Yan Arewa Mu Farka: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shafin Taron Matasa Na Kasa 2021
Yan Arewa Mu Farka: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shafin Taron Matasa Na Kasa 2021 - Kar Muyi Kasa A Gwaiwa Mu Hanzarta Cike Wannan Damar
Jigo: Siyasa da Mulki, Ilimi da Ci Gaban Matasa, Zaman Lafiya, Hadin Kai da Tsaro, Sake Fasalin Tunanin da Fasaha, Martabar Wasanni, Nishaɗi da kagaggun Fasahohi
Taron Matasan Najeriya
Wannan dandali ne don cin moriyar tunani da ra’ayoyin wani ɓangaren Matasan Najeriya a matsayin hanyar tantance halin da ake ciki yanzu tare da tunatarda matasa abubuwan ci gaba da suka shafe su haɗi da ƙirƙiro dabaru don magance waɗannan matsalolin da ke addabar matasa ayau.
Manufar Taro
Manufar wannan taro ita ce samar da ingantaccen tsari da samfurin isar da sako don daidaita tattaunawar Matasan ƙasa baki ɗaya. Hanyar da ta fi dacewa ita ce sake fasalin tunanin Matasanmu game da ayyukan gwamnati da kuma wayarda kai game da ƙalubale da wahalhalun da matasan Najeriya ke fuskanta.
Duba Bidiyon Tsarin Taron
Wasu Daga Cikin Hotunan Taron
Taron kyauta ne ga duk wakilai da masu halarta.
Abubuwanda za'a tattauna ko kaddamarwa a wajan taron
1. Siyasa da Mulki
2. Ilimi da Ci Gaban Matasa
3. Zaman Lafiya, Hadin Kai da Tsaro
4. Sake Fasalin Tunanin da Fasaha
5. Martabar Wasanni, Nishaɗi da kagaggun Fasahohi
Yadda Za'a Cike Wannan Taron
Domin cike wannan tsarin/damar Latsa Nan
Latsa Nan: Shiga Taron Matasan Najeriya
https://nationalyouthconference.ng/
Idan ya bude nemi inda aka rubuta " REGISTER TO GET STARTED " Sai ka latsa shi.
ALLAH YASA MUDACE AMIN
0 Response to "Yan Arewa Mu Farka: Gwamnatin Tarayya Ta Buɗe Shafin Taron Matasa Na Kasa 2021"
Post a Comment