-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Bilkisu Abdullahi

Tarihin Jaruma Bilkisu Abdullahi

Tarihin Jaruma Bilkisu Abdullahi 

Bilkisu Abdullahi na daya daga cikin jarumai mata masu hazaƙa dA kuma ƙwazo a masana’antar Kannywood. Jarumar na ɗaya daga cikin Kyawawan matan kannywood, jarumar na da dunbin masoya

An haifi jarumar Kannywood Bilkisu Abdullahi a ranar 5 ga Mayu 1993 a Jihar Legas, Kudu maso Yammacin Najeriya. Mahaifin jarumar Mallam Andullahi, dan jihar Kano ne mahaifiyarta kuma ta fito daga Yola, jihar Adamawa. Jaruma Bilkisu Abdullahi bata tabayin aureba. Jarumar ta yi karatun Firamare da Sakandare duk a jihar Legas.

Jaruma Bilkisu Abdullahi ta bayyana cewa tana da shawar shiga wasan kwaikwayo ta masana'antar kannywood dakeda resha a jahar kano tun tana karama kasantuwar nisa wasu matsaloli batasamu cika wannan gurin nataba har zaida ta girma.

Bilkisu Abdullahi ta shiga masana'antar Kannywood ta hannun fitaccen darakta kuma jarumi Ali Nuhu. Fim din da ya jawo hankalin ta shine lokacin da ta yi fim ɗin Aikin Duhu. Fim ɗin ya yi nasara kuma ta zama sunan gida a Najeriya. Har yanzu jarumar ta fara fitowa a fina -finai sama da dari.

Muna yiwa jarumar fatan alheri da samun nasara acikin sana'arta. Muna fatan za ta samar da dawwamammen ci gaba a masana'antar Kannywood ta hanyar gwaninta a wasan kwaikwayo.

Menene hangen ku game da jarumar?


Duba Wasu Daga Cikin Kyawawan Hotunan Jaruma Bilkisu Abdullahi

































0 Response to "Tarihin Jaruma Bilkisu Abdullahi"

Post a Comment