Yadda Zaku Cike Tallafin Balaguro Na Kai (PTA) da Tallafin Balaguro na Kasuwanci (BTA), CBN loan cikin Sauki
Yadda Zaku Cike Tallafin Balaguro Na Kai (PTA) da Tallafin Balaguro na Kasuwanci (BTA), CBN loan cikin Sauki
Tsarin PTA da kuma BTA tsarine da ake amfani dashi ga matafiyan da zasu fita izuwa kasar waje domin neman ilimi ko kuma kasuwaci ko kuma neman lafiya.
Amfanin wannan tsari shine a matsayinka na dan Najeriya idan zaka fita izuwa kasashen ketare to kana bukatar chanji na kudi domin ba lallai bane kudin ka na kasarka yayi aiki yadda kake so a wata kasar.
Hakan yasa Gwamnati take amfani da wannan tsari domin tallafawa ‘yan kasa a lokacin da zasuyi tafiya sai su sanya wani adadi na naira a cikin asusun su daga nan sai a canja izuwa Dollar wanda zai isa har kaje kadawo batare da wata matsala ba.
Bugu da kari wannan tsarin yana da matukar mahimmanci domin kuwa matafiyi zai sami Dollar a farashin gwamnatu maimakon farashin ‘yan kasuwa.
Hakan yana faruwa ne bayan matafiyi ya kammala dukkan abubuwan da ake bukata kamar su: International Passport, Visa da sauransu.
Saidai wani hanzari ba gudu ba. A wannan makon babban bankin kasa wato CBN ya canza tsarin yadda ake karbar wannan tallafi na PTA da BTA ta inda mai neman zaije café mafi kusa dashi domin cikewa sannan sai yatafi izuwa bankinsa domin karasawa, ko kuma idan zaka iya yi da wayar hannunka shima yana iya yiwuwa
Maza ka garzaya izuwa bankin ka domin samun Karin haske game sabon tsarin da Gwamnati ta tanadar ga alumma.
0 Response to "Yadda Zaku Cike Tallafin Balaguro Na Kai (PTA) da Tallafin Balaguro na Kasuwanci (BTA), CBN loan cikin Sauki"
Post a Comment