Zamu sake fitar da ‘yan Nageriya mutun milyan ashirin da biyar 25m daga kangin talauci - Cewar Farfesa Osinbajo
Zamu sake fitar da ‘yan Nageriya mutun milyan ashirin da biyar 25m daga kangin talauci - Cewar Farfesa Osinbajo
Mataimakin shugaban Ƙasar Nageriya farfesa Yemi Osinbajo yace shirin Hukumar zuba hannun jari ta ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje wato- NDIS na ɗaya daga cikin wata hanya Mai mahimmanci da zata kawo zuba hannayen jari a Ƙasar.
Osinbajo ya bayyana haka a lokacin taron Hukumar cigaban ƴan Najeriya mazauna ƙasashen waje NDIS karo na 4 na wannan shekara ta 2021.
Mataimakin Shugaban Ƙasa yace hakan zaiyi sanadiyar a fitar da ‘ƴan Najeriya Miliyan 25 daga ƙangin Talauci a shekarar 2025. Taron Daya gudana ranar Talata a ɗakin taro na shugaban ƙasa dake Villa Abuja.
Osinbajo Wanda ya samu wakilcin Sakataren Gwamnatin Tarayya Boss Mustapha yayi nuni dacewar an ƙirƙiri NDIS domin samar da zuba hannun jari a Najeriya.
Osinbajo ya bayyana cewar manufar Gwamnatin Buhari shine a inganta kuɗaɗen shiga a ƙasar.
Yace gwamnatin a shirye take domin samar da ayyukan yi ga matasa Yan Nageriya.
Source: opportunitieshub
0 Response to "Zamu sake fitar da ‘yan Nageriya mutun milyan ashirin da biyar 25m daga kangin talauci - Cewar Farfesa Osinbajo"
Post a Comment