-->

SHAFIN HASKENEWS NA WHATSAPP

Tarihin Jaruma Bilkisu Safana

Tarihin Jaruma Bilkisu Safana

Tarihin Jaruma Bilkisu Safana

Haɗu da Bilkisu Abdullahi Safana, Jarumar Kannywood mai lokaci

Masana'antar Kannywood a halin yanzu cike take da hazikan 'yan wasan kwaikwayo  a inda kowa sai fafutukar neman nasara yake a masana'antar.

Daya daga cikin fitattun jarumai masu hazaka da kuma kyawun fuska masana'antar kannywood itace Bilkisu Safana. 

An haifi jaruma Bilkisu Safana a Jihar Kaduna. Ta yi makarantar firamare da sakandare duk a jahar Kaduna.

Bilkisu Safana ta shiga masana’antar kannywood a shekarun baya, Jarumar na ci gaba da samun yabo da kuma daukaka daga masoya kallon sharin fina -finan kannywood. Bilkisu Safana na daya daga cikin fitattun jarumai mata da masana'antar kannywood ke alfahari dasu.

Ta fara wasan kwaikwayo na kannywood a matsayin 'yar rawa. Ta fito a cikin shahararrun wakokakin kannywood, tare da shahararrun mawakan kannywood, kamar Garzali Miko, Hamisu Breaker, Umar M Sharif, Sanusi Oscar, da sauran su.

Daga baya Jarumar ta shiga acikin shirin fina-finai, Ta fito a fina -finan kannywood da dama, kamar Haram, shahararren shirin fina -finan Hausa, da sauransu.

Me za ku ce game da wannan sarauniyar kyau ta kannywood?

Duba Wasu Daga Cikin Kyawawan Hotunan Jaruma Bilkisu Safana


















0 Response to "Tarihin Jaruma Bilkisu Safana"

Post a Comment