Barawo ya sace kuɗi a POS, kudan zuma sun tilasta ya tona wa kansa asiri, duba yadda ta faru
Barawo ya sace kuɗi a POS, kudan zuma sun tilasta ya tona wa kansa asiri, duba yadda ta faru
Wani abin mamaki ya faru bayan wani mutum da ya saci kudi a wani POS ya dawo da shaidar abin da ya sata washegari kuna cikin matsanancin hali na damuwa, azaba, da kunci. Jaridar Haskenews.com.ng ya samo.
Lamarin ya faru a yankin APAC a gundumar Kaberamaido da ke gabacin kasar Uganda.
Rahotanni na cewa bayan an yi wa mai POS sata, ya je ya kai kara wajen wani Boka
Sai dai washe gari kwatsam sai ga wanda ya yi satar dauke da sauran abin da ya sata. Kuma yana cikin kunci domin dai kudan zuma sun daskare a bayansa.
Nan take aka sanar da yansanda domin kauce wa yiwuwar wasu su fada masa da duka har su kashe shi ko su yi masa illa, duba da yadda jama'a suka taru domin ganin abinda ke faruwa.
Sai dai Boka ya bukaci ala tilas a ba shi lokaci cewarsa wajibi ne ya gudanar da karkaren aikinsa domin sama wa barawon lafiya kafin dauki kowane irin mataki.
0 Response to "Barawo ya sace kuɗi a POS, kudan zuma sun tilasta ya tona wa kansa asiri, duba yadda ta faru"
Post a Comment