Kusan Waye Nirsal Microfinance Bank Vendor Naku: vendor bai da ikon da xai baka kaya kai tsaye dole sai Nirsal microfinance bank sun aika masa da sunan ka
Kusan Waye Nirsal Microfinance Bank Vendor Naku: vendor bai da ikon da xai baka kaya kai tsaye dole sai Nirsal microfinance bank sun aika masa da sunan ka
Babu kalar zagin da mutane basu yi wa vendor kano ba, akan cewa ya ki basu kayan su bayan abun ba haka yake ba marubuta sun sha sanar da mutane cewa vendor bai da ikon da xai baka kaya kai tsaye dole sai Nirsal microfinance bank sun aika masa da sunan ka wurin shi sannan xai kiraka ya baka kayan ka.
Kwanakin baya naso nayi rubutu akan Dr. Bashir Vendor kano sai nace bare dai in fara neman sa a waya muyi magana, mun dau lokaci muna waya yana fadi min wasu abubuwan akan tsarin non interest loan na gamsu da duk bayanai sa , wannan shine adalci idan kaje ana magana akan mutum karka yada kace hakane kayi duk yadda zakayi ka ji da bakin sa wannan shine adalci.
Sanin kowa ne yanzu vendor kano yana iyakar kokarin sa wurin salamar mutane wanda Nirsal microfinance bank suna aika mishi da sunayen su, vendor ba zai cin yi muku abun da aka umarci shi ya baku ba abun daya fi dacewa ku sani shine, dole sai Nirsal microfinance sun tura sunan ka zuwa wajen vendor sannan zai kiraka ya baka kayan ka.
Wanda baa kirasu ba suyi hakuri da yardar Allah nan kusa vendor zai kira ku, akwai mutane da dama wanda har yanzu baa amince da rancen su kada su damu zaa amince da ikon Allah.
Ya hayyu ya qayyum Allah ka sanya rabon mu.
Marubuci ©Ahmed El-rufai Idris
Bayanin ka gaskiya ne, Amma aikin Dr Bashir vendor na kano baya sauri, saboda akwai Wanda na sani sunyi accepted na offer tun September Amma har yanzu ba a sallame suna, bayan haka a halin a da ake ciki yanxu duk Wanda aka masa approved na kayan 500,000. To vendor zai dau 50,000, Masu ba da kaya zasu dau 50,000 idan baka yarda ba a baka kayan da Bai wuce 350,000 ba, Kai wani a watsup group na vendor yace 380,000 aka bashi, to idan akace bashi ne mara ruwa, waye zai cika kudin zuwa 500k idan ka tashi biya. Saboda haka Ina kira da Masu ruwa da tsaki da suyi bibiya akan wannan lamarin.
ReplyDeleteNagode. Sunusi Muhammad Bello. Kano state. 08022212602
Hmmm! Mu dai muna nan muna jira, Allah yasa mu dace. Ameen
ReplyDelete