amsa a kira na biyu
har ta baka uzurin da zaka gamsu na dalilin
rashin amsa kiran, idan har bata amsa a kira
na biyu ba sai ka bar kiranta haka idan har da
so zata kira ka da zarar ta ga kiranka da ta
rasa har ta baka uzurin kare kai.
✓ Matu’kar tana son ka za ta kasance mai
kar’bar shawarar da duk ka bata kuma za ta
kasance mai son abun da kake so.
✓ A duk lokacin da ka je wajen ta zance za ta
fito cikin farin ciki kuma ba zata nuna ‘kosawa
da jin firarka ba matukar ka iya zance har zuwa
lokacin da za ku yi sallama. *Idan har ka saba
kiran ta a waya matu’kar ta damu da kai idan
ka kwana biyu baka kira ta ba to za ta kira ka
ta ji ko lafiya, idan ma bata kira ba saboda
wani dalili bayan ka kira za ta yi kalamai na
nuna ta yi kewar ka.
✓ Idan har tana son ka a kullum za ta ke
‘ko’karin yin abun da zai faranta ranka, za ta ke
‘ko’karin guje wa abun da zai sa ka yi fushi.
✓ A lokacin da soyayyarku ta yi nisa zata iya
bayyana maka wasu sirrikanta da suka shafe
ta.
✓ A lokacin da ka nuna ‘bacin ranka a kan wani
abu da ta aikata da ba dai- dai ba, a yayin
baka ha’kuri da shawo kan ka za ta iya zubar
da hawaye.
✓ Zata ke ‘ko’karin bayyana ka ga ‘kawaye da
kuma ‘yan gidansu.
✓ Zata ke ‘ko’karin turo maka da kalamai na
soyayya.
✓ Zata kasance mai tambaya a dangane da ‘yan
uwa da kuma abokanka da ma dai duk wani
da ta san kuna a tare.
✓ Za ta ke damuwa da damuwarka. Irin
wad’annan abubuwa da sauran ire-iren su duk
zai kasance ta na nuna maka su.
YANAYINTA DA KUMA HALAYYARTA.
Akwai bu’katar ka fahimci yaya yanayinta da
kuma halayyarta suke,
✓ Shin tana da jan aji ne da yawa? wanda hakan
ka iya sawa ko tana son ka ba zata amince da
kai a karon farko ba har ma za ta iya yin wasu
abubuwa da zaka iya tinanin wula’kanci ta yi
maka, amma da sannu matu’kar ka iya allonka
za ka wanke.
✓ Tana da kunya ne? ta yadda ba za ta iya sakin
jiki da kai ba a karon farko kuma bayan tana
son ka, idan ka yi ha’kuri da sannu soyayyarka
za ta cire mata wannan kunyar da take ji a kan
ka domin kuwa idan aka juri zuwa rafi da
sannu tulu yake fashe wa.
✓ Koda a ce bata da son kud’i farkon soyayyar
ku sai ya kasance ka fara yi mata kyaututtuka
to da sannu idan ka matsa da yi mata kyauta
son abun hannunka zai rinjayi son da take yi
maka na gaskiya, an dai kuma ce kyauta tana
‘kara soyayya, amma kuma komai ya yi yawa
to zai kawo matsala. Wannan shi ne abun da
zan iya cewa a ta’kaice.
Ina fatan kuna nan lafiya tare da fatan ku
kasance cikin ‘koshin lafiy.
Ni inada wata yarinya wacce nakeso yar sheikara 13 tanayiman abubuwa kalala wani lokaci harda zagi
ReplyDeleteNakasa gane abunda take nufi
Inaneman shawara