Tambayoyi Guda Goma (10) Tare Da Amsoshinsu Akan Sharin Bayarda Rance Marar Kuɗin Ruwa Na NIRSAL Microfinance Bank
Har Yanzu Ana Ci Gaba Da Turawa Mutane Sakon Amincewar Rance Marar Kuɗin Ruwa Na Covid-19
Tambayoyi Guda Goma (10) Tare Da Amsoshinsu Akan Sharin Bayarda Rance Marar Kuɗin Ruwa Na NIRSAL Microfinance Bank
1 yaushe nayi apply?
2 yaushe akayi approved dina?
3 ta ina aka turomin sako?
4 yaya sakon yake?
5 to taya zanyi accept din offer?
6 idan kuma karamar waya ce dani fa?
7 shin akwai wani link da ake shiga a sanya BVN don abincika ko mutun yasamu approved?
8 meyasa nake shiga cikin link din amma sai inga sunan wani?
9 Taya zangane accept dinda nayi yayi dai dai?
10 shin taya zangane apply dinda nayi yayi dai dai?
A yanzu ne na tabbatarda cewa nayi accept din wannan offer tawa. Tun dazu aiki kawai nakeyi amma hankalina yanaga wannan approved da akayimin kamar da wasa nasake shiga sai kuwa naga dukkan bayanaina har adireshina.
To tunda hankalina yakwanta yanzu zan amsa wasu daga cikin tambayoyinda mutane suke yawan yi kuma suna son sanin amsarsu. Gasu kamar haka.
Tambaya da amsa tare.
Kowace tambaya ga amsarta.
1 yaushe nayi apply? Amsa tun randa aka bude wannan portal.
2 yaushe akayi approved dina? Amsa . Jiya da misalin karfe 1:00 da wasu yan mintuna na manta dai.
3 ta ina aka turomin sako? Amsa ta massage wato a layina.
4 yaya sakon yake? Amsa zakaga anrubuta NMFB sannan afada maka cewa anyi approved dinka kaduba gashi nan nadora yadda zaka gani to idan kaga haka shikenan. Anyi approved dinka.
5 to taya zanyi accept din offer? Amsa zaka danna wannan link din da suka turoma zai kaika wurinda zaka dinga danna accept zaka gansu Step uku ne kowanne zaka danna Accept ne sai ka danna Next. Har kazo Step din karshe Wanda shine zakaga Submit saika dannashi shikenan kajira zakaga sun nuna maka successfully
6 idan kuma karamar waya ce dani fa? Amsa sai kayi copy din link zuwa babbar waya ko karubutashi yadda aka turoma shi saikayi accept din offer a babbar wayar. Kokuma kaje cafe ko kabiyani inmaka dari uku nake karba kacal. Saboda tausayawa Al umma.
7 shin akwai wani link da ake shiga a sanya BVN don abincika ko mutun yasamu approved? Amsa A A babushi indai sunyi approved dinka to zasu turoma da sako. Dalili kuwa shine zasu turoma link dinne tareda TCF number dinka sannan ta kowa daban take. Don haka idan kashiga cikin link din sunanka kawai zaka gani da baya nanka saboda TCF dinnan takowa daban. Kamar BVN ce lokacin Validate matuqar kasanya taka to bayananka kawai zata nuno maka
8 meyasa nake shiga cikin link din amma sai inga sunan wani? Amsa saboda matsalar network amma banda wannan idan kaci gaba da jarrabwa sunanka zai fito saika karasa abinda ake bukata.
9 Taya zangane accept dinda nayi yayi dai dai? Amsa idan kayi zaka iya sake yi to anan zasu nuna maka wannan sakon da kagani na dora saboda nayi nawa sai kuma nasakeyi sai sukace ai yarigada yayi bazan sake yin wani.
10 shin taya zangane apply dinda nayi yayi dai dai? Amsa kasake zuwa wurin wani yacikama a karshe idan akazo karshe zai nuna ancikashi idan bazaka iya sake bada kudi asake cikama ba to sai kayi a wayarka kokuma kaje inda Wanda yacikama ka tambayeshi
Sai wata tambaya da wasu sukeyi wacce sam baidace ace musulmin kwarai yanayin irinta ba.
Itace wai meyasa ni ba ayi approved dina ba. Ko suce yaushe za ayi approved dinsu?
Wannan babban kuskure ne
Yakai dan uwa Allah shine mai azirtawa da talautawa idan kayi hakuri hanyoyin Allah sunada yawa Allah yasan halinda kake ciki yasan bukatunka yasan abinda ma zai faru da kai nan gaba. Kada kaga kana rokonsa kamar bayajinka Wallahi yanajinka kaji tsoron Allah ka kara hakuri wata kila akwai hanyarda Allah ya tanadar maka wacce tafi wannan sau dubu.
Don haka kada ka zarge kanka ko wani saboda baka samu approved ko wani Loan ba Wallahi tallahi duk duniya babu Wanda zai iya cinye rabonka yana nan kawai kadage da addu a dare da rana kuma kayi hakuri.
Kadaina irin wadannan tambayoyi saboda ta nan ne shedan yake samun damar jefa maka wasu wasi ka fadi abinda zai je ya hallaka ka a karshe kayi biyu babu.
Ya Ubangiji kasanya Alkhairi ga duk Wanda yasamu approved
Ya Allah duk Wanda baisamu ba kasa yasamu kokuma kayi masa hanya wacce tafi wannan.
Allah ka kara kawo muna zaman lafiya a kasarmu da kwanciyar Hankali.
Masha Allah
ReplyDeleteMasha Allah
ReplyDeleteSalamu alekum tayaya zamuhadu dakai ga lambar WhatsApp na 08060051231
ReplyDelete