Samu Rancen N500,000.00: Addu'a Ga Masu Neman Samun Kuɗin Covid-19 Na Nirsal Microfinance Bank
Samu Rancen N500,000.00: Addu'a Ga Masu Neman Samun Kuɗin Covid-19 Na Nirsal Microfinance Bank
ADDU'AR BIYAN BUKATU DA GAGGAWA DAGA MANZON ALLAH (SAWW)
Ya zo a cikin Littafin "Muhajud-da'awat" na Sheikh bn Dawus (ra) cewa: Wani Bawan Allah ya yi Mafarki da Manzon Allah (saww) ya roki Manzan Allah ya sanar da shi addu'ar samun Faraji da mafita a cikin kowanne irin yanayi. Sai Manzon Allah (saww) ya ce da shi, ka ce:
"يا من لا يستحيى من مسألته ولا يرجى العفو إلا من قبله، أشكوا إليك ما لا يخفى عليك، وأسألك ما لا يعظم عليك، صل على محمد وآل محمد.
وادع بما شءت ينجح الله طلبتك. فقال يارسول الله وحدي، فقال لك ولكل من دعا بها.
Sannan Manzon Allah (saww) yace da shi: Sai ka roki Allah abinda kake so, Allah zai biya bukatar taka. Sai Mutumin yace: Ya rasulallah ni kadai ne za a yi biya wa bukatata idan na yi addu'ar? Sai Manzon Allah yace da shi: Kai, da kuma duk wanda ya roki Allah da wannan addu'ar.
Ga addu'ar da Hausa:.
"Ya man laa yustahya min mas'alatihi, wa laa yurjal afwu illa min qibalihi, ashkuu ilaika maa laa yakhfa Alaika, wa as'aluka maa laa ya'azumu alaika, Salli ala Muhammadin wa Ali Muhammad"
Madogara: Littafin Muhajud-da'awat shafi na 437.
0 Response to "Samu Rancen N500,000.00: Addu'a Ga Masu Neman Samun Kuɗin Covid-19 Na Nirsal Microfinance Bank"
Post a Comment