Ƙungiyar manoma ta SEIFAC za ta fara rabawa manoma masu cin gajiyar shirin samun rance na gwamnatin Tarayya ATM ɗin su a ranar Litinin mai zuwa
Ƙungiyar Manoma Ta SEIFAC Za Ta Fara Rabawa Membobinta ATM A Ranar Litinin Mai Zuwa
Ƙungiyar manoma ta SEIFAC za ta fara rabawa manoma masu cin gajiyar shirin samun rance na gwamnatin Tarayya ATM ɗin su a ranar Litinin mai zuwa.
Idan baku manta ba a shekarar da ta gabata gwamnatin Tarayya ƙarƙashin ƙungiyar manoma ta SEIFAC ta tattara sunayen dukkannin manoman da suka nemi ranche na dukkannin jihohin Nijeriya baki ɗaya.
Bayan kallama tattara bayanansu ƙungiyar ta ware wasu daga cikin wa 'yanda zasu fara cin gajiyar, inda suka tura bayanansu zuwa ga HERITAGE BANK aka buɗe musu asusun a jiya a ƙarƙashin bankin.
Zuwa yanzu an kammala haɗa ATM na wasu daga cikin jihohin, za kuma a fara raba musu a ranar Litinin mai zuwa, a kowane ofishin ƙungiyar na kowace jiha.
Amma banda jihohi guda Goma da suka haɗa da; Gombe, Sokoto, Borno, Abia, Enugu, Rivers, Delta, Anambra, Imo, da Ebonyi, dukkannin wa 'yanda nan jihohi guda Goma sai a rukuni na gaba za'a basu ATM ɗin su.
Duk wanda zai je karɓa ya tafi da Naira 500 da zai baiwa ƙungiyar SEIFAC ɗin domin a bashi nashi ATM din.
Duk wanda ya mallaki ATM din, ya shiga jerin cikin manoman Nijeriya da gwamnatin za ta bawa ranchen makudan kuɗaɗe ƙarƙashin tsarin "ANCHOR BORROWERS’ PROGRAM".
Idan gwamnatin za ta bada ranchen kai tsaye zuwa ga asusun bankunan kowa za ta tura.
0 Response to "Ƙungiyar manoma ta SEIFAC za ta fara rabawa manoma masu cin gajiyar shirin samun rance na gwamnatin Tarayya ATM ɗin su a ranar Litinin mai zuwa"
Post a Comment