Menene P-YES National Youth Empowerment? Ya Kuma Ake Cin Gajiyar Sharin?
Menene P-YES National Youth Empowerment? Ya Kuma Ake Cin Gajiyar Sharin?
P-YES dai wani Programme ne wanda Gwmanatin tarayya ta kirkireshi tun a baya domin tallafawa al’ummar kasar nan duba da irin halin da ake ciki na roron wake.
Saidai a yanzu sunan wannan programme na P-YES ya cika social media makil inda zaka ga mutane nata kokarin sharing dinsa zuwa ga ‘yan uwansu domin samun romon wannan tallafi.
Maganar gaskiya Arewatalent Professinal Team sunyi bincike domin gano yadda wannan lamari yake, cikin taimakon Allah Team din sun gano wannan Programme na P-YES ba gaskiya bane don haka kada kayi ko kasa wani ya cike bayanan sa domin gujewa fadawa halin nadama.
Domin kuwa irin wannan lamari wasu ne a gefe suke fakewa da tallafin Gwamnati suna danfarar al’ummar kasar nan.
A karshe muna kira ga shuganni da wadanda suke da iko na wannan kasa tamu mai albarka das u sanya idanu da kuma bibiyar duk irin wadannan abubuwa domin dakilesu da wuri kafin miliyoyin alumma su fada cikin rami mai zurfi.
0 Response to "Menene P-YES National Youth Empowerment? Ya Kuma Ake Cin Gajiyar Sharin?"
Post a Comment