Tarihin Jaruma Maryam Yahaya
Tarihin Jaruma Maryam Yahaya
Maryam Yahaya (An haifa maryam yahaya a ranar 23 ga watan yuni shekara ta 1997)yar fim din Najeriya ce a masana'antar Kannywood. Ta sami yabo ne saboda tana cikin fim din Taraddadi, fim din da elnass ajenda ya shirya. Saboda rawar da ta taka, an zabi Maryam Yahaya a matsayin kyakkyawar yar wasa mai kwazo daga City People Entertainment Awards a shekarar 2017. Hakanan an zabi ta a matsayin yar wasan kwaikwaiyo ta City People Entertainment Awards a shekarar 2018.
Wasu daga cikin fina-finan da Jarumar ta fito Gidan Abinci, Barauniya, Tabo, Mijin Yarinya, Mansoor, Mariya, Wutar Kara, Jummai Ko Larai, Matan Zamani, Hafiz, Gidan Kashe Awo, Gurguwa, Mujadala, Sareenah
Jaruma Maryam Yahaya na daya daga cikin tsofaffin fuska a masana'antar kannywood dake taka rawar gani a wannan shekarar, Jaruma Maryam Yahaya wadda akafi sani da Maryam Yahaya na daya daga cikin Kyawawan jarumai a masana'antar kannywood, Jarumar ta fito acikin sabin wakokakin da kuma fina-finan kannywood da sukayi fice a shekarar nan hakan ya bawa Jaruma Maryam Yahaya dunbin masoya daga daga yanki daban-daban a fadin kasarnan. A yanzu haka jarumar na najin sauki kan fama da rashin lafiya da tayi a baya
Duba Wasu Daga Cikin Kyawawan Hotunan Jaruma Maryam Yahaya
0 Response to "Tarihin Jaruma Maryam Yahaya"
Post a Comment