Arha banza na sameta, sadaki N400 na biya, shi ma sadaka na yi a coci, Mijin Baturiya mai shekaru 70
Arha banza na sameta, sadaki N400 na biya, shi ma sadaka na yi a coci, Mijin Baturiya mai shekaru 70
Bernard Musyoki ya hadu da Deborah Jan Spicer mai shekaru 70 a Facebook shekarar 2017 wanda suka fada tsundum cikin soyayya.
A ranar 29 ga watan Disamban 2020 Baturiyar mai shekaru saba’in ta nufi har kasarsa (Kenya) don ganin masoyinta kuma bayan wata daya su ka yi aure.
Yayin da fitacciyar jaridar Kenya ta TUKO.co.ke ta yi hira da shi ya bayyana cewa:
“A Facebook mu ka hadu kuma ni na tura mata gayyatar zama kawata ta amince. Cikin mako daya na bukaci ko za ta iya aure na ta kuma amince.”
A cewarsa ya dinga kokarin zuwa Amurka don ganinta amma abin ya ci tura har sai da dai tazo su ka hadu.
Batun kuwa sadaki ya ce ya samu arha don dala daya (N409.89) ita da yaranta su ka nema a wurinsa, shi ma cewa su ka yi ya yi sadaka a coci.
Duk da yadda gidanmu yake kamar mashekarar jaki, a haka kyakkyawar budurwata take so na, Saurayi
Wani matashin saurayi dan kasar Ghana mai amfani da suna unrulymacmonies, kuma yana amfani da bra_kingsley1 a manhajar TikTok, ya shayar da mutane da dama mamaki.
A bidiyon kyakkyawar budurwarsa wacce ya wallafa a TikTok, ya ce haka nan budurwarsa take sonsa.
An ga yadda budurwar ta shiga gidansu wanda yake kaca-kaca duk kwata har bakin kofar dakinsa.
Wannan bidiyon ya isa har Twitter inda wani Oscarnuwati ya wallafa inda yace:
“Ga inda nake zama amma a haka take makale da nu, kuna ganin ya dace nima in so ta?
Shin kuna da wani abin cewa? za ku iya bayyana ra’ayinku a wajen sharhi dake kasa.
Ku cigaba da kasancewa da jaridar mu domin cigaba da samun sahihan labarai kai tsaye a wayoyinku, za kuma ku iya biyo mu a shafukanmu na sadarwar kamar haka:
0 Response to "Arha banza na sameta, sadaki N400 na biya, shi ma sadaka na yi a coci, Mijin Baturiya mai shekaru 70"
Post a Comment