Tarihin Jaruma Bilkisu Shema
Tarihin Jaruma Bilkisu Shema
Bilkisu Abdullahi Shema (An haife ta 28 ga Watan Yuli a shekarar 1994). A Dutsen Ma a Jihar Katsina. Fitacciyar jaruma ce, ta fara karatun ta na firamari ne a makarantar Isa Kaita College of Education, bayan nan ta shiga sekandari a Government Day Secondary School Dutsin-Ma.
Shema dai na cikin mata masu tashe a fagen fim a wannan lokaci, ita ce matashiyar jaruma wadda tauraronta yake haskawa.
Sanadiyar Haskawar Tauraron Bilikisu Shema: ‘Tabbatacce Al’amari’, wannan fim shi ne wanda ya sanya wannan jaruma darewa matsayi na daya a cikin jarumai mata a kannywood domin ta tsaga a tsakiyar gogaggu ta kuwa nuna gwaninta.
Kasancewar labarin fim din kusan a kanta yake, hakan ya bata damar taka rawarta har da tsalle. Domin mafiya yawan wadanda suka kalli shirin maganar ta kawai suke yi ba ta sauran jaruman ba.
A wata Hira Bilkisu ta shaida cewa tun bayan da tayi fim din farko taso tayi aure domin har ta daina karbar aiki, amma Allah cikin ikonsa bai nufi yin auren ba, duk dai bata sanar da dalilin da ya hana yin auren ba.
Yan mata da samari na fuskantar kalu bale da yawa daga ciki da wajen masana’antar fina-finai a kokarin su na tabbatar da burin su na zama manyan taurari, amma Bilkisu tun bayan tabbataccen Al’amari Ali Nuhu ya saka ta a wani Sallamar so, sai kuma finafinai irinsu Dawood, Ranah da dai sauransu wanda yanzu haka suna hanya basu fito ba, Ita ce Wadda aka shirya zata fito a cikin fim din Mansoor sai ta makara ba ta zo da wuri ba har aka canja ta da wata.
Wasu daga cikin fina-finan da Jaruma Bilkisu Shema ta fito
Bilkisu shema tafito a fina-final da dama
kamarsu
sallamar so
dan saurayi
tabbataccen al,amari
muja dala
makamashin mata
hafeez
gidan abinci
barauniya
mansoor
dawood
ranah
Da sauransu
Sannan jarumar tafito a finafinai tare da jarumai
da dama
Kamarsu
Alinuhu
Adam A zango
Umar m shareef
Abdul M shareef
Shamus dan,iya
Maryam Yahaya
Hafsat idriss
Adamu Hassan Nagudu
Dadai sauransu
Duba wasu daga cikin Kyawawan hotunan Jaruma Bilkisu Shema
Nice
ReplyDelete