-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Rancen Covid-19: Nirsal Microfinance Bank Sun Fara Tura Sakon Biyan Rencen Kuɗin Na Targeted Credit Facility (TCF) Da Akaci, Duba Yadda Sakon Yake

Rancen Covid-19: Nirsal Microfinance Bank Sun Fara Tura Sakon Biyan Rencen Kuɗin Na Targeted Credit Facility (TCF) Da Akaci, Duba Yadda Sakon Yake

Rancen Covid-19: Nirsal Microfinance Bank Sun Fara Tura Sakon Biyan Rencen Kuɗin Na Targeted Credit Facility (TCF) Da Akaci, Duba Yadda Sakon Yake

Kamar yadda muka sani Babban Bankin Najeriya (CBN) ya gabatar da N50bn ga Nirsal Microfinance Bank kan tsarin Targeted Credit Facility (TCF) a matsayin wani kunshin tallafi don tallafawa taimakawa dai-daiku, kanana da manya nazauna gida,  kanana da matsakaitan masana'antu (MSMEs) da annobar COVID-19 ta shafa.

Babban Manajin Darakta na Bankin Microfinance na Nirsal, Abubakar Abdulahi Kure, ya bayyana karara a cikin hirar  da akayi dashi a kwanakin baya yace " Rancen NMFB ba wai ganimar kasa  ba ne, dole ne wadanda suka ci gajiyar rancen su tabbatar sun biya bashin.

A yanzu haka, masu cin gajiyar shirin sun fara karɓar saƙonni daga Babban Bankin Nirsal Microfinance don biyan kuɗin lamuni.

Sakon ya fito ne ga daya daga cikin

 cikin shafukan Facebook na NMFB ta hannun wani da yaci gajiyar Lamunin na Targeted Credit Facility wanda ya samu sakon NMFB inda acikin sakon bukace shi da ya biya bashin ta hanyar amfani da lambar USSD, bankin Intanet, ko ziyartar daya daga cikin rassan da ke kusa da su.

Ga jawabinda ke cikin sakon a kasa acikin harshen Turanci

“Dear USMAN IBRAHIM SHERIFF”

Your repayment account for the CBN/NMFB Targeted Credit Facility (Covid-19 Loan). You can start saving towards, or pay monthly installments from any bank’s USSD, mobile app, and internet banking channel, or kindly visit the nearest NMFB branches in your location.”

For enquiries call 09010026900.”

0 Response to "Rancen Covid-19: Nirsal Microfinance Bank Sun Fara Tura Sakon Biyan Rencen Kuɗin Na Targeted Credit Facility (TCF) Da Akaci, Duba Yadda Sakon Yake"

Post a Comment