-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

NYIF Training: Ana Ci Gaba Da Tura Sakon Training Ga Matasa Dubu 10,000 Da Zasuci Gajiyar Shirin Asusun Zuba Jari na Matasa na Najeriya(NYIF)

NYIF Training: Ana Ci Gaba Da Tura Sakon Training Ga Matasa Dubu 10,000 Da Zasuci Gajiyar Shirin Asusun Zuba Jari na Matasa na Najeriya(NYIF)

NYIF Training: Ana Ci Gaba Da Tura Sakon Training Ga Matasa Dubu 10,000 Da Zasuci Gajiyar Shirin Asusun Zuba Jari na Matasa na Najeriya(NYIF)

Abaya Ma’aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Tarayya ta fiatarda jerin sunayen mutum dubu daya da zasuci gajiyar shirin Asusun Zuba Jari na Matasa na Najeriya wato Nigeria Youth Investment Fund(NYIF). 

Shidai wannan shirin an kafa shi ne a matsayin wani bangare na Ma’aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Tarayya (FMYSD) da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya ba da Kuɗi don saka hannun jari a cikin tunanin matasa don gina sana’o’i masu dorewa da za su iya kulla kasuwanci da kuma kara samar da ayyukan yi a Najeriya. An sadaukar da asusun ne don saka hannun jari a cikin sabbin dabaru, fasaha da hazaka na matasan Najeriya da nufin mayar da su ’yan kasuwa, masu samar da ayuka da kuma samun arziki da  daukar ma’aikata, da ke ba da gudummawa ga ci gaban kasa.

Shirin ya shafi matasa masu shekaru 18-35 da kuma cikakkun bayanai game da ayyukan da ake bukata don tallafawa kafa kasuwanci, fadadawa da kuma samar da ayyukan yi ga matasa a sassa masu mahimmanci na tattalin arziki da zamantakewa.

A yanzu haka Ma’aikatar Matasa da Cigaban Wasanni ta Tarayya ta fara tura sakon gayyatar horo(training) ga matasan domin basu training da kuma koya masu kasuwanci kafin basu jari da zasu fara kusuwanci dashi.

Duba wasu daga cikin hotunan sakon training



ALLAH Yasa Muyi Nasara

0 Response to "NYIF Training: Ana Ci Gaba Da Tura Sakon Training Ga Matasa Dubu 10,000 Da Zasuci Gajiyar Shirin Asusun Zuba Jari na Matasa na Najeriya(NYIF)"

Post a Comment